Chapter 29
CHAPTER 28
I just published Amriyar Hatsabibiyar Aljana Chapter 28 of my story “AMRIYA Hatsabibiyar Aljana”
http://www.ashblogg.com.ng/2022/03/amriya-hatsabibiyar-aljana-chapter-28.html
Zuciyar Zahara bugawa take da sauri-sauri, cikin ƙanƙanin lokaci ta daina jin duk wani sauti da ke kewaye da ita. Idanunta sun ƙafe akan masoyan guda biyu.
Abinda yake yi kenan duk wannan lokacin? Ta tambayi kanta. Soyayya yake da best friend ɗinshi ni kuwa ya jefar da ni babu labarinsa. Hakan zai yi min kenan? Ya gama amfani da ni ya jefar. Duk wannan tunanin Zahara ce ke yin sa ne.
Maryam da mamakin ganin wani abu ya ɗauke hankalin ƙawarta, ta bi inda Zahara take kallo da kallo. Nan ita ma ta ga tashin hankalin da ya ɗauki hankalin ƙawarta. Ta ji tsoro na ɗan lokaci. Ita da ta kawo ta nan dan ta sauya mata tunani. Bata taɓa tunanin irin wannan coincidence ɗin zai faru ba. Gyara nustuwarta tayi sannan ta ɗan zunguri Zahara a ƙafa. Ɗan zabura Zahara tayi tare da dawowa daga duniyar tunani.
Maryam fiddo wayarta tayi ta yiwa Zahara text : Sakarai ne, please.. Ki daina kallon su. Kar ki zubar da ajinki, mun zo nan ne dan nishadi.
Karanta saƙon Zahara tayi ba tare da tace komai ba. Tasan ƙawarta tana da gaskiya amma ba zata iya controling damuwar da ta zo ta mamaye ta ba.
“Me kuke kitsawa ne ƴan mata? Na ga lokaci guda kun yi shuru.” Cewar Habib cikin sigar zolaya.
Maryam kallon ƙawarta tayi. Nan take ta fahimci abinda ƙawar tata take nufi. Gyaɗa kai tayi tare da cewa
“Muna tambayar abinda ya kamata ayi oda ne."
Murmushi Habib ya yiwa Zahara kuma maganarta ta bashi dariya. A ranshi yana tunanin sanyi sanyi gare ta ko kuma a takure take saboda yanzu ne suka huɗu.
“Toh me kuke so a kawo muku? Ni ina son cin abinci sosai domin kuwa yunwa nake ji. Tsawon kwanaki kenan ban samu cin abinci ba sosai sakamakon aiki."
Dariya Mansoor yayi tare da cewa
“Kai dai abokina faɗi gaskiya baka son su ce maka acici. Na fa sanka."
“Barshi ya yi magana dear. Ai Zahara kaɗai zai wayancewa a nan. Mu mun sanshi." Cewar Maryam.
“Kar ki saurare su Zahara. Daman sun shirya tarar min yau, amma nasan ba zaki yarda ba."
“Dole akwai dalili idan sun ce maka acici.” Zahara ta faɗa tare da yin murmushin dole da mazajen biyu kaɗai ne ba zasu gane ba.
“A'a Zahara ba zaki biye musu ba kema. Three against one, akwai zalunci a ciki!"
“Kana da gaskiya, dan haka na koma tsaginka. Nasan Maryam da Mansoor suna jin daɗin sako mutum gaba."
“Yauwa kinga zai zama mu biyu against the world, babu wanda zai iya tsaida mu."
Nishaɗi ne ya kewaye table ɗin saidai Zahara ba zata iya hana kanta tunanin Kamal ba. Tana iya ƙoƙarinta ganin ta hana kanta kallon inda suke amma akai-akai tana juyawa na wasu ƴan daƙiƙu dan ta ƙara tabbatarwa kanta da tsohon saurayinta ne. A duk lokacin da ta kalle su kuma ta ga yanda Kamal yake washe baki, sai ta ji tana nadamar yarda da shi da tayi. Bata ganin fuskar Khadija amma Zahara ta tabbatar tana cikin farin ciki. Khadija ta jima tana nuna mata Kamal nata ne kuma su biyu ko ba daɗe zasu ƙare a tare. A baya ta ɗauka kawai farfaganda ne na ƙawa mai kishi amma daga ƙarshe ta gane gaskiya. Kamal dama cen yana son bestie ɗinsa, amma sai da ya fara soyayya da Zahara kafin ya fahimci hakan.
Zahara bata daina yiwa ƙanta tambayoyi ba kuma daga ƙarshe ta fahimci kasantuwar masoyan a wurin ba ƙaramin cutar da ita yake ba. Dan haka ta ji babu abinda take so da wuce zuwa gida, bata ɓata lokaci ba wajen fahimtar da ƙawarta. Sake turo mata text Maryam tayi :
« Na rantse miki Zahara, idan kika bar restaurant ɗin nan, ba ni ba ke. Haka zaki dinga guduwa duk lokacin da kika haɗu da shi wani wuri? Ina kika kai ajinki da mutuncinki? Ina son ki share su kiyi kamar baki taɓa sanin su ba. Su gasu cen suna nishaɗinsu ke kuma kin zo kin wani takure kanki. Kiyi haƙuri ki danne ki cigaba da biyewa shirmen Habib domin yafi wannan sakaren Kamal ɗin. »
Zahara da sai ta dara idan da babu damuwa a tattare da ita. Maryam na da baiwar dawo da ita cikin haske. Tana jin zafi amma bata yi wani abun cutarwa ba da zai sa ta gudu kamar ɓarauniya.
“So Zahara, me kike yi a halin yanzu?” Habib ya tambayi Zahara.
“Ina aiki a publishing company.” Ta bashi amsa.
“Eh amma aikin jarida ta so karanta. Idan ban manta ba kanwarka ma karatun aikin jarida take yi."
“Eh wannan shekarar ta huɗu ce take yi. Ke kuwa me ya hana ki cika wannan mafarki naki?” Cewar Habib.
Zahara tana tunanin ba zata iya amsa wannan tambayar ba domin amsar ta kai da kai ce. Murmushi kawai ta iya yi.
“Anyway, idan da gaske kina son yin karatun zaki iya nema na, ni zan haɗa ki da Mrs. Amadi na tabbatar zata yi murna da taimaka miki.”
Godiya tayi masa na ƙoƙarin da ya nuna domin cikar burinta.
(...)
Ɓangare ɗaya cikin restaurant ɗin kuwa, masoya biyu ne ke cin abinci cikin nishaɗi. Kamal yaji daɗi sosai da suka yi wannan fitar shi da masoyiyarsa. Da duk ayyukan da suka takure shi, bai samu lokacin hutu ba..
Ya kasa daina santin soyayyar Khadija. Yana jin kamar yana faɗawa soyayyarta ne a duk lokacin da ya kalle ta... Wannan abu ne da ya kasa fahimtar shi. Yana cikin farin ciki sosai da yasa bai lura da damuwar da Khadija take ciki ba.
“Yanzu.. da muka ci abinci.. Ina son yin wata magana da kai.” Khadija ta fara magana bayan ta tattara kuzarinta da hannu biyu.
Ajiye kofin ruwan da ke hannunsa Kamal yayi tare da tattare duk hankalinsa zuwa gare ta.
“Wacce magana ce?" Ya tambaye ta.
“Kamal ina da juna biyu." Ta sako masa maganar kamar saukar aradu.
Kamal a take bai fahimci abinda budurwar tashi tace ba, sai da ya ɗauki daƙiƙu masu yawa kafin maganar ta ratsa ko'ina na ƙwaƙwalwarsa. Sosai ya girgiza da jin wannan zancen.
“Ta yaya kika san da hakan?" Ya tambaye ta.
“Nayi pregnant test kuma nayi na jini da ya tabbatar min ina ɗauke da ciki.”
Kamal bai san takamaimai abinda zai ji ba game da wannan labari. Bai taɓa tunanin aikin dare ɗaya zai sa shigar ciki ko kuma in ce baya tsammanin hakan.
“Ka ce wani abu please..” Khadija ta roƙe shi cike da tsoron kar saurayin nata ya ɗauka da zafi.
“Sorry for my reaction.. abun ne yazo min bazata..ban..ban ma san abinda zan ce ba."
“I see.” Ta faɗa a kausashe.
Jiran komai take daga gare shi amma banda wannan reaction ɗin.
“Kar ki ɗauka da zafi Khadija, ba zan taɓa gudunki ba.. kawai na girgiza ne da jin wannan labarin... Ba zaki hukunta ni ba akan hakan. Sanar da ni fa kika yi zan zama uba. Kema nasan zaki girgiza, ya kamata ki fahimce ni.”
“Na fahimce ka Kamal, kawai ina tsoron abinda zai biyo baya ne. Na kasa daina tunanin gobe.”
“Ko me zai faru Khadija, zan kasance kullum domin ki. Wannan cikin da yake jikinki nima nawa ne kuma zan yi iya ƙoƙarina ganin na baku kulawa.”
Kamal da gaske wannan ne a zuciyarsa. Tabbas bai taɓa kawo hakan ba amma yana da tunanin kulawa da su domin yanzu sun zama familynsa.
Hannunsa ya sa cikin na Khadija domin nuna mata yana tare da ita.
“Kar ki ji tsoron komai, ina nan kuma zan cigaba da kasancewa a kusa da ke."
Khadija daɗi sosai ta ji na bayyana mishi cikin da tayi kuma ta ji batada wata sauran damuwa tinda Kamal yana tare da ita. Saidai matsalar ita ce...
Ko Amriya zata bar mata yaron idan ta ga yanda Kamal ke sonshi?
“Me yasa har yanzu baki saki fuskarki ba? Ki daina damun kanki Khadija, ina tare da ke kin ji ko?"
Gyaɗa masa kai kawai Khadija tayi a matsayin amsa. Ba zai yiwu ta yi masa zancen Amriya ba. Ba lallai ya fahimta ba, wa ma zai fahimta. Ba wanda zai fahimci cewa sai da ta nemi taimakon aljana domin shawo kan Kamal..babu. Bare ma Kamal ɗin. Tana tunanin yaƙar wannan hatsabibiyar ne ita kaɗai domin ƙwato ƴancinta da kuma ceto ɗanta.
“Mahaifiyarki ta sani? Nasan zata tsane ni, na controling kaina da ban yi ba.”
“Ni ban damu ba, rayuwata ce. Kuma bana nadamar baka kaina. Mun nunawa junanmu so a wannan daren kuma wannan ce tabbacin soyayya da na samu tinda nazo duniya.”
Na ƙanƙanin lokaci Khadija taji kamar ba ita ke magana ba. Saidai da sauri ta kori wannan tunanin tare da ɗora laifin akan damuwar da take ciki.
Hausa amriya
“Duk da haka, bai dace na taɓa ki ba alhali ba muyi aure ba. Mun aikata zunubi kuma ina son mu nemi gafarar ubangiji.”
“Nadama kake yi kenan?" Khadija ta tambaye shi.
“Ina nadama akan zunubin da muka aikata ba samuwar juna biyun ba. Dan haka ina son da kin haihu, muyi aure."
Khadija ji tayi kamar ta daka tsallen murna. Ta ji da kyau, Kamal yace zai aure ta bayan ta haihu.
“Nasan ba lokaci bane mai kyau yanzu na yin maganar aure..ko kuma yanzun ne ya kamata. Dan haka bani son ƙara jira. Zaki zama uwar ɗana, so ina son ki zama matar da zan rayu da ita."
“Oh my..God. baka san irin farin cikin da nake ji ba. Yau ranar farin ciki ce fiye da kowacce rana a rayuwata." Cewar Khadija.
Farin ciki take ciki sosai ta yanda ta ƙasa riƙe kanta sai da ta rungume Kamal. Kunya ce ta kama Kamal ganin mutanen da ke cikin restaurant ɗin na kallonsu, ya cewa Khadija ta nutsu.
“Yau farin ciki kawai nake ciki my love, babu abinda yake iya sauya hakan a yau."
Da faɗar haka Khadija taji wani yanayi a take a jikinta. Ta jita wani iri kafin ta dawo da sauri hayyacinta. Tana samun wannan yanayin ne kawai idan Amriya na ga wuri.
“Domin murnar hakan, ina son mu je gidanka. Ina buƙatarka.. Ina dab da roƙonka ka ɗauke ni tun nan gaban kowa, idan bamu tashi muka tafi ba yanzu."
Dariya ta so kwacewa Kamal yana tunanin me yake damun Khadija. Saidai abinda bai sani ba Khadija ta daina controlling duk wani abu da take cewa.
“Yanzu fa na gama faɗa miki ba zan ƙara taɓaki ba, sai bayan mun yi aure.”
“Na sani zamu yi aure amma yanzu a buƙace nake, ina buƙatar ka. My love.. ina ruwanmu da addini. Mun riga mun aikata wannan zunubin.”
“Ba dan mun aikata zunubi ba zai sa mu sake maimaitawa. Na faɗa miki gaskiyar abinda ke raina."
“Eh ni kuma ban damu da abinda yake ranka ba, ina son ka..”
Kafin ta ƙarasa kalaminta, ya rufe mata bakinta da hannunsa. Ya rasa me zai yi, ya kasa fahimtar abinda ke faruwa na sauyawar Khadija lokaci ɗaya."
Ita kuwa fuskarsa ta shiga shafawa.
“You are so beautiful, ina son na shiga jikinka. Ina son na mallake ka gaba ɗaya, ka zama nawa ni kaɗai."
Kamal wannan karon cikin fushi, ya damƙo hannunta da har ta kaishi ga cikinsa.
“Meye haka Khadija, ko ki daina abinda kike yi ko na maida ke gida.”
“Oops.. na ɓata maka rai? Shikenan zan dawo lokacin da kake jin wasar." Ta faɗa.
Nan sai ga Khadija ta dawo hayyacinta. Bata iya tuna komai na abinda ya faru ba, amma tasan akwai sa hannun Amriya lokacin da ta ga irin kallon da Kamal yake mata.
“Me ya faru?" Ta tambaye shi.
“Amma wasa kike ko? Har kin iya tambaya ta me ya faru bayan scene ɗin da kika yi yanzu?"
« A kan me kake magana? » Tambayar da Khadija take son yi masa, amma ta san idan tayi zai fahimci akwai abinda ke faruwa. Dan haka ta yanke bashi hakuri kawai.
“Please kayi haƙuri, na sha wasu magunguna ne da zan zo. Ina tunanin su ke sa ina yin wani abun.”
“Me yasa kika sha magungunan?” Ya tambaye ta.
“Ciwon kai ne ya ɗan dame ni."
“Idan waddanan magungunan suna sanya ki irin wannan abun, ki daina shan su mana."
“Kar ka damu baby, i'm so sorry."
“Ba komai, ya wuce."
“Thank you my love."
“Na gaji ni, tashi mu je gida." Ya faɗa tare da cewa a kawo masa bill.
Khadija na son tsayawa amma babu yanda ta iya.
Bayan ya biya bill ɗin sun fito daga restaurant zuwa wajen parking. Tafiya suke shuru babu wanda yace ƙala. Saidai sun kusan ƙarasa wajen parking ɗin yaji wata murya da ya sani.
“Ni dai Maryam ba haka muka yi da ke ba!!"
“Cewa Mansoor zai kai ki gida lami lafiya ko kuwa Habib da zai yi hakan yanzu, ni ban ga wani abu ba a ciki Zahara !”
Zahara ce ! Kamal ya faɗa yana neman inda muryar ke fitowa. Hango su yayi ɗan nesa da su kaɗan.
“Tsoro na kike ji Zahara?" Cewar Habib.
“A'a kawai ita tayi min alƙawarin zata mayar da ni gida!"
“Toh mu daga nan hotel zamu wuce, idan kuwa riƙon kwalba zaki yi mana sai ki zo muje !”
Harara Zahara ta kwaɗawa Maryam.
“Mu je Habib kafin dare ya yi.” Zahara ta cewa Habib da tun ɗazu yake dariyar dramarsu.
“Idan baki son zuwa gida yanzu, zaki iya zuwa wani wajen ke da Habib. Yasan lungu da saƙo na garin nan."
“Ya isa haka Maryam, ku dai ku je abinku." Cewar Habib.
“Ku daina takurawa matata. Tana da gaskiya, idan baku son zuwa gida yanzu. Kuna iya zuwa wani gurin." Cewar Mansoor.
“Kin ga mu je Zahara, rabu da su."
A ɓangaren Kamal, ya kasa ɗauke idanunsa daga kan Zahara. Yanzu da yake kusa da ita, sai yaji kamar duk wata soyayya tata da yake ji ta dawo lokaci guda. Ya ji kamar abinda yake ji game da Zahara an dakatar da shi ne. Yanzu.. kuma yana jin kamar ya ruga wajenta, ya rungume ta sosai a jikinsa. Ya kasa fahimtar meke faruwa.
Tambayar kansa yake ko wanene wannan mutumin da yake tare da Zahara, me yasa suke da kusanci haka? Me yasa Zahara zata yi masa haka? Me yasa take yiwa wannan mutumin murmushi? Me yasa? Me yasa? Me yasa?
Ita kuwa Zahara yayin da take ƙoƙarin shiga mota tayi ido biyu da Kamal yana kallonta. Kallon juna suka shiga yi na wasu ƴan daƙiƙu kafin ta share shi, ta yi shigewarta cikin mota.
Kamal matsawa yayi da niyyar zuwa ya fiddo Zahara daga cikin motar mutumin nan domin ya yi mata magana amma Khadija ta riƙe hannunsa har motar su Zahara ta tafi.
“Kamal ina kake ƙoƙarin zuwa?" Khadija ta tambaye shi.
Juyowa yayi ya kalle ta a hankali kamar a mafarkin ido biyu.. Ya fara fahimtar abinda ke faruwa da shi tsawon duk wannan lokacin.
---------------------------------------------------------------------------------------------
To be continued...
AMRIYA ☠️
(Hatsabibiyar Aljana)
Love 💞 and Horror ☠️ story📖
By Malik al-Ashtar 🖋
Table of Contents
Chapters
- 1 Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
- 2 CHAPTER 1
- 3 CHAPTER 2
- 4 CHAPTER 3
- 5 CHAPTER 4
- 6 CHAPTER 5
- 7 CHAPTER 6
- 8 CHAPTER 7
- 9 CHAPTER 8
- 10 CHAPTER 9
- 11 CHAPTER 10
- 12 CHAPTER 11
- 13 CHAPTER 12
- 14 CHAPTER 13
- 15 CHAPTER 14
- 16 CHAPTER 16
- 17 CHAPTER 15
- 18 CHAPTER 17
- 19 CHAPTER 18
- 20 CHAPTER 19
- 21 CHAPTER 20
- 22 CHAPTER 21
- 23 CHAPTER 22
- 24 CHAPTER 24
- 25 CHAPTER 23
- 26 CHAPTER 25
- 27 CHAPTER 26
- 28 CHAPTER 27
- 29 CHAPTER 28
- 30 CHAPTER 29
- 31 CHAPTER 30
- 32 CHAPTER 31
- 33 CHAPTER 32
- 34 CHAPTER 33
- 35 CHAPTER 34
- 36 CHAPTER 35