Chapter 14
CHAPTER 13
⚖ HOME OF QUALITIE'S WRITERS ASSOCIATION 📚
Zahara ce a bakin Window, tana kallon yanayin garin mai cike da ban sha'awa. Ta nutsu tana tunanin rayuwa, tun bayan abinda ya faru ita da Amriya, Alkur'ani ne da salloli da Azkar ne kadai suke iya kwantar mata da hankali. A halin yanzu ta mayar da hankalin ta kacokam kan addini, har makarantar dare take zuwa duk weekend. Sabuwar rayuwar da ta kirkirarwa kanta kenan..
Karatun da take zuwa ya bata damar dan sakewa da rayuwa ba kamar baya ba. Saidai ta kasa manta ita ce silar rushewar soyayyar oganta. Ta cigaba da zuwa wajen aiki, kuma ita ce shaidar halin da Mr. Ammar yake ciki. Mutumin da ya kasance a kullum cikin raha da kazar-kazar, amma yanzu ya canza. Ya daina mayar da hankali a aiki, ya daina murmushi, ya daina dariya, magana ma ya daina idan ba ta zama dole ba. Haka kayan jikin sa sai yanda yaso yake zuwa da su. Duk ma'aikatan sa sun damu da halin da yake. Kuma duk wannan a ganin ta itace sila.
Kamal yana iya kokarin sa ganin ya nuna mata ba laifin ta bane, amma ta kasa kawar da muryar dake nuna mata laifin ta ne. Tun ranar da Kamal ya bata wannan wayar, bai daina kiranta ba yana jin yanda take. Da farko kananan sakonni yake turo mata, da kawai na tambayar ya jiki ne... Amma wata rana zuwa karfe dayan dare, kusan tana bacci, taji sautin shigowar sako a wayar.
“Bacci kike?”
Sai da ta karanta sakon so ba adadi, farat daya kuma taji ta daina jin baccin. Sai da ta jira na kamar mintuna goma kafin ta tura masa amsa, bata son yayi tunanin ko daman tana jiran sakon nasa ne ( duk da kuma hakan ne.)
“A'a, not yet.”
Ta mayar masa da amsa a takaice. 5 min.. 10 minutes bai turo wani sakon ba. Har ta fara tunanin ko dan bata mayar masa da amsa da sauri bane. Sautin karar kiran wayar ne ya dawo da ita daga tunanin da take. Koda taga sunan sa a jiki, gabanta ya fadi. A zuciyar ta tace “Wayyo Allah, murya ta a wannan lokacin, kar fa ya tsorata.” Sai da tayi ta hada yawu sau ba dadi, kafin ta dauki kiran. Tana mai gyaren murya idan ba haka zai dauka da kato yake magana. A cewar ta.
Sallama tayi, ya amsa sannan yace
“Fatan dai ban takura ki ba?”
“A'a babu abinda nake yi.” ta bashi amsa.
Bata san ya zata siffanta alakar dake tsakanin su ba. Tana son ta sanshi sosai... Tana jin kullum tana kara kusanci da shi, lokaci daya kuma tana jin tsoro. Bata da wani kwararan experience a wannan fannin. Karancin yarda da kai dake gare ta, ya hana ta gasgata abinda zuciyar ta ke raya mata. A tunanin ta, wane mutum zata iya birgewa, babu wani abu special a tattare da ita. Wata kil, ko Kamal dake dan kula ta yana turo mata da messages, tausayin ta ne kawai yake ji. Ita ma tana son jin abinda sauran mutane ke ji, amma tana tsoron abinda zai biyo baya.
“Hello, are you there?” Ya tambaye ta.
Ta bace a cikin tunani, muryar sa ce tayi nasarar dawowa da ita.
“Bacci kike ji? Idan kina so zan iya bari sai da safe muyi maganar.”
Bata son ya katse kiran.
“A'a bana jin bacci.” Ta fada a takaice.
“Ok, gobe kin zo wajen aiki ko?"
“Eh.”
“Ammar yace min kuna da seminar a Madawa, ai kin shirya da kyau ko?”
“Yace min kwana biyu ne zamu yi a cen. Har na fadawa iyaye na, sun amince.”
“Ah, ok good. Nima cen zan je. Idan kina so zamu iya yin tafiyar tare.”
“Ummh..”
“Kar ki damu da dan uwana, motar mu zata kasance a bayan motar shi ne. Kanwar mu ma Afnan tare zamu je, zasu iya tafiya tare. Kuma ina tunanin akwai abokanan aiki da suma zasu je.”
“Eh akwai Hajiya Hasana da mijin ta, Ibrahim da kuma Sarat.”
“Hajiya Hasana da mijin ta suna da motar su, Dan uwa na kuma zai iya daukar Ibrahim, Afnan da Sarat. Ni da ke kuma sai muje a mota ta.”
A ranta tace me yasa yake son dole sai sunyi tafiyar nan tare.
“Idan hakan zai takura miki, ba damuwa Zahara. Amma ba cizon ki zan yi ba.” Ya fada a hankali.
Ji tayi tamkar yana kusa da ita, yayi mata rada ne a kunne. Wani kadawa hanjin ta suka yi... Ya kamata ta kawo karshen abun nan.. tun kan ayi nisa.. ba zata yarda ta sa a ranta abinda ba shi yake nufi da ita ba.
“A'a babu takura amma nafi son tafiyar da Sarat. Domin akwai ayyukan da zamu karasa kafin mu isa cen.”
Bai bata amsa ba.. amma tana jin sautin numfashin sa. A ranta tace wata kil ta yarfa shi ne. Da ta samu wani excuse din ba wannan ba. Domin tasan ya gane kawai ta kirkiri hakan ne dan kar tayi tafiyar da shi.
“Ok.. sai mun hadu a Madawar kenan.” Ya fada cikin sanyin murya.
“Ok.. Allah ya kai...”
Katse wayar yayi ba tare da ta karasa magana ba.
A ranta tace, da gaske kenan hakan yayi masa zafi. Eh gara hakan da taje ta wahala.
Duk tace hakan, sai gashi ta kasa komawa bacci. Ta kasa daina tunanin yanda zata yi idan ta hadu da shi gobe. Ba zata iya sanar dashi gaskiyar dalilin da yasa bata son yana shige mata, zai dauke ta a matsayin mahaukaciya kuma wata kil yayi mata wulakanci. Idan tana kauce masa, irin haka ba zata faru ba.
Saukowa tayi daga bisa gado, lokacin da taji sautin tafiyar Mama cikin corridor. Idan bata yi sauri ba, zata iya yin latti. Anyi sa'a ma har ta shirya jakar tafiyar ta tun jiya. Abayoyi ne da ta siyo da dadewa kadai zata da su. Tayi niyyar canza saka kayan ta masu rufe jiki, domin kare kanta daga maza da kuma aljanu. Sarat sai da ta kusan faduwa lokacin da taga abayoyin. A cewar ta Zahara har yanzu matashiya ce, ya kamata taci moriyar matasantakar ta. Wannan shigar ta aje ta zuwa gaba. Saidai abinda Sarat bata sani ba, mutuwa bata sanarwa kuma babu ruwan ta da yaro, babba ko tsoho. Da jin za'a yi wannan tafiyar, Sarat sai da ta dan yi shopping na dogayen riguna masu kyau da sauran kayan kwalliya.
Zahara fitowa tayi daga wanka, sannan ta shirya. Koda ta fito daga dakin ta da jakar ta, Mama ta tari gaban ta.
“Ki kula sosai Zahara, kar ki kuskura ki cire layar nan daga hannun ki. Koda zaki ganin wata matsala, kiyi gaggawar kira na. Na yarda da ke, shi yasa na barki kiyi wannan tafiyar, kin san da hakan koh?”
“Kar ki damu Mama, zan kula sosai.”
“Ok, Allah ya tsare. Ku dawo lafiya.”
“Ameen ya Rabbi. Sai na dawo Mama.”
Sai da Mama ta raka ta har bakin hanya ta shiga dan sahu sannan ta dawo. Sarat ce ta turo mata msg kan cewa tana bakin kamfani, abinda ya baiwa Zahara mamaki kenan, ganin ga komai sai Sarat tazo latti. Amsa mata tayi da gata nan isowa nan da mintuna. Amma ba ita ta iso ba sai bayan rabin awa, domin lokacin kowane mutum ya fito neman na abinci. Koda ta isa, har motocin sun zo, nan ta hangi Mr. Ammar, Sarat, Hajiya Hassana da kuma mijin ta. Saidai babu alamun Kamal amma motar sa na nan. Da sauri ta biya Mai Dan sahu ta fiddo jakar ta. Koda Sarat ta tsinkayo ta, ta tinkari inda take.
“Haba Zahara, me zaki yi da wannan karamar jakar? Ciki kika sa duka kayan ki? Ni kananan akwatina biyu nazo da su. Ba wanda yasan me zai faru a cen.”
“Kwana biyu kawai zamu yi a cen Sarat. Kuma aiki ne zai kai mu.”
“Ke kike ganin haka, amma ni holewa zan je. Oya muje sauran har sun iso.”
Bin bayanta Zahara tayi, tana gaishe da wanda ta gamu da su.
“Kokarin kiran ki nake yanzu.” Mr. Ammar ya cewa Zahara. “Tinda kin zo zamu iya tafiya. Ku shiga nan.”
“Ibrahim, kai da Sarat zaku shiga mota ta. Hajiya Hasana da mijin ta zata tafi. Shi kuma Kamal zai biyo bayan mu shi da Afnan.”
Zahara taso tambayar Sarat inda Kamal yake, amma bata samu damar hakan ba. Koda suka shiga motar, Mr. Ammar yayi mata key. Motar su Hajiya Hasana na bayan tasu. Ibrahim na gaba shi da Kamal. Zahara da Sarat kuwa na baya suna ta hira. Ko ince Sarat na ta zuba, Zahara na sauraron ta ba tare da tace kala ba. Amma koda Sarat tace mata, hankalin Mr. Ammar take son jawowa kanta. Lokacin ne Zahara tayi magana.
“Yana da budurwa, ya kamata ki daina yin hakan.”
“Ji wata magana.. ke da kanki kika ce ina burge shi. Kuma ma doguwar rigar da ya bani har yanzu tana nan. Bansan wani wasan kwaikwayon yake yi ba, amma na tabba yana bukatar na dan tunzura shi.”
Zahara a ranta tace wannan ma aikin Amriya ne. Bata san me yasa tayi hakan ba, amma dole ita zata gyara kuskuren.
“Bansan me yasa na fada miki hakan ba, amma bana tunanin Mr. Ammar yana jin wani abu a kanki...” Zahara ta fada mata cikin rada dan kar su Ammar su jita.
“Toh me yasa zai mini kyautar wannan tsadaddiyar rigar? Dakata Zahara, bansan me kike nufi ba, amma ba zan saurare ki ba. Ina son yin soyayya ta gaske da shi, dan haka babu abinda zakk fada min, ki sani.”
“Kuskus din me kuke yi ne haka yan mata?” Cewar Ibrahim da sigar wasa.
“A'a ba komai, mun dai kagu mu kai ne.” Cewar Sarat.
“Ah na gani, kar dai a manta aiki ne zai kai mu.”
“Eh, mun sani.” Sarat ta sake fada.
Duk wannan lokacin Mr. Ammar bai ce ko kala ba. Da alamu yana cikin yanayin da ya shiga ne kwanan nan kuma Zahara bata daina tunanin abinda ya faru da budurwar shi ba. Kuma idan Sarat ta shigo cikin labarin, wani hargitsi zata sake haifarwa.
(.....)
“Ke..Zahara..!”
Zahara taji ana girgiza ta cikin bacci. Sai da ta dauki lokaci kafin ta farka daga baccin da take. Bata ma san lokacin da bacci ya dauke ta ba. Sarat ce a kanta tana kokarin tashe ta.
“Ki tashi mun kusa karasawa.”
“Mene..?” Zahara ta fada cikin yanayin bacci.
Tashi tayi daga jikin Sarat tana murza idanun ta dan ta gani da kyau. Gyara gyalen ta tayi, tana kokarin dawo da natsuwar ta.
“Zahara sai kace kasa." Cewar Ibrahim. “Kinsan kira nawa nayi miki dan ki tashi, amma kamar wacce tayi doguwar suma. Injin dai kin samu yin mafarki mai dadi?”
Murmushi kawai Zahara tayi ba tare da ta bashi amsa ba. A lokacin Mr. Ammar yana faka motar a bakin wani hostel. Kyakyawan wuri ne sosai, da ya dauki hankalin Zahara ta yanda bata jin duk wani sauti dake kewaye da ita. Kyan wurin yasa taji tana son daukar hoto. Da sauri ta fiddo wayar da Kamal ya ara mata ta shiga daukar wurin hotuna da video.”
“Wow Zahara, a ina kika samu wannan wayar? Mu gani.” Cewar Sarat tare da warce wayar daga hannun Zahara. Saidai cikin rashin sa'a wayar ta fadi kasa. Gaban Zahara ne ya fadi. Da sauri ta duka ta dauko wayar. Saidai wayar duk ta kwankwatse.
“Wayyo Allah.. I'm very sorry Zahara. Wlh ba da gangan nayi ba."
Wayar tana aiki duk da faduwar da tayi, saidai Zahara bata san ya zata yi wajen biyan mai wayar ba. Ko albashin ta na shekara guda ba zai isa ba.
“I'm very sorry. Dan Allah Zahara. In ga wayar.” Sarat fada.
Amma Zahara bata bata amsa ba, tayi gaba ba tare da tace komai ba. Tayi alkawarin kula da wannan wayar. Me zai ce game da ita kenan yanzu?
Su Hajiya Hasana suka karaso daidai lokacin. Mr. Ammar yayi wani waje sai gashi ya dawo bayan wasu mintuna. Ya fada musu ma'aikatan hotel din zasu zo su gwadawa kowa dakin da zai zauna. Zahara tayi tunanin zasu jira Kamal ne, amma Mr. Ammar bai ce komai ba. Dan haka suka wuce domin hutawa. Zahara santin kyawun wurin kawai take. Zuwan ta na farko kenan irin wannan kyakyawan wurin. Haka ma Sarat tana ta surutun ta game da kyan wurin. Koda suka karasa dakin da aka basu. Sarat tayi tsalle bisa gado.
“Wow wurin nan ba karamin kyau gare shi ba, da har ya fara sa ina jin wani yanayi. Yi tunani a ce ni matar Mr. Ammar ce? Ba bukatar sai nayi aiki, zan kasance kullum a makale da shi. Zan zama tauraruwa a kasar nan.”
Ba tare da Zahara ta tanka ta ba, ta cigaba
“Kina dage min kai ne saboda na fashe miki waya? Nace miki kiyi hakuri, to me kuma kike so?"
“Bar zancen Sarat." Zahara ta fada a sanyaye.
“Wa ya baki wayar? Ba irin wacce zaki iya siye da kudin ki bace, ki cewa wanda ya siya miki da ya gyara miki ko ya sauya miki."
Zahara bata ma san dalilin da yasa take sauraron duk wannan shirmen da Sarat take fada ba. Bathroom ta shiga tayi wanka. Sun samu kamar hutun awa biyu, kafin Mr. Ammar ya kira su domin suyi summarazing abinda zasu yi gobe. A wani private room suka hadu, kowa yazo banda Kamal da kanwar su.
Mr. Ammar ya fara magana, yayi musu bayanin abinda yake son yi da wanda su zasu yi.
Meeting din sai da kwashi kusan awa uku kafin su kare. Bayan nan, aka kawo musu abinci da abin sha.
Zahara ta mayar da hankali akan abinda aka zuba mata, lokacin da aka bude kofa. Tayi tunanin ko ma'aikatan hotel din ne, amma katuwar muryar Kamal tasa ta gane ba ma'aikatan bane. Shine da kanshi, a bayan ta shi da Afnan.
Afnan sai da ta zagaya table din ta gaishe da kowa kafin ta zauna kusa da dan uwan ta. Shi kuwa Kamal kusa da Zahara ya zauna, alhali table din babba ne kuma akwai wuraren zama. Zahara bata yi gangancin dago kai ba.
Mitsinar Zahara, Sarat tayi a kafa sannan ta rada mata a kunne
“Ina jin kanshin turaren sa har nan. Hadadden guy ne, naso in gwada da shi inda ba miskili bane.”
“Let me eat please.” Zahara tace mata.
“Ai sai kiyi ta yi.” Sarat ta fada tare da jan dan guntun tsaki.
Hira a wurin ta barke. Har Mr. Ammar da yake a kame sai gashi yana dan kokarin magana da Sarat, ita kuwa abinda take so kenan. Sai kuma Zahara da ta mayar da hankali kan plate din ta, ko ince tayi kamar hankalin ta na ga plate alhali duk a takure take ganin Kamal na kusa da ita, da shima ba magana yake ba sai sauraro.
Zuwa wani dan lokaci, Zahara taji kafar sa ta hade da tata. Dan zabura tayi, tare da bashi hakuri domin tayi tunanin ko ba da gangan yayi ba. Bai ce komai ba, ya shiga zubawa kanshi abinci. Lokacin da ya shafi hannun ta domin ya dauki gishiri, nan ta gane dazun ma da gangan yayi.
Abun sa fa ya fara yawa, Zahara har ta fara da nasanin sakar masa fuska. Yana tunanin ita irin yan matan nan ne? Sai yanzu take jin haushin amsar wayar shi da taimakon ta da yayi. Ta tabbatar tun ranar da ta kwana gidan shi, yake tunanin ita yarinya ce mai sauki kuma zai iya samun damar ko me yake so da ita. Dole ma ta taka masa birki tun kan yayi nisa.
“Please zamu iya yin magana?” Zahara ta tambaye shi ba tare ta bari sauran sun jiwo ta ba.
Da mamaki ya kalle ta kafin ya amince. Tashi tayi daga kujerar ta tare da neman uziri ga sauran. Fita tayi waje tana jiran shi. Bayan wasu yan mintuna shima ya fito.
Nufar wani lambu dake cikin hotel din tayi, yana biye da ita a baya. Kafin su karaso cikin lambu Zahara ta tattara duk wani kuzarin ta, amma koda ya kasance daga ita sai shi sai duk kuzarin ya bace. Shi kuwa kallon ta yake da dan guntun murmushin sa. Zahara kuwa takaici ne na rashin tattaro kalaman da zata yi amfani da su wajen bayyana masa abinda take ji.
Yanke shawarar ta fara da mai muhimmanci tayi. Ta ciro fasashiyar wayar shi ta miko masa.
“Na kayar da ita ba da gangan ba amma zan biya ka. Ina son ka fada min nawa ne screen din ta yake, zan yi iya kokari na ganin na gyara maka ita.”
Kallon wayar yayi kafin ya kalle ta.
“Kin samu wata sabuwar wayar ne?” Ya tambaye ta ba tare da ya karbi wayar ba.
“No, but I don't need your help anymore. Ina jin kana tunanin ni yarinya ce mai sauki, wacce zaka iya yin yanda kake so da ita. A shekaru ka girme mini, amma ba hakan ya nuna zaka juya ni ba ta sauki. Idan saboda na kwana a gidan ka ne kuma ka taimaka min shi yasa kake min haka, toh ka sani ba dan naso hakan ta faru ba. Abinda ya faru a daren nan, babu inda zan je ne da ya wuce wajen ka. Kuma ma zai iya yiyuwa baka yarda da labarin da na baka game da Amriya ba...”
[03/03 à 05:18] ASHTAR: AMRIYA
(Hatsabibiyar Aljana)
Love 💞 and Horror ☠️ story 📖
By Malik al-Ashtar 🖋
For more novels https://bit.ly/3Egdy1m
On wattpad : https://www.wattpad.com/story/270492485
Table of Contents
Chapters
- 1 Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
- 2 CHAPTER 1
- 3 CHAPTER 2
- 4 CHAPTER 3
- 5 CHAPTER 4
- 6 CHAPTER 5
- 7 CHAPTER 6
- 8 CHAPTER 7
- 9 CHAPTER 8
- 10 CHAPTER 9
- 11 CHAPTER 10
- 12 CHAPTER 11
- 13 CHAPTER 12
- 14 CHAPTER 13
- 15 CHAPTER 14
- 16 CHAPTER 16
- 17 CHAPTER 15
- 18 CHAPTER 17
- 19 CHAPTER 18
- 20 CHAPTER 19
- 21 CHAPTER 20
- 22 CHAPTER 21
- 23 CHAPTER 22
- 24 CHAPTER 24
- 25 CHAPTER 23
- 26 CHAPTER 25
- 27 CHAPTER 26
- 28 CHAPTER 27
- 29 CHAPTER 28
- 30 CHAPTER 29
- 31 CHAPTER 30
- 32 CHAPTER 31
- 33 CHAPTER 32
- 34 CHAPTER 33
- 35 CHAPTER 34
- 36 CHAPTER 35