Chapter 26
CHAPTER 25
⚖ HOME OF QUALITIE'S WRITERS ASSOCIATION 📚
Watanni sun shude kuma abubuwa da dama sun faru.
Kamal har yanzu cikin bakin ciki yake tun lokacin da ɗan uwansa ya faɗa masa abinda mahaifinsu ya aikata. Kamal bai iya haɗa idanu da Afnan; babu wanda yake iya yin hakan duk da ƙoƙarin da suke yi wajen nuna kamar komai bai faru ba. Yayyun Afnan din sun yi mata alƙawarin cigaba da kallonta kamar a baya amma bata san kawai dauriya ce suke yi ba. Ba mai yiyuwa bane nuna kamar komai bai faru ba.
A ranar nan lokacin da Ammar ya kira family meeting kuma kowa yazo, har da Kamal da yake asibiti sai da ya nemi da a kawo shi gida. Ya gaji da zaman asibitin kuma wannan meeting din sai ya zamar masa wata dama, duk da ƙaguwar baro asibitin nasa ta ɓace lokacin da yaji gaskiyar dalilin kiran meeting din.
Ammar yazo da Afnan. Daddy kuwa sai muzurai yake, yana kallon Afnan cike da tsana. Yaso yayi wani wasan kwaikwayo a wurin kuma ya tari Afnan hannu biyu saidai hakan bai yiyu ba sakamakon tsanar da yake ji game da yarinyar. Abinda bai sani ba, Afnan ba zata bari yayi magana ba ko yin dramar da ya shiryo ba. Tana jin wani ƙwarin gwiwa a tattare da ita sakamakon kasancewar Ammar a gefenta. Ba zata ce bata jin tsoro ba, amma tana jinta cikin tsaro kuma a shirye take domin tunkarar wannan dodon.
Lokacin da Hajiya Karima ta dawo gida tareda ɗanta Kamal da kuma daya daga cikin nurses na asibitin, Mijinta da Afnan na zaune a falo babu yanayin alkhairi a yanda ta gane su, dandanan ta fahimci meke faruwa. Kuma ta fahimci lallai familynta bai gama rushewa ba.
Cikin yanayin ɓacin rai ta taimakawa Kamal ya zauna. Ta gaishe da mijinta bayan ta ba banza ajiyar Ammar da Afnan. Wuri ta samu ta zauna sannan ta fara magana
“Me ya kawo ku gidana?” Tace da Ammar da Afnan.
“Ki yarda naso kar na sake tako ƙafata cikin gidan nan.” Cewar Ammar.
Daddy da tun dazu yayi nisa cikin tunani yace
“Ɗanki ne ke zargi na da aikata wani abu marar dadin faɗa, har kunya nake ji na furta hakan.”
“Afnan, kin rantse sai kin wargaza min iyali ko? Bayan kin je kin yi karuwancin ki waje shine kike son ni ki zo bata min sunan ahali ko? Me na faɗa miki a baya?”
“Kin san da zancen kenan?” Cewar Ammar da mamaki. “Kuma shine baki ce komai ba?”
“Saboda ƙarya take, kawai tana son wanke kanta ne ta hanyar ɓata nawa gidan. Ba zan yarda da wannan ba!” Cewar Mommy.
“Wai meke faruwa ne?” Kamal ya tambaya da muryarsa ta marasa lafiya.
“Ba komai ɗana, bari na sa nurse ya kai ka tsohon ɗakinka domin ka huta.” Cewar mahaifiyar tasu.
“Ba komai? Wannan mutumin da muke kallo a mahaifinmu shi ya yiwa Afnan fyaɗe.”
Da farko Kamal bai fahimci komai ba, amma da maganar ta rasa illahirin ƙwalwarsa, waro idanu yayi ya kalli Daddy ya kalli Ammar.
“Rufe min baki.” Cewar Hajiya Karima. “Kar na sake jin ka ƙara faɗar irin wannan shirmen ƙanzon ƙuregen da bakinka."
Afnan ɓoye fuskarta tayi da tafin hannuwanta a bayan Ammar. Shi kuwa Daddy gefe yake kallo ba tareda ɗaya daga cikinsu ya canki abinda yake tunani ba.
“Tsaya Ammar. Wannan fa ba ƙaramar magana bace. Na kasa fahimta, kayi min bayanin abinda ya faru.” Cewar Kamal.
Ammar ya fara bashi labarin duk abinda ya sani da kuma yanda yayi ya gane gaskiya. Lokacin da ya ƙare, Kamal ya kalli Afnan yace
“Afnan, dagaske ne abinda ya faɗa?”
Afnan bata ce komai ba na tsawon wasu mintuna.
“Dagaske ne abinda ya faɗa?” Kamal ya ƙara tambayar ta wannan karon gyaɗa kai tayi alamar eh.
Kunya ce sosai ta lulluɓe Kamal ya rasa me zai yi. Wannan ne na farko da yaji kunya na kasancewar shi ɗan wannan mutumin. Ya tabbatar da gaskiyar Afnan da Ammar, yana jin ina ma ace mafarki yake.
“Barin wannan maciya amanar zaka yi su zubar maka da mutunci?” Hajiya Karima ta juya kan mijinta da yayi shuru bai ce komai ba.
“Shikenan a ɗauka da gaske ne abinda ta faɗa, ina son ganin hujjoji. Idan naga hujjojin cewar mijina ne ya yiwa yarinyar nan fyaɗe ni da kaina zan kai ƙararshi."
“Bama bukatar nuna miki hujjah idan baki yarda ba shikenan. Bana bukatar taimakonki wajen yin wani abu. Amma jin cewa kinsan da wannan zancen baki faɗa mana komai ba na gane kin wuce yanda nake tunani. Koda na fahimci kin ƙirƙiri wani labari kawai dan ki kare daddy naji ina son barin gidan nan, na ƙara yin nesa da shi. Kuma ina son ku saurari sammacin kotu."
“Shikenan...” Cewar Daddy da ya dawo hayyacinsa.
“Ban gane shikenan ba? ƙoƙarin wargaza mu fa yake kuma kasan kamfanoni zasu durƙushe.” Cewar Mommy.
Ta ƙara da cewa
“Ina guje maka ranar da zaka san ainihin wacece wannan yarinyar, ranar zaka yi baƙin ciki. Zaka yi nadamar yiwa mahaifinka sharri da kuma juya mana baya da kayi. Kayi nadamar yarda da maganar wannan makirar, rayuwarka ta zama babu komai sai wahala..”
“Wahala ce a rayuwata tun lokacin da na gane abinda iyayena ke iya aikatawa, bana tunanin akwai wani baƙin ciki da yafi wannan. Ina fata adalci yayi halinsa."
“Ina fatan haka nima.." Daddy ya faɗa cen ƙasan maƙoshi. “Zan yi iya ƙoƙarina wajen dawo da mutuncina da ka zubar na yimin wannan mummunan sharrin. Ke kuma Afnan bansan me nayi miki ba da zaki saka min ta wannan hanyar. Bansan cewa sakamakon da zan samu na zamar miki uba da nayi ba shine sharrin fyaɗe.” Ya fada da ƙaramar murya ba tareda ya kalli kowanne daga cikinsu ba.
“Babu abinda kayi, baka buƙatar sai ka faɗa my love. Na yarda da kai, na yarda ba zaka taɓa aikata hakan ba. Allah yana tare da mu.”
Tashi Ammar yayi sannan ya taimakawa Afnan ta tashi.
“Ina fata wannan ne na ƙarshe da zan ganku cikin wannan gidan." Cewar Hajiya Karima.
“Kar ki damu Hajiya koda yunwa zata kashe ni ba zan ƙara saka ƙafata a gidan nan ba." Cewar Ammar kafin ya juya ya cema Kamal sai sun haɗu gidansa.
Kamal bai bashi amsa ba, domin babu wannan kwarin gwiwar a tattare da shi.
Koda suka fita daga gidan Afnan ta fashe da kuka.
“Bana son ka rabu da su saboda ni.” Cewar Afnan.
“Ban rabu da su ba saboda ke. Ki daina faɗar haka bana so. Ki daina kuka please. Idan da gaske kina son ki taimakamin wajen taimaka miki ya kamata ki daina ganin laifinki. Babu laifinki a cikin duk wannan."
“Eh amma..”
“A'a, babu amma. Komai zai yi daidai. Na tabbatar Kamal a ɓarinmu yake. Ba zamu kasance mu kaɗai ba.”
Haka aka yi koda Kamal ya samu sauki, ya nunawa su Ammar da yana tare da su. Makonni sun shuɗe kuma sun shigar da Alhaji Yusuf ƙara kotu. Cikin sa'a suka samu Rakiya yar aikin gidan tace zata bada shaida domin tasan abubuwa da dama. Lauyen Afnan din yace mata lauyen Daddy zai iya tsorata ta akan me yasa bata faɗa ba tun farko amma ya samar mata hanyar da zata bi ta bashi amsa mai kyau ba tare da an zarge ta ba.
A yanzu haka suna cikin haɗa ƙwaƙwaran file ne na shari'ar da za'a yi nan da wata huɗu.
(.......)
Kamal ne ke fama da yin wani zane da zai yiwa wani balarabe da zai bawa matarsa a matsayin kyauta na birthday ɗinta. Kamal yana ɓata lokaci sosai akan zanen dan ganin ya ƙawatu da kyau.
Amma wannan ranar, wani abu na damun Kamal. Yanzu yake tunanin kusan wasu watanni kenan rabon da yaga Zahara ko jin labarinta kuma abun mamakin bayada bukatar ji. Duk lokacin da ya ɗauki waya da niyyar kiranta sai ya manta kuma ba zai sake tunawa ba. Kuma abinda yafi bashi mamaki, baya jin kewarta ko kaɗan. Irin abinda yake ji game da ita duk ya ɓace, kamar ma hakan bai taɓa faruwa ba. Hakan na damun sa sosai domin yayi imani da soyayyar da yake yi mata. Ya kasa fahimtar meke faruwa kuma baya son sanin meke faruwan.
Ya kan ji a duk lokacin da yaso ya nemi sanin me yasa yake sauyawa game da Zahara wani abu na hana shi kuma sai ya tilasta shi mayar da hankali ga wani abun daban.
A ɓangare ɗaya kuma rayuwa sai yiwa Khadija daɗi take. Kowace rana da zata wuce, tana jin ƙara samun kusanci da Kamal take. Bai iya kwana biyu ba tare da yaji labarinta ba, kullum ciki son ganinta yake da son jin muryarta. Har ya nemi da Khadija ta kwana a gidanshi, abinda bai taɓa yi ba a baya kuma yake nadamar aikata shi. Saidai ita Khadija hakan da ya nema bai wani dameta ba.
A wannan daren, sha'awa ta rufewa Kamal idanu. Ya nunawa Khadija adadin yanda take jan hankalinsa. Sun aikata a ko'ina, a falo, cikin kitchen, cikin ɗaki har cikin bathroom ma.
Washe gari, Khadija tayi sauko wajen aiki. Fuskarta cike da annuri kamar wacce aka yiwa albishir da gidan aljanna. Tana cikin murna domin burinta ya cika, Kamal ya kamu da sonta. Me kuma zata nema bayan wannan? Komai ya tafi da sauri ta yanda har yau ta kasa yarda. Abu ɗaya ya rage mata yanzu shine AURE !
(.....)
“Ba dai haka zaki zauna ba, har sai kin ƙarar da hawayenki akan wannan mutumin?" Cewar Maryam tare da dauke pillow din da ta jefawa Zahara.
Komawa Zahara tayi gefen gado tareda share Maryam dake ta faman masifa domin da alamu ta saba.
“Zahara! Wai kina saurare na kuwa? Ki daina wani abu kamar yarinyar ki tashi! Ba zaki ɓata watanni kina kuka akan mutumin da bai damu da ke ba. Ki tuna ajinki mana..”
Wani sabon baƙin ciki ne ya mamaye Zahara, taji kamar Maryam ta caka mata wuƙa amma kuma tasan gaskiya ta faɗa. Kamal bai damu da ita ba.
“Ya isa haka, yanzu ki tashi ki shirya ki je wajen aiki kamar yanda kike yi a baya kafin ki haɗu da shi. Kina tayar da hankalin kowa."
“Idan da kin san yanda nake ji.."
“Ki yarda da ni, nasan abinda kike ji fiye da kowa.” Maryam ta bata amsa cikin sanyin murya wannan karon. “Ba zaki cigaba da cutar da kanki ba alhali shi yana cen yana sheƙe ayarsa wa ya sani."
“Nasan wannan nisan da nayi da shi shine mafita. Nice silar duk wani hali da yake ciki. Wata kila hakan ne yafi. Amma ba zan iya hana kaina tunaninsa ba.. nayi kewarsa sosai har yasa ina jin zafi. Ina jin ciwo sosai Maryam.”
“Bansan me zan ce miki ba.” Cewar Maryam. “I'm really Sorry.. kinsan wani abu? Ni zan je in ganshi.” Maryam ta faɗa tare da saukowa da sauri daga bisa gadon.
“What? A'a!" Cewar Zahara. “Kar kiyi hakan."
“Saboda me? Kawai ina son gane dalilin da yasa yake miki...”
“A'a..a'a..a'a.." Zahara ta katse ta. “Bana son sanin komai.. please kar ki aikata hakan.”
“Toh ni dai ina son sanin meke faruwa kuma yanzu zan je. Ai nasan gidan nashi.”
Maryam ɗaukar gyalenta da takalminta tayi da sauri ta fice daga ɗakin kawar tata. Tashi Zahara tayi domin taro Maryam da tuni ta daɗe da fita daga gidan.
TO BE CONTINUED...
Readers na daina jin ra'ayoyinku gameda wannan labari. Ya kamata ku fito domin labari ya fara nisa nasan duk kuna nan kun yi likimo. 😇
[03/03 à 05:18] ASHTAR: AMRIYA
(Hatsabibiyar Aljana)
Love 💞 and Horror ☠️ story 📖
By Malik al-Ashtar 🖋
Table of Contents
Chapters
- 1 Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
- 2 CHAPTER 1
- 3 CHAPTER 2
- 4 CHAPTER 3
- 5 CHAPTER 4
- 6 CHAPTER 5
- 7 CHAPTER 6
- 8 CHAPTER 7
- 9 CHAPTER 8
- 10 CHAPTER 9
- 11 CHAPTER 10
- 12 CHAPTER 11
- 13 CHAPTER 12
- 14 CHAPTER 13
- 15 CHAPTER 14
- 16 CHAPTER 16
- 17 CHAPTER 15
- 18 CHAPTER 17
- 19 CHAPTER 18
- 20 CHAPTER 19
- 21 CHAPTER 20
- 22 CHAPTER 21
- 23 CHAPTER 22
- 24 CHAPTER 24
- 25 CHAPTER 23
- 26 CHAPTER 25
- 27 CHAPTER 26
- 28 CHAPTER 27
- 29 CHAPTER 28
- 30 CHAPTER 29
- 31 CHAPTER 30
- 32 CHAPTER 31
- 33 CHAPTER 32
- 34 CHAPTER 33
- 35 CHAPTER 34
- 36 CHAPTER 35