Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 4

CHAPTER 3

Amriya Hatsabibiyar Aljana Book 1 Complete Hausa Novel 2,675 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book


*HOME OF QUALITIE'S WRITER'S ASSO📚*
_(The Home Of Qualitative Writers That Are Educate Humanities)._
https://www.facebook.com/100495222137315/posts/100496042137233/?substory_index=1&sfnsn=mo

*[📝I.W.A📝]*

AMRIYA HATSABIBIYAR ALJANA
Complete Hausa Novel
A WANI KAUYE MAI SUNA NA'IYA

Duka mutanen kauyen sun taru a bakin wata babbar bishiyar kuka. Yara da manya kowanne ya halarta kamar yanda aka bukata. Da ka kalli fuskokin su zaka san a tsorace suke, hatta da yara ma da ba fahimtar meke faruwa ba sosai suke. Addu'a mutanen kauyen suke ta yi ganin wannan tashin hankalin yazo karshe.

Wani tsoho da suke kira da MALAM SHEHU ne ya mike yana kokarin maido hankalin mutanen kauyen kansa.

“Ku saurare ni da kyau,bayan watanni da na kwashe ina bincike, daga karshe na gano inda Amriya take.” Cewar Malam Shehu cikin daga murya yanda kowa zai jishi.

Wannan maganar kuwa da yayi, ta kara ninka tsoron da mutanen kauyen ke ji. Tsoro hade da yar nutsuwa ce ta ziyarci kowannen su. Ko ba komai yanzu suna da sa ran za'a kama Amriya kuma wadanda suka bata ta sanadiyyar ta su dawo.

Wata sanda da shi kadai yake iya daukan ta tsabar nauyi, Malam Shehu ya buga a kasa. Daga sandar nan da yake iya yi, yana da nasaba da karfin tsafin dake gare shi. Karar wannan sanda yasa kowa na kauyen ya nutsu baka jin ko motsin kuda. Malam Shehu ya cigaba da cewa :

“Wannan hatsabibiyar aljanar ta zalunci kowanne daga cikin ku. Kowa a kauyen nan babba da yaro yasan irin abinda ta aikata. Ni, Malam Shehu nayi alkawarin ba zan barta ta sha ba cikin sauki.”

Nan fa wani surutun ya sake barkewa a wajen, wasu na murnar abinda Malam Shehu zai yiwa Amriya, wasu kuwa na ganin ba karamar kasada ta rasa rayuwa bace ja da wannan aljanar. Domin da yawa daga cikin su sun san wacece Amriya da abinda take iya yi. Ta wargaza rayuwar da yawa daga cikin yan kauyen nan na Na'iya : Kashe-kashe, sace masu dukiyoyi da albarkatun gona, da fitowa mutane dan ta haukata su ga duk wanda tsautsayi ya kaishi ya fito karfe taran dare.

“Kun tabbata zaku iya wannan sadaukarwar saboda wannan kauyen? Amriya batada digon tausayi ko kadan. Ba zata yi sanya ba wajen kashe mu baki daya. Kun fi kowa sanin wacece ita.” Cewar wani tsoho daga cikin mutanen kauyen. Sai da Malam Shehu yaja dogon gemun sa kafin yace :

“Wata kila Amriya tana da karfi sosai, amma ku sani ba ni kadai bane a wannan yakin. Zan je birni kuma zan dawo da ita nan. Ku yarda dani.”

Malam Shehu baya jin tsoron Amriya, domin yasan yanada aljanu wanda zasu taya shi yakar ta. Sa'ar dake gare shi ita ce, Amriya ba wai mutane kadai ta zalunta ba. Tana da makiya da dama anan, haka ma a duniyar su. Da yawan aljanu burin su ganin mutuwarta. Malam Shehu shine wanda suke tunnin zai kawo karshen wannan hatsabibiyar anan duniya.

“Ka nemota Malam, tunda ta tafi 'yata ta haukace baki daya. Kowa a kauyen nan tsoron 'yata yake yanzu, alhali a da tafi kowacce yarinya kyau da farin jini a kauyen nan. Naje wajen duk malammai da bokayen makotan kauyen mu amma abu daya suke fada min, Amriya ce kawai zata iya warkar da ita. Dan Allah Malam Shehu ka taimaka mini.”

Cewar Wata mata da kowa a kauyen yasanta saboda haukan 'yarta. Durkushe take gaban Malam Shehu tana rokon shi da iya karfinta da ya taimake ta. Kowa a wajen yaji tausayin ta.

“Ni, 'yata ta 6ace kimanin watanni uku. Hauka ta fara kafin daga baya ta gudu cikin daji. Tun daga wannan ranar babu wanda ya kara jin labarin ta, kuma mutane suke tsoron zuwa wannan dajin.”

Wata matar ce tazo bayan ta farkon, tana bada labarin kowa sai girgiza kai yake dan tausayawa. Kowa yasan yanda 'yarta da ta bace take da nutsuwa ga hankali. Kyakyawa ce sosai yarinyar ga kuma manema aure da dama. Har ma ana shirye-shiryen auren ta. Sai dai aka wayi gari aka ganta ta canza, tana biyar maza, daga baya kuma ta koma tana kwana ita kadai waje, alhali lokacin kowa na cikin gida gudun haduwa da Amriya. Daga nan yarinyar ta fara hauka, tana duka da jifan duk wanda yabi ta inda take, har wata rana aka wayi gari ta shiga daji. Bata kara dawowa ba.

“Dan Allah Malam ka taimaka min.” Matar ta fada kafin ta koma wajenta. Wata matar ce ta sake zuwa, da ganin ta kowa a wajen jikin shi yayi sanyi. Domin ba zasu manta da 'yarta ba da kuma abinda ya same ta. Ba wanda cikin su ya iya manta kukan da matar tayi a daren da ta rasa yarta.

Kamar sauran yan matan na baya, ita ma wannan yarinya ce kyakyawa ga nutsuwa, da ilimin addini. Duka danginta suna alfahari da ita domin ta hardace kur'ani baki daya. Kullum a cikin dogon hijab take, kuma bata fita daga gida idan ba da dalili ba. Bata wuce shekaru ashirin, har karatun yamma take koyawa yara a masallacin kauyen. Sai dai wata rana da yamma, ta dawo daga masallaci zuwa karfe bakwai bayan sallar Maghreb, ta fadi daidai kofar gidan mai gari. Wasu matasa ne sun dawo daga kamun kifi suka tarar da ita sumamma. Lokacin da ta dawo hayyacin ta, bata gani ta makance. Labari dandanan ya watsu kamar wutar jeji a kauyen, sai dai mutane da jin hakan suka san aikin Amriya ne. Mahaifiyarta tayi kuka har ta godewa Allah, amma kuma tayi farin ciki da kasancewar yarta kusa da ita. Yarinyar nan bata yi kasa a gwiwa ba, ta cigaba da zuwa tana koyar da alkur'ani. Ta kan ce wata kila ba zata sake gani ba da idanunta, amma tana gani da zuciyarta kuma iliminta a cikin kwalwarta yake. Dan haka ba zata daina koyar da karatun alkur'ani ba, har karshen rayuwar ta. Haka kuwa aka yi, wata ranar juma'a da dare bayan sallar isha, tafiyarta take a nutse. Ta hardace hanyar zuwanta gida a zuciya. Kowa na ta sauri yaje gida gudun aljana Amriya, amma ita bata da wannan tsoron domin Allah yana tare da ita kamar yanda take cewa. Tana cikin tafiya ta kawo wata mararrabar hanya, nan taji wani yaro na ta rusa kuka.

Matsawa tayi kusa da yaron, tare da durkusawa dan yi masa magana. Ba zata iya barin shi shi kadai ba anan.

“Yaro, me yasa kake kuka? Ina maman ka? Ya kamata kaje gida kaji.” Ta fada tana shafa fuskar yaron domin lallashin sa.

“Tsoro nake ji ba zan iya zuwa gida ba ni kadai.” Cewar yaron yana mai rage sautin kukan sa.

“Ba damuwa bari nayi maka rakiya, ai kasan gidan naku ko?” Ta tambaye shi.

“Eh na sani amma ina jin tsoro...”

“Ka daina jin tsoro, Allah yana tare da mu. Ka iya karanta ayatul kursiyyu?” Cewar matashiyar budurwar tana mai mikawa yaron hannunta domin yi mata jagora zuwa gidan su.

“A'a menene haka nan?”

“Ita kariya ce. Idan kana karanta ta, ba zaka kara jin tsoro ba, domin Allah zai kare ka. Bari na koya maka. Ka maimaita duk abinda na fada...”

A haka suka cigaba da tafiya.

Cikin rashin sa'a, wannan ranar, yarinyar nan bata dawo gida ba. Mahaifiyarta tayi jiran ta tsawon daren nan babu labarin ta. Washe gari zuwa karfe ukun dare, wani ya konkwasawa mahaifiyar yarinyar dake tsaka da yin Sallah kofa. Katse sallar tayi da saurin ta taje ta bude da tunanin ko 'yarta ce. 'Yar tata ce, amma a kwance a kasa, anyi mata yankan rago. Babu hijab a jikin ta, fuskar ta tasha kwalliya alhali ita bata taba yin kwalliya ba, da wata karamar riga a jikin ta da duk ta bayyana surar jikin ta. Da ganin wannan mahaifiyar tata ta fasa kara tare da somewa. Wajen yiwa yarinyar wanka kuwa, mata yan binciken kwakwaf sun tabbatar da ba budurwa ba ce, alhali cikin kauyen babu wacce keda kyakyawar sheda mai guarantee kamar ta.

Matar yana kuka take bawa Malam Shehu labarin ta. Kusan rabin mutanen dake wajen sai da suka zubar da hawaye da jin labarin. Mutane da dama sun so zuwa su fadawa Malam Shehu labarin abinda Amriya tayi musu amma ya dakatar dasu.

“Zan je birni gobe, na kamota domin ta girbi duk wani ta'addanci da tayi.”

“Kaje Malam kuma ka ceci rayuwar wadanda take kokarin cutarwa nan gaba!” Cewar wani tsoho a cikin taron.

Godiya Malam Shehu yayi musu duka, kafin ya tafi gida yana zumudin ganin ya fara yaki da hatsabibiyar Aljana Amriya....

Ku latsa shudin rubutun dake nan kasa don cigaba da karanta littafin ta hanyar downloading nashi akan wayoyinku
👇👇👇👇👇👇😭
https://t.co/MvIrCc0zi6
https://t.co/MvIrCc0zi6

A WANI BANGARE CIKIN BIRNI KUWA

Wannan rana, Zahara ta tashi da jin wani irin sauyi a jikin ta. Ba wai sauyi na jiki ba wanda ake gani, a'a cen cikin ranta tana jin akwai abinda ya sauya. Tana jin yarda da kanta, jin kanta kyakyawa sosai, jin ta a matsayin cikakkiyar mace. Kallon ko'ina na cikin dakin da take kwance ta shiga yi, wato dakin motsa jiki da ta baro nata ta dawo cikin sa, anan take ta rena dakin, ta gani ashe cikin kazanta ma take. alkawari tayi ba zata sake sako kafa cikin sa ba. Tambayar kanta ma take ta yanda aka yi ta iya kwanciya a dakin.

Bata yi wata-wata ba, ta fito daga dakin zuwa dakinta na asali. Ban daki ta shiga tayi ta wanka kamar zata kwaye fatar jikin ta. Bayan ta fito, ta shiga bincike kayan wardrobe dinta, tana mamakin wai ita ke saka wannan kayan. Alkwari tayi idan taje ta amshi salary din ta, zata siyo wasu kayan masu class. Da kyar ta samu wata riga cikin kayan, karama sosai, da ta saka ta fiddo mata kusan rabin kirjin ta waje, sai kuma wani wando jeans da ta dade bata saka ba wanda a da take ganin ba zata iya saka shi ba, ta saka shi ya dan kame ta sosai. Yau tana ji har cikin ranta wannan wandon shi ya kamata ta saka. Bakin madubi ta koma ta karewa kanta kallo tana juye-juye, tana yaba irin matching da wandon yayi da kirar ta. Rigar kuwa da kamar zata yage saboda yanda ta matse ta, tace irin wannan babu namijin da zai sha a hannun ta. Wani abun haushi da ta tuna batada kayan kwalliya ko kadan. Tsinewa kanta tayi ta yi ba adadi, kafin ta dauki jakarta ta fito zuwa wajen aiki. Haka takalmi ma da kyar ta samu na sakawa domin a cewarta babu irin fashion din nan.

Saukowa tayi kasa, ta nufi kitchen wajen Mama.

“Hello my mamashou!!!” Da ihunta ta rungume mama.

Mama kuwa daskarewa tayi a wajen na mamakin 'yar tata da kuma yanayin shigar ta. Tsayar da aikin da take yi tayi tare da juyowa tana karewa Zahara kallo. Ba zai yiwu ba, wannan ba yarta bace. Ita da ta tsani fiddo da surar jikin ta, ta yaya zata sauya farat daya? Tunanin zucin da Mama ke yi kenan.

“Lafiyar ki kuwa Zahara?” Cewar Mama.

“Lafiya sumul nake Mama! Me yasa kika ce haka?”

“Naga kamar kin... Ban sani ba, amma yau kamar ba ke ba.” Mama ta fada cike da tsoron canjin yar tata.

“Ni din dai ce Mama.” Cewar Zahara tana dariya. “Ni ce dai Zahara, kawai yau ina ji na ne fiye da jiya. Jiya na yiwa kaina karatun ta nutsu sosai, kuma na yanke shawarar canza kaina daga sakaryar da ake kallo na! Ba murna ya kamata kiyi ba Mama?”

Mitsina kanta Mama tayi dan ganin ko mafarki take. Sai da ta dauki lokaci kafin ta fahimci meke faruwa. Lallai 'yarta ce ke mata magana, maganar ma mai tsawo kuma ba tare da ta sadda kai kasa ko kuma taji tsoron abinda take fada ba.

“Nidai Mama zan wuce wajen aiki idan ba haka ba zan yi latti. Duk kirkin ubangida na baya kaunar latti.”

Zahara fitowa tayi daga kitchen, ta baro Mama daskare a wajen cikin matukar mamaki.

Zahara kafin ta samu dan sahu, ta jawo kallo da yawa na yan unguwa, musamman maza. Dan ba wai kaya kawai ta canza ba, hatta tafiyar ta ta sauya. Duk da ba wani masifaffen kyau gareta ba, amma da yake duk inda mace zata yi shigar da zata fiddo da kirar ta haka zaka ga Maza na tuntube wajen kallonta, hatta mata ma yan uwanta.

Da tarfic da komai dan Sahu ya aje Zahara daidai bakin kofar kamfanin su cikin mintunan da basu wuce goma sha biyar ba. Gaishe da duk ma'aikacin da ta hadu dashi take. Kowannen su na mamakin sauyawar Zahara. Domin a kullum idan zata gaishe da mutum kanta kasa yake, yau kuwa sun ga abun a tsa-tsaye kuma ga wata shiga da basu taba tunanin ganinta da ita ba.

Yau ya zamana hira daya ake a kamfanin, hirar Zahara Usman sakatariyar Mr. Amar CEO. Mintuna talatin da zuwan Zahara, sai ga ubangidan ta Mr. Amar Yusuf yazo. Yanayin da yake bai sa ya lura da sauyin da sakatariyar sa ta samu ba, dalilin jiya matsalar da ya samu da mahaifiyar shi da ta tayar masa da hankali dan ya fada mata wacce yake son aure.

Gaishe shi Zahara tayi ya amsa ba tare da ya kalle ta ba yace “Please samo min coffee mai karfi.” Kafin ya shige ofishin sa.

“Toh shi kuma wannan meye matsalar shi?” Cewar Zahara tare da mikewa zuwa hado coffe.

Tana dawowa, konkwasa kofar tayi sau biyu kafin ta murda ta shiga. Tarar dashi tayi hankalin sa ga computer.

“Ga coffee din.” Ta fada tana ajewa saman table. Mr. CEO daukan coffee din yayi ya kai baki, yana kurbawa ya wani dame fuska tare da kiran Zahara dake kokarin fita.

“Wannan coffee ne? Me yasa baki sa suga ba? Kina son ki kashe ni ne ko me?” Ya fada har yanzu hankalin shi na kan computer.

“Sorry sir, amma ban taba jin coffee marar suga ya kashe mutum ba. Cewa fah kayi na hado maka coffee mai karfi.” Zahara ta fada da kusan kakkausar murya.

Dago kansa yayi cikin mamakin yanda Zahara tayi masa magana yace :

“Zahara da ni kike magana?” Ya fada da mamaki.

“Baka taba min magana da wannan sigar ba, shi yasa nima na baka amsa a hakan.” Zahara ta bashi amsa.

Amar tambayar kansa yake idan da gaske Zahara ce. Kallon Zahara yayi yaga irin shigar da tayi. Sauka idanunsa suka yi kan kirjin ta. Wata zuciyar ce ta gargade sa, Zahara kamar kanwa ce gareshi, da sauri ya sauke idanun sa.

“Toh yaya, na dauke coffee ne?”

“E..e..eh tafi dashi.” Ya fada murya na masa rawa.

“Ok, bari na hado maka wani.” Zahara ta fada kafin ta juya ta fita.

Kokawa Amar yake da tunanin sa marar kyau, da yake ingiza shi na son kallon mazaunan Zahara, amma ya kasa yin hakan. Dan daga idanun sa yayi da niyyar kallon ta, sai dai aka yi katari Zahara ta juyo suka hada ido. Signa tayi masa da ido kafin ta rufe kofar. Amar da sauri ya mike tare da bude maduban window, dan duk ac dake wurin amma zufa yake.

Meke faruwa kenan da Zahara? Tambayar da yake yiwa kansa Allah yasa ba wai maganar da suka yi bace, ta juyar mata da tunani ko kuwa da gangan ne take yi? Ba wanda za'a ce ya sauya farat daya idan ba munafuki ba ko mayaudari. Tsoro yake kar ya kasa rike kansa idan yarinyar nan tana a waje. Dan haka yafi kaunar Zahara ta da sau dubu akan wannan.

Tunani yake, ya kirkirar wa kansa abinda ba zai iya controlling ba. Sai dai ko da gaske shi ne silar wannan sauyi nata?

------------------------------------

Toh yaya fatan wannan chapter ta kayatar da ku? Idan haka ne ku nuna min a comment hakan zai kara min karfin gwiwa. Nagode 💓

AMRIYA
(Hatsabibiyar Aljana)

Love 💞 and Horror ☠️ story 📖

By Malik al-Ashtar 🖋

On wattpad : https://www.wattpad.com/story/270492485

Table of Contents

Chapters

36 chapters
  1. 1 Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
  2. 2 CHAPTER 1
  3. 3 CHAPTER 2
  4. 4 CHAPTER 3
  5. 5 CHAPTER 4
  6. 6 CHAPTER 5
  7. 7 CHAPTER 6
  8. 8 CHAPTER 7
  9. 9 CHAPTER 8
  10. 10 CHAPTER 9
  11. 11 CHAPTER 10
  12. 12 CHAPTER 11
  13. 13 CHAPTER 12
  14. 14 CHAPTER 13
  15. 15 CHAPTER 14
  16. 16 CHAPTER 16
  17. 17 CHAPTER 15
  18. 18 CHAPTER 17
  19. 19 CHAPTER 18
  20. 20 CHAPTER 19
  21. 21 CHAPTER 20
  22. 22 CHAPTER 21
  23. 23 CHAPTER 22
  24. 24 CHAPTER 24
  25. 25 CHAPTER 23
  26. 26 CHAPTER 25
  27. 27 CHAPTER 26
  28. 28 CHAPTER 27
  29. 29 CHAPTER 28
  30. 30 CHAPTER 29
  31. 31 CHAPTER 30
  32. 32 CHAPTER 31
  33. 33 CHAPTER 32
  34. 34 CHAPTER 33
  35. 35 CHAPTER 34
  36. 36 CHAPTER 35
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});