Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 25

Chapter 25

Karshen Duniya Book 1 Complete Hausa Novel 1,206 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

zauna tunanin mafita Na Dade a gun ina tunanin mafita Ga dai ciki a jikina' Wanda bansan makomar mu nida shi ba" Gani garin da bansan kowa' Tom ina nan zaune Ina saka da warwara' nayi nisa a tunani wasu matasa suka zo suka Yasheni tass' Ban farga ba sai da na fara Jin yunwa na nemi jaka jaka tacee daukar ni inda Kika ajje' Lallai rayuwa duniya juyi juyi' Ban wahalar da kaina ba' wajen neman su na tashi naci gaba da tafia" Hukunci daya da zuciya ta ta yanke min shine inshiga karuwanci' Bani da sauran gata a duniya me nake dashi da yayi saura? Wa na sani? Wa zan tunkara? Amma ina da duk wani abinda d'a namiji yake buqata Wallahi a zuciya ta babu danasani' daukar fansa shine kawaii burina Zan bata sunan zuriyar tasu zan wulaqanta su wulakanci Mai muni Wani Dan acaba na tare nace mishi yakaini inda karuwai ke taruwa ko kuma yakaini babban gidan karuwan garin ya kalleni ya qara kamar zaiyi magana sai kuma yace hau muje Kai tsaye maraban jos ya kaini' Wlh a ranar na tabbatar da cewa mata sun halaka ga maza magidan ta' suma duk sun baro matan su na sunna sunzo sun tare wajen qadangarun bariki' Abun dai babu kyawun gani Zoben hannu na gold na nabawa mai acaban ya karbe da gudu yana murna ban saurari wasu Kudi da yake Miko min ba nayi gaba Kai tsaye cikin gidan karuwan na nufa Anan nakuma ganin wqni bala'in Dan abin wlh ya qazanta" kamar zuciya na ta karaya infasa har nayi baya zan fice' naji an damqi hannu na' Da sauri na waiga Dan ganin waye? Wata matashiyar mace nai cin karo da ita tana min. Murmushi" Ban Musa mata ba na bita jana tayi har dakin ta Dakiñ plain ne Amma atsare yake daga katifa sai akwatu na sai dan qaramin fridge' Sai shoe rack" Sai d'an qaramin cylinder mai Kai Wanda da alamu dashi take girki' Jana tayi har ciki ta zaunar Dani tace min Ina zuwa' Ruwa ta kawo min mai sanyi da abinci Ba jira na hau ci Tai zaune tana kallo na duk yawan abincin Nan sai da na tadashi tass Na fita na wanke hannu na na dawo' Murmushi na Mata nace nagode itama murmushin ta min tace kar ki damu" "Nace zan tafi Tace "Ina ?" Nace "inda Allah yaso A da nashigo gidan Nan ne da niyyar in zama daya daga cikin members na gidan Nan' Amma da naga yanayin abin ya qazanta naji bazan iyaba Gwara inje ko da aikatau ne inyi in rufa wa kaina asiri" Murmushi tamin tace "ko?" Na gyada Mata kai' Tace "da alama kediin Yar Hutu ce nasan kin fada ne Amma bazaki iya aikatau ba Kuma ko da aikatau din Zaki da cikin Zaki?" Da kallon mamaki na bita ya akai tasan inada ciki' No dear kada ki mamaki mace Mai ciki Bata boyuwa Musamman a gun mu y'an bariki' Kallo daya na Miki nasan ciki ne dake Kuma da alama shine sanadiyyar fitowar ki daga' gida' Wani fitinannen kuka na saki Mai cin rai.da zuciya Bata hanani ba har nayi Mai isata' Sannan na Bata labarina da yanda akai nazo gidan Idanun ta sunyi jazur Bata daiyi kuka ba tace Amma wannan anyi watsattsen tsoho' Sorry fa Amma wlh wannan tsohon yayi asara Amma fa ba ke ya cuta ba kanshi yayiwa domin akwai ramuwar gayya wacce tafi ta gayya zafi'" ire iren ku nake Nema wadanda suka rasa gata Basu da madafa inshiga rayuwar su in tallafesu in Kuma tayasu daukar fansa Ta kalleni tace "Ina fata Zaki bani had'in Kai Cikin jikin ki bazamu zubar dashi ba.domin shi zai zama makamin mu" Da sauri na kalle ta nace "Taya?" Tace "kin amince Zaki zauna Dani? Kin amince Zaki yakin kwato wa sauran Mata yanci?" tana ta huci Gyada Mata kai' nayi tace "to dole zaki shiga karuwan ci Dole.zamuyi hijra daga garin kaduna mukoma kanon Ta hakane zamu cimma burin mu idan kin amince Ki Dora hannun ki akan nawa" Ai da sauri ma Dora hannu na akan nata *"to fa ga zeenah ga Kuma mero currency Mai idon cin nera ko ya zata kaya? saura page biyu free page ya kare karki bari ayi bake kawata littafin nan shakundum ne a Tafiyar ba ai komai ba Kunji alwashin currency ga zeenah ta amince da had'a hannu domin kwato wa sauran mata y'anci ta yaya? Hmm fresh package dinmu na daban ne buk 2yafi buk 1 har mutsi karki yarda a fara karatun nan dake ki saki damarki taci gaba da karanta wannan labari kowanne tsari kike bukata Akwai shi 300,500,600 duk Dan jindadin ku* _muje zuwa'_ Comment Share 08038541511 [1/31, 6:57 PM] Zahrahbukar: *KARSHEN DUNIYA* _kalubalenku Iyaye_ *na* *Zahrabukar* *exquisite WRITTERS forum* Normal group #300 VIP #500 special #600 _duk tsarin da kike bukatarku zaki samu Akwai banbanci yawan posting a kowacce rana akan kowanne tsari_ ki biya yan sulallan ki ta wannan account number din *6035968908 keystone bank umma yusif* Sai ki Turomin shaidar biya akan wannan number din 08038541511, Sai insaki paid group *29* *second to d last free page* Wani ta Kira a waya tasanar dashi tana Nan tafe Kano gobe amma ba a hotel zata sauka ba gida takeso ya Kama mata Dan danan kuwa acikin abinda baifi' awa uku ba akace Mata ansamu gida a unguwar na'ibawa Kayan ta tashiga yin parking tace "bariki babu Amana kada asamu wani yazo ya yasheni" Nidai Ina zaune zuru Ina ta kallon ta kamar Mai jira dama? Ta dauki.abin da zafi ainun' Kuma da alamun zata zamemin tsani da zai kaini ga cimma burina' na ganin Kaka malan ya wulaqanta' A dakin ta muka kwana Dan duk baqon da yakawo mata ziyara cewa take tana da bakuwa daga garin su Tazo sanar mata anyi Rashi so gobe asubanci zasuyi, Haka muka raba dare muna tsara yanda zamu gudanar da komai ban wahalar da Sharia ba duk abinda nasani game da kaka malam sai da nasanar da ita Asubancin kuwa muka Yi Dan tun kafin asubar ma Wanda zai kaimu ya iso Komai dama mun kimtsa so babu b'ata lokaci muka fito Hanyar Kano muka dauka cikin ikon Allah mukaje lapiya har gidan da aka kama mana. Ta sallami Wanda yakawo mu Ta kira aka kawo mana makullan gidan Ba wani katon gida ba ne d'an madaidaicine mai wadatar tsakar gida ZAMAN wucin gadi zamuyi acikin shi Babban Fallon muka nufa dakuna uku ne aciki sai kitchen da d'an madaidaicin toilet aciki kowacce ta zab'I inda zata zauna Wanka mukayi mukayi sallah sannan takira wanda yaka ma mana gidan tace mishi akawo Mana abinci Haka kuwa akai yabayar aka kawo muka zauna mukaci muka koshi Nakawar da kayan sannan nazo na zauna Nace "taya kike ganin zamu Fara! ? Domin na qosa wallahi am eager" Murmushi tamin tace "karki damu a yau din Nan basai gobe ba za a sato minshi" Na zaro ido waje nace "a sato shifa" gyada Kai tayi ta ce "wannan shine mataki na farko sai na fara gama gana mishi narkon azaba sannan zan bayyana mishi ke Kuma a gidan nan

Table of Contents

Chapters

27 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});