Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 3

CHAPTER 2

Amriya Hatsabibiyar Aljana Book 1 Complete Hausa Novel 4,607 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book


*HOME OF QUALITIE'S WRITER'S ASSO📚*
_(The Home Of Qualitative Writers That Are Educate Humanities)._
https://www.facebook.com/100495222137315/posts/100496042137233/?substory_index=1&sfnsn=mo

*[📝I.W.A📝]*

Kowa a offishin yaji irin karar da ta fito daga corridor, hatta Mr. Kamal da shigowar sa kenan. Haka ma Mr. CEO duk da nisan dake akwai tsakanin offishin sa da corridor yaji wannan karar. Saving aikin da ya fara a computer yayi tare da fitowa da sauri domin ganin meke faruwa. Yana fitowa yayi kicibus da yayan shi Mr. Kamal da shi ma karar ce ta fito dashi.

“Karar meye wannan?” Mr. CEO ke tambayar dan uwan sa. Shi kuwa daga masa kafada kawai yayi a matsayin amsa.

Nufar inda suke tunanin karar ta fito suka yi. Tun daga nesa suka tsinkayi kamar alamar mutum a kwance. Sai da suka karasa Amar ya gane Zahara ce. Tambayar kansa yake abinda ya faru da har ta tsinci kanta a nan. Tsoro ne ya kama shi ganin ya tabata bata motsa ba. Durkusowa dan uwan nasa yayi tare da taba jijiyar hannunta kafin yace :
“Suma ne tayi.”

Ajiyar zuciya Amar yayi, cak ya dauke ta ya nufi office din sa da ita. Shi kuwa dan uwan sa ya tsaya tattare takardun da suka zube a kasa.

Aje sakatariyar tasa Amar Yusuf yayi kan doguwar kujerar da ke a offishin nasa. Kokarin tayar da ita ya shiga yi a hankali amma bata tashi ba. Dan uwan sa ne Kamal Yusuf ya shigo, ya ajiye takardun bisa desk din Amar kafin ya samu kujera ya zauna. Amar kokarin kiran likitan su yake domin yayi gaggawan duba Zahara, amma ya dakata sakamakon ganin ta fara motsi. Kokari take ta tashi zaune da sauri yazo ya taimaka mata ta zauna.

A bangaren Zahara kuwa, har yanzu hankalin ta bai dawo jikin ta ba, bata iya tuna komai ba. Razanar da tayi yasa ta manta a wajen aiki take.

Sunan Mama ta kira tana murza idanun ta. Tana kallon wanda ke a gaban ta, da har yanzu dishi-dishi take ganin sa. Sai dai lokacin da ta fara dawowa hayyacin ta, ta fahimci hannuwan da ta taba yanzun ba na Mama ba ne. Daga kanta tayi anan tayi arba da fuskar Amar wato ogan ta. Da sauri tayi baya tana mai tashi daga kujerar. Kamal da ya mayar da hankalin sa ga wasu takardu ya dan juyo ya kalle su.

“Dan..dan..dan..Allah..ku..kuyi hakuri, ban..bansan me nake..yi..ba anan.” Zahara ta shiga i'i'na tana bada hakuri ba tare da tsayawa ba.

“Suma kika yi, shi ne na kawo ki nan. Lafiyar ki kuwa?” Cewar Amar.

“Dan..Allah..kayi hakuri, ba da gangan...”

Wai hakuri take badawa da suman da tayi? Kamal ya fada a zuciyar sa tare da sake kallon su karo na biyu.

“Me yasa kike bani hakuri? Ba fa da gangan kika yi ba. Toh saboda me ma zaki yi karyar suma? Zauna ki huta, bari na kirawo doctor.” Amar ya fada da sigar umarni amma Zahara ta cigaba da bashi hakuri.

“Kayi hakuri, ban so in takura ka ba.”

Kamal da ba shiga lamuran mutane yake ba, yaji halin Zahara ya takura shi yace :

“Bayar da hakurin ya isa haka, ki jira ya kira doctor idan kuma ba zaki iya aikin ba ki tafi gida.” Ya fada da kakkausar murya da alamun an takura shi.

Wannan ne karon farko da ya fara yi mata magana tun zuwan ta kamfanin nan. Ya fada mata hakan ne yana kallon ta cikin ido. Hakan kuwa ya tsorata Zahara ba kadan ba. Allah yayi mata dabi'ar bada hakuri ba tare da ta tsaya taji ita ke da laifi ko kuwa. Bata son tashin hankali ko kadan shi yasa da abu ya hada ta da mutum take kokarin su rabu lafiya.

“Kina son na kira likita ne ya duba ki? Ko zaki tafi gida ki huta. Zan samu wani sai ya karasa aikin naki.” Cewar Ogan nata.

Juya Zahara tayi tana fuskantar shi tare da cewa zata iya cigaba da aikin nata.

“Bana son na kara tarar dake a kasa. Na yarje miki, zaki iya tafiya idan baki jin dadi.”

A cikin ranta, babu abinda take so kamar zuwa gida, amma bata son taje bayan takurawar da tayi masu. Gashi kuma tana da aiki da yawa, kuma tana son kammala documents din da ya bata dazun. Tunawa tayi da har takardu zata kai a dakin meeting. Amma bata sani ba ko tana da kuzarin da zata kara tunkarar wannan corridor ba. Har yanzu tana tuna abinda taji lokacin da hannun nan ya taba ta. Lokacin da ta juyo bata ga kowa ba. Alhali ita tasan hannu ya dafa ta.

Amar gani yayi sakatariyar sa tayi nisa cikin tunani kuma da ka ganta zaka san akwai abinda ke damun ta. Koda basu wani dade ba a kamfanin nan, yayi wa sakatariyar tasa farin sanin koda yayi mata tambayoyi ba amsa masa zata yi ba. Irin kullum cikin tunani take, ga wahalar fitar magana a bakin ta.. Kamar dan uwan shi. Ya fada a zuciya. Niyyar ya barta taje yake da, amma kafin nan yana son yaji me ya kaita cikin corridor nan.

“Fada mini Zahara, me ya kai ki wannan wurin? Idan ban manta ba cewa nayi ki hado min coffee.”

“Naje na kai wasu takardu ne a dakin meeting.” Zahara ta fada kanta kasa.

Kunya ce ta kamata da ta gayi hakan, domin taje aiken Sarat akan na oganta.

“Na dauka wannan aikin Sarat ce ya kamata ta yi shi?”

“Eh, amma tana wani aikin ne..”

Amar yasan sakatariyar sa karya take masa domin ba sau daya yana kama Sarat ta saka ta aiki ba. Yayi shuru ne da tunanin ko badin ba jima Zahara zata daina yarda Sarat na sata aiki sai dai ba haka abun yake ba. Canza maganar yayi domin baya son yayi ta gaban dan uwan sa da yasan halin sa. In yaso sun yi maganar daga baya.

“Zaki iya tafiya.” Ya fada.

Zahara ji tayi kamar tayi tsalle da jin abinda oganta yace. Zuwa tayi da niyyar daukan takardun amma ya hana, yace ta barsu nan. Fita daga offishin tayi bayan tayi masa godiya. Koda ta rufe kofar office din Amar yaji alamun shi yayan sa ke kallo.

“Wai da gaske wannan ce sakatariyar ka?” Cewar kamal.

Gyada masa kai Amar yayi yana kokarin kunna computer.

“Ban ga alamar iya aikin nan gare ta ba. Anya kuwa tana yin aikinta yanda ya kamata?”

“Tana da kwarewa sosai. Kawai tana da dan sanyin hali ne. Amma tana aikin ta da kyau.” Cewar Amar.

“Gwara ka sallameta idan ba zata iya ba. Domin kana dab da ci baya idan ka barta a matsayin sakatariyar ka.”

Kamal ya kasa gane me yasa dan uwan shi yake iya zama da ma'aikata masu sanyin hali kuma suke iya kallon sa cikin ido. Yasan dan uwan shi da tausayi, yana iya daukan mutum aiki dan ya dinga samun albashi mai kyau ba wai dan kwarewa ba. Bai san iya adadin lokacin da ya kori ma'aikata ba a madadin dan uwan shi saboda rashin kwarewa. Saboda halin dan uwan shi, yake zuwa duk bayan wata uku kamfanin dan bincikawa idan komai na tafiya daidai.

Kamal yana da tsanani idan akan aiki ne. Shi yasa Amar ke tsoron kar ya kori Zahara, domin shi yana tausayin ta sosai. Gashi yanzu saura yan watanni dan uwan nashi yazo duba aikin kamfanin, dan haka zai yi kokari yaga Zahara ta sake da mutane dan ganin dan uwan shi bai koreta ba. Abinda yasa yake son zama da Zahara saboda tana tuna mishi da dan uwan shi, kusan dabi'un su daya, na koda yaushe shuru-shuru da kadaice kansu daga mutane. Abin mamaki ne wata kila amma Kamal yanada karancin yarda da kanshi, amma da yake shi mutum ne very intelligent sai ya zamana yana iya controlling rashin yardar shi.

“Ka barni na tafiyar da ma'aikatana yanda nake so dan Allah, kai ma kaji da naka damuwowin.”

“Ni kai ne damuwa ta, nasan idan na kyale ka, shekara daya tayi yawa ka durkusar da kamfanin nan.”

“Daddy kai ya fara yiwa tayin zama CEO a kamfanin nan amma kace baka da bukata. So please kaji da naka matsolilin, ni nasan yanda nake tafiyar da kamfani na.”

“Zan kyale ka ne duk ranar da ka iya handle emotions din ka.” Cewar Kamal da ransa ya fara baci.

“Ba'a ce dole sai mutum ya zama robot kafin ya iya tafiyar da kamfani ba. Ni ba kamar ka bane Kamal. Ba mai fatan ya zama kamar ka. Ina son naji ni a raye, in yi kuka idan abun kuka ya sameni haka ma dariya idan ina cikin farin ciki. Bana da ra'ayin cire duka wannan kawai saboda aiki.”

Cewar Amar shi ma cikin bacin duk da yasan ya dan wuce gona da iri wajen fadawa yayan sa wannan kalaman. Kuma ya yiwa yayan nasa farin sanin da yasan irin wannan kalaman suna taba shi amma ba zai taba nunawa ba. Sai dai ya kamata ya fada masa gaskiyar abinda yake tunani game da halin yayan nashi.

“Ni ba munafuki bane. Ba zan yi karyar dariya ko kuka ba domin nunawa mutane akwai ni. Ina yin abinda nake ganin ya dace ne, bana bukatar sai mutane sun soni. Amma idan kana tunanin gaba kake da ni saboda kana kewaye da mutane masu sonka, toh congratulations.”

Kamal kayan shi ya shiga tattara yana kokarin barin office din. Shi kuwa Amar yaji bai kyauta ba, kuma ba zai juri fushin dan uwan sa ba.

“Bro, tsaya please... Kayi hakuri akan abinda na fada maka... Ba wai nayi bane dan...”

“Kana bani hakuri ne saboda da gaske kayi nadama ko kuwa dan ka nuna min kai mutum ne mai kawa zuci? Toh ka sani emotions ba zasu amfanin komai ba idan dai ba abinda kake ji bane da gaske.” Kamal ya fada kafin yayi tafiyar sa ya bar dan uwan nasa yana tunani.

A bangaren Zahara kuwa, tsoron da take ji ya sake nunkuwa. Domin motsi kadan sai ta tuna da hannun da ya dafa ta dazun. Ta kasa gano me yake damun ta. Amma yanzun ta fara tunanin ko aljanu ne ke bibiyar ta. Idan kuwa haka ne me aljanun nan suke nema da ita? Me tayi masu? Wata kila idan ta samu tattaunawa dasu zasu fada mata abinda tayi masu, daga nan ma ta nemi yafiyar su, su shafa mata lafiya.

Har wajen karfe sha biyun rana, Zahara na bisa internet tana neman yadda ake korar aljani, ko yanda mutum zai yi magana da aljani mai bibiyar sa. Gaba daya tabi ta karanta duk wani posting dake bayani game da shafar aljanu. A wasu shafukan shawara ta samu akan ta yawaita saka suratul Bakara duk safe da yamma domin korar aljanin. Wasu kuma wuridi suka bata da zata yi da dare domin yin magana da aljanin. Amma ita tafi ganewa saka Al-kurani mai girma.

Tana cikin binciken nata, sai ga Sarat ta shigo a kidime...

“Mr. CEO yana ciki? Yanzu ya kira ni, yace yana nema na.” Sarat ta tambayi Zahara.

“Eh yana ciki.” Zahara ta bata amsa.

Koda ta shiga Zahara ta tuna bata kai takardun da ta bata ba. Oga yace kar ta yi. Ta ma manta da takardun na meeting ne. Addu'a take har cikin ranta Allah yasa dai kar Sarat ta tsane ta. Cikin rashin sa'a kuwa Sarat na fitowa ta wurgo mata wani mugun kallo wanda yasa Zahara shan jinin jikin ta.

“Idan kin san ba zaki je ba, me yasa baki fada min ba da ki je ki kaiwa Mr. CEO su. Ba'a taba wulakanta ni ba irin na yau.” Sarat ta fada kafin tayi gaba.

Idan da ta tsaya da Zahara tayi mata bayani zata fahimci cewa ba laifin ta bane taso da gaske taje ta kai takardun... Amma, koda yake yanzun bata da lokacin wannan, domin matsalar Sarat auta ce a cikin matsalolin da take fuskanta yanzu. In yaso daga baya ta ma Sarat bayani.

Komawa tayi ta zauna ta cigaba da abinda take. Da ta gaji ta aje ta shiga tunanin da ta saba, kafin Mr. Amar ya katse ta, ta dan tsorata domin bata san lokacin da yazo ba.

“Oh sorry na tsorata ki?” Ya fada.

A lokacin ita ko ya kankanin motsi yake ma tsoro yake bata.

“Ah ba komai.” Ta fada tana gyara zaman ta.

“Kin karasa aikin ne?”

“A'a saura kadan dai na karasa.”

“Kadan ya rage? Ok, zaki iya zuwa dashi gida ki karasa. Muje na aje ki, yau kusan unguwar ku zan je..”

Tunani take daman yasan gidan su. Nan take kuma ta tuna wata rana da suka taba haduwa daidai kusan gidan su. Tana tunanin akwai wani da ya sani nan unguwar su.

“A'a kar ka damu sir. Zaka iya tafiya ni ba yanzu zan je gida ba.”

“Umarni ne Zahara. Kashe wannan computer ki same ni a mota ina jiran ki. Na baki minti goma.” Yace mata kafin ya tafi.

A ranta tace me yasa yake son dole sai ya kaita gida. Tafi gane ma ta shiga dan sahu yayi ta gararanba da ita akan ta shiga motarshi ta takure kanta. Ba dan taso ba ta mike ta tattare kayan tabi bayan shi. Ta tabbata yana son yi mata maganar Sarat ne da aikin da take sa ta. Maganar zuci ta fara kafin ta karasa bakin motar “Wayyo Allah, kuma wacce matsalar na sake jawa kaina? Nasan cewa zai yi ba son aikin kamfanin nake ba... Daga karshe ma ya kore ni. Toh kuma idan kora ta zai yi ai ba zai ce min naje da files din gida na karasa aikin.”

Ba zata so ace ta rasa wannan aikin ba, domin a halin yanzu shi kadai take iya yi. Idan har ya kore ta ba zata iya jurewa ba, domin aikin ya fara sawa ta fara yarda da kanta. Ba wai aikin da take mafarkin samu bane, amma tasan idan har tana yinshi zata fara sakewa har nan gaba taje ta nemi wasu kamfanonin na jarida.

Suna zuwa wajen parking, yace ta jira ya fiddo motar. Hakan kuwa tayi, ta labe bakin wata bishiya dan kar wani ya ganta. Domin yanzu mutum ake kiwo ba dabba ba. Sai dai cikin rashin sa'a, lokacin da baka son haduwa da kowa, lokacin ne zaka ga kowa a waje. Sarat dan sahu ko bus ta saba shiga idan zata je gida, amma yau sai gata tare da Hajiya Hasana sun nufo wajen parking. Da ganin su Zahara tayi kokarin guduwa amma aka yi daidai da Mr. Amar ya fito da motar shi kuma ya faka daidai gaban Zahara. Tuni cikin Zahara ya duri ruwa, tsoro da kunya duk sun dabaibaye ta. Ba tare da ta kalli su Sarat ba tayi saurin shigewa mota.

Kin tayar da motar Amar yayi sai da ya gaisa da Hajiya Hasana da kuma Sarat.

“Zahara sannu.” Cewar Sarat tana wani yamutsa fuska.

“Yauwa.” Abinda Zahara ta iya ce mata kenan.

Bayan Mr. Amar yayi musu sai gobe ya tayar da motar.

A saman hanya ba wanda yace kala cikin su. Daman haka Zahara take so, dan bata ma san me zata ce ba. Shi kuwa ta kasa gane dalilin da yasa yayi shuru, domin bata taba ganin sa haka ba.

“Ya jikin naki?” Ya tambaye ta.

A ranta tace ashe nayi azarbabin ganin rashin maganar sa. Ya tambaye ta ya jikin ta ita da ba rashin lafiya tayi ba.

Cigaba yayi dacewa
“Daman kin saba suma ne irin haka? Ko kina fama da wata rashin lafiya ne?”

“Eeh a'a..”

“A'a me?”

“Lafiya ta kalau kuma babu wata rashin lafiya da nake.”

“Oh, tambayoyin nawa ne kika hade kika bani amsa da a'a? I see. Ke ba mai yawan surutu bace. A office naga kullum kamar a takure kike, amma nan kina iya sakin jikin ki. Mu biyu ne kawai anan.”

Abinda bai sani ba, a office din tafi sakewa akan cikin motar shi, domin a cen ba'a cika magana a kanta ba, amma anan ya zamar mata dole tayi magana kuma idan zata yi sai ya kalle ta.

“Kayi hakuri.” Ta fada.

Ji tayi alamun yana kallon ta.

“To shi hakurin na meye Zahara? Kina bani hakuri ne saboda baki da surutu ko kuwa? Wannan ai ba laifi bane. Daga yanzu bana son na kara jin kin bayar da hakuri ba da dalili ba. Da wannan halin naki, sauran ma'aikata sai su raina ki.”

“Kayi hakuri.” Ta sake fada kafin ta tuna abinda baya son ji ne.

Ya jima yana kallon ta kafin ya girgiza kai.

“Ba da gangan nayi ba..”

“Kin san wani abu, ni ban ganin aibun abinda kike yi, amma wasu suna ganin kamar sakarcin ki yayi yawa. Sorry da kalamin.”

“Na sani..”

“A'a baki san irin girman wautar da kike yi ba. A tunanin ki tauye kanki wuri daya, ba zai sa ki samu matsala da mutane ba, amma bari na fada miki mutane sun fi samun dama ga irin ku wajen cimma wata manufa tasu. Ki duba kamar Sarat, na lura kullum cikin saka ki aiki take yi. Kuma ita ba girme miki tayi ba. Na lura da komai amma nayi tunanin wata rana zaki yi wani abun amma naga baki da alama, in banda ni yau da na mata magana da ba zaki taba yi mata ba... Ni ban ce abinda kike yi yana da aibu ba. Ke ma'aikaciya ta ce, kuma hakki na ne na taimaka miki akan abinda ya shafi zamantakewa da mutane. Amma kafin nan kema sai kin yi yaki da tunanin ki. Shi yasa na nemi da na kawo ki gida, dan mu tattauna akan hakan. Dan haka idan kina bukatar wani abun kar kiyi sanya wajen fada min.”

“Nagode sir.”

“Bari yimin godiya. Ina yin hakan ne domin cigaban kamfani. Yayana Kamal zai dawo domin binciken ma'aikata kuma idan har bai tarar da aiki mai kyau ba zai yi sanya ba wajen kora. Duk da ina kokarin na hana shi yin hakan, amma mu biyu muke da hakki akan kamfanin kuma yafi ni kwarewa akan aikin.”

Shuru kowannen su yayi, sai da suka shigo unguwar su Zahara, Amar yace
“Toh ina tunanin idan kika bi nan zaki isa gida da wuri. Ni zan je ganin matar da zan aura ne a cen kwanar take. Nasan ma ba zaki rasa sanin ta ba.”

Zahara bata cika fita ba, dan haka ba lallai bane ta santa.

“Meye sunan ta?” Tayi karfin halin tambayar sa.

“Salmah Idris sunan ta.”

Kamar yanda tayi zato, bata taba jin sunan nan ba a cikin unguwar su. Kowa na burge Zahara amma banda masoya. Bata taba soyayya ba, kum bata tunanin zata yita nan gaba. A nata yin soyayya ba sauki gare shi ba. Bata san ta yaya mutane zasu sota idan bata ao kanta ba. Idan ace tana soyayya, zata dinga tunanin bata dace da mutumin da take soyayya dashi ba. Zata iya tunanin wannan mutumin yafi ta komai ... Kuma ba karamin tabin kwalwa zata samu ba idan yau ya guje ta.

Godiya ta yiwa ogan nata bayan ya aje ta. Yace tayi tunani akan abinda ya fada mata kafin ya tayar da motar. Yan mintuna kadan sai gata a kofar gidan su. Sai da tayi ta konkwasawa kafin wani Cousin din ta Abdul ya bude. Shekarun sa sha takwas kuma yana zuwa gidan au akai-akai.

Gaisawa suka yi, ta tambaye shi ya mutanen gida. Inda Mama take ta tambaye shi, yace mata tana dakin Abba.

Sama ta nufa zuwa dakin Abba. Tana zuwa bakin kofa ta jiwo su suna magana. Juyawa tayi da niyyar zuwa ta watsa ruwa, amma ta tsaya jin sunan ta cikin hirar tasu. Kunnenta ta kara jikin kofar dan jin me suke cewa da kyau.

“Ni ban ce mahaukaciya ce ba, na dai ce tana yin wasu abubuwa masu rikitarwa. Ya kamata muyi wani abu Abban Zahara, ko shawo kanta ne muyi dan taga likitan kwalwa.”

“Wata kila aikin office ne ya takurata kwana biyu, kinsan yanda take. Ba wanda take gayawa matsalar ta, ko kawaye bata da. Dole ki dinga ganin wasu abubuwan ba daidai ba gare ta. Ki bata lokaci nasan komai zai wuce.” Cewar Abba.

“A'a Abban Zahara, kayi tunani idan abun nan ya girmama. Me mutane zasu ce? Abinda ya faru tsakanin ta da Mami ma har yanzu zancen ake.”

“Toh yanzu me kike so ayi?”

“Zaka iya kiran abokin nan naka likitan kwalwa domin yazo ya duba ta. Kuma zamu iya kaita Damagaram wajen Malam Mani mai rukiya. Ni ban ma san ta ina zamu fara ba.”

Jin abinda suke tattaunawa yasa Zahara jin ba dadi. Ashe iyayen ta kallon mahaukaciya suke mata. Amma ya ta iya, tunda bata da hujjar da zata kare kanta. Bayan abinda ya faru tsakanin ta da Mami wa zai rantse yace tana da hankali? Ina ma zata iya bayyana masu abinda ke faruwa da ita. Idan mahaifiyar ta wacce ta haifa ta bata yarda da ita ba, waye zai yarda da ita? Allah yasa bata baiwa Mama labarin komai ba. Da shakkun da take da game da tabin kwalwarta ya tabbata. Kuma Allah kadai yasan irin wahalar da Mama zata sha ganin ta samu lafiya.

Yanzu Zahara ta kara tabbatar da kadaicin ta. Dole ta fara nemawa kanta magani da Al-kur'ani mai girma. Yanzu ta tabbatar akwai abinda ke bibiyar ta. Bata san me yake so ba, amma zata kare kanta da kur'ani. Sports Hall ta nufa, dakin motsa jiki da ta share ta mayar nata. Katifa ce cikin sa, sai wasu daga cikin kayan sawarta. Dawowar ta nan yana daga cikin abinda ya kara daga hankalin Mama. Ita kuwa tayi hakan ne domin gujewa dakin ta. Bacci mai kyau take samu tunda ta dawo nan. Duk da tsoron nata bai ragu ba, amma ta daina ganin wasu abubuwan na tsoro.

Kwantawa tayi kan katifar ta, ta shiga tunanin yanda zata bullowa sabuwar matsalar ta, wato Mama. Idan ba haka ba kuwa zata kare a gidan mahaukata, ko kuma a hannun wani dan tsubbun da zai yi tunanin warkar masu da ita.

Zahara tana cikin wannan tunanin nata, taji kamar alamun bacci ga kuma wata uwar gajiya da tazo mata. A hankali idanun ta na rufewa tana bude su. Tana cikin wannan yanayin taji an kira sunan ta.

“Zahara....!”

Da sauri ta bude idanu, sai dai ganinta ba a cikin dakin motsa jiki da ya dawo dakin ta ba tayi, wani daki ne da bata taba gani ba. Dubawa tayi gefen ta, nan ma taga ba a bisa katifar ta ba take kwance, bisa wani tamfatsetsen gado ne take. Ba tare da ta iya motsawa ba, ta shiga kalle-kalle da idanun ta...hadadden dressing table, katon madubi... littafai da hotunan shahararrun mawaka da yan film ne a cikin dakin. Kokarin tashi take amma kafafun ta kamar babu su jikin ta, kai kawai take iya motsawa.

“Dan Allah akwai mutum anan?” Ta fada muryar ta na rawa.

Tsoro take ji iya tsoro. Bata san a inda take ba. Runtse idanu tayi tana hawaye da tunanin ko zata bude ta ganta cikin dakin ta. Sai dai babu alamun mafarki ne take.

Kuka ta shiga rerewa mai ban tausayi. Domin shi kadai ne take tunanin yi a halin yanzu.

“Me yasa kike kuka ne Zahara?” Ta sake jiwo muryar dazu da ta kira sunan ta.

Zahara waigowa tayi, sai dai wacce ta gani yasa ta kara razana. Amriya ce dan nesa da ita, har yanzu da kyanta da yanzu Zahara take gani yafi komai muni. Kallon ta Zahara ke yi ba ko kyaftawa, ita ma haka Amriya ta tsura mata idanu na wani dan lokaci kafin kamar da kyaftawar ido ta iso gaban ta.

Duk da tsoron da Zahara take ji, tana son yiwa Amriya magana, ta tambaye ta duk wannan abun, ko mai sabon hauka ne ke yin shi. Sai dai tuni Amriya ta riga ta yin magana cikin kakkausar murya tace

“Toh kawata ya kike?”

Zahara shakku take na yiwa Amriya magana. Ita da take son haduwa da abinda ke bibiyar ta, yanzu gata gaban ta, bata san ta ina zata fara ba.

“Kin san dai ba cizo nake ba ko?” Cewar Amriya.

“Wacece ke?” Zahara ta samu karfin halin fada.

“Ni nice, ke kuma kece Zahara.”

“Ba sunan ki ba Aisha?” Cewar Zahara.

Kallon ta Amriya tayi da murmushin ta da bai barin fuskantar ta.

“Ni ba Aisha bace, sunana Amriya.”

“Toh me yasa kike kama da Aisha?”

“Tambaya mai kyau.” Amriya ta fada da dan daga murya, tana mai hawowa kan gadon da rarrafe.

Fuskarta ta kara wani annuri kamar dama tambayar da take son Zahara tayi mata tun da dadewa kenan. Zahara tsoro ne ya kara kamata ta sake kokarin tashi amma har yanzu kafafuwanta a sandare suke...

“Aisha ta mutu kawata.. har yanzu ke baki gane ba?”

“Toh me yasa kike bibiyata? Ni meye laifi na a ciki?”

“Kin fara zama mai surutu Zahara.. Ina son haka!!” Cewar Amriya cike da murna, tana mai kara kusanto Zahara. “Ina son sabuwar kawa ne, saboda Aishata ta mutu. Hakan kuma baya min dadi, kuma naga ke kina da qualities da nake so a gun kawa.”

Kuka Zahara ta sake fashewa dashi tace
“Dan Allah ki fada min wacece ke?”

“Azarbabin me kike yi? Ku dama bil'adama kun cika rashin hakuri. Ada Aisha ma kamar ke take, amma zama dani ya koya mata dangana.”

“Dan Allah ina rokonki ki rabu da ni. Kar ki cutar dani.”

“Zahara har kin manta ke kika amince da kawancen mu? Ba fa dole nayi miki ba. Kamar yanda na fada miki naga wasu abubuwa da dama da ke burgeni a tattare dake.”

Zahara idan da tsoro yana Kashewa da tuni ya kashe ta.

“Ita ma Aisha da farko tsorona take ji amma daga karshe ta yarda da kawancen mu. Sai dai da mahaifin ta ya gano ni, ya nemi ya rabani da ita, ita kuwa Aisha ta yarda da ayi mata magani. Kin ji cin amana ko? Taci amana ta ni kuma na tsani a dauke ni doluwa. Ni kuwa ganin haka, nasa mota ta bi ta kan kawata Aisha. Kina ganin ban kyauta ba?”

Da jin wannan kasan da barazana a maganar ta.

Cigaba tayi da cewa
“Kin sani ni ba muguwa bace. Mahaifin ta mashayi ne, tun tana yarinya yake mata fyade. Kawai ni nazo ne domin na taimaka mata, amma daga karshe ta yarda da zancen mahaifin ta dake son korata daga jikin ta kawai dan ina hana shi yi mata fyade. Aisha butulu ce, shi yasa ta cancanci mutuwa. Shin ni muguwa ce ko kuwa?”

Har yanzu Zahara rusar kuka take, tana kokarin karanto wasu ayoyi da ta sani cikin kur'ani. Sai dai cikin yan dakikun da basu wuce biyu ba, sai ga Amriya dab da fuskar ta yanda har hancin su na gugar juna.

“Shin ni muguwa ce ko kuwa Zahara?” Cewar Amriya, wannan karon cikin bacin rai, dan har kamannin ta sun fara sauyawa.

Domin ta kare kanta, Zahara tasan a wannan lokacin Amriya ba zata so jin abinda ya sabawa ra'ayin ta ba.

“A'a.. tayi kuskure.” Zahara ta fada cikin kuka.

Dariya Amriya ta kyalkyace da ita, alamar amsar Zahara tayi mata dadi.

“Kin gani kin fara ganewa. Da alamu tamu zata zo daya. A tare zamu wataya a duniya ko?”

Zahara bata da wani zabi da ya wuce ta gyada kai, sai dai bata kawo ko kadan a kanta abinda zai faru gaba ba....

AMRIYA
(Hatsabibiyar Aljana)

Love 💞 and Horror ☠️ story 📖

By Malik al-Ashtar 🖋

On wattpad : https://www.wattpad.com/story/270492485

Table of Contents

Chapters

36 chapters
  1. 1 Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
  2. 2 CHAPTER 1
  3. 3 CHAPTER 2
  4. 4 CHAPTER 3
  5. 5 CHAPTER 4
  6. 6 CHAPTER 5
  7. 7 CHAPTER 6
  8. 8 CHAPTER 7
  9. 9 CHAPTER 8
  10. 10 CHAPTER 9
  11. 11 CHAPTER 10
  12. 12 CHAPTER 11
  13. 13 CHAPTER 12
  14. 14 CHAPTER 13
  15. 15 CHAPTER 14
  16. 16 CHAPTER 16
  17. 17 CHAPTER 15
  18. 18 CHAPTER 17
  19. 19 CHAPTER 18
  20. 20 CHAPTER 19
  21. 21 CHAPTER 20
  22. 22 CHAPTER 21
  23. 23 CHAPTER 22
  24. 24 CHAPTER 24
  25. 25 CHAPTER 23
  26. 26 CHAPTER 25
  27. 27 CHAPTER 26
  28. 28 CHAPTER 27
  29. 29 CHAPTER 28
  30. 30 CHAPTER 29
  31. 31 CHAPTER 30
  32. 32 CHAPTER 31
  33. 33 CHAPTER 32
  34. 34 CHAPTER 33
  35. 35 CHAPTER 34
  36. 36 CHAPTER 35
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});