Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 18

Chapter 18

Karshen Duniya Book 1 Complete Hausa Novel 1,198 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

kar ya gushe ki dawo hayyacin ki Yar ki ce kada ki mata mugun baki Kuma kin san illar hakan" ****************** Batare da ta tankawa aunty amarya ba tafice tanufi dakin ta da gudu Ta wuce umaymar dake zaune falo tana jijjiga jiki ********************** Idanun ta sunyi jazur sanda suka isa gidan dan ba qarya fa tana cikin tashin hankali Ba qaramin buri ta daura akan tahseenah Ba Allah kad"ai yasan burin da taci akan Yanmatancin tahseenah har zuwa auren ta Amma yanzun wani qaton banza ya rushe mata budget Kuma yaci bulus Zata aurar da budurwa matsayin bazawara Haka dai ta surutai azeema na kallon ta wankan ma bata samu tayi ba abincin kawaii ta girka mai sauki ta dauki abinda tasan zasu buqata a asibityn ta rufe gidan dama bata shigo da motar ciki ba a waje ta barta Da wani irin gudu take tafia da ta tuna yanda ta hangi tahseenah a kwance kamar gawa sai taji kamar kafin sukai za a kirata ace mata ta mutu haka dama iyayen da akayiwa Yaransu *fyade* sukeji? Lallai Ashe Akwai masu kakkarfar zuciya acikin mutane Tabdin Wallahi da ace Yanzun zatai ido hudu da shegen da ya farke Mata y'a wlh itace ajalin shi _nace anya kuwa?πŸ€”_ ********************* Cikin kwana biyu soyayya ta yi nisa tsakanin basheer da humayda ruwan love kawai suke zubarwa Basheer d"an katsina ne karatu yakaishi adamawa tun yana d'an shekara tara aka kaishi almajiran ci cikin ikon Allah da fadi tashin rayuwa a makarantar ba a bara za a kai yaro da abincin shi har na shekara to idan yaro yakai shekara Sha biyar to alokacin za a yayeshi daga kawo abunci sai ya tafi ya fara kananun Sana'o'i Dan ya ruke kanshi a haka shima yai tashi rayuwar har Allah yasa ya mallaki hankalin shi lokaci zuwa lokaci yana ziyar tar iyayen shi dake katsina yaje musu da abin alheri daga cikin irin fad'i tashin da yake na neman na Kai A hankali har yasiyi fili a katsinar Yana ginawa a hankali iyayen na taimaka mishi A haka suka had'u da humayda da sunyi soyayya mai tsafta ita Yar adamawa ce inda karatun ta da kaf din rayuwar ta anan ta yita bata da yawan qawaye qawarta daya *fannah* tun kuruciya a tare suka tashi qawancen su na muddin Rai kowa baya boyewa kowa damuwa ko farinciki son Gaskia ne a tsakanin su babu hassada kyashi bare bakin ciki ba tare da bata lokaci ba iyaye suka shiga maganar Duk wani shiri na hidimar bikin *fannah* ce a gaba haka dai akai biki lpy aka watse akayo da amarya garin katsina _ta dikko dakin kara kunya garemu ba dai tsoro ba_ Amarya ta tare a gidan ta suna rayuwar su cikin aminci da kyautatawa juna ******************* Durkushe take bakin kofar dakinta ruwa ne Ake tsugagawa kamar da bakin kwarya Amma dakin a Rufe yake duk bayan lokaci sai tasa hannu ta bubbuga Dafatan Wanda Ke ciki ya bude mata duk ruwan nan batai yunkurin kare kanta daga zubar ruwan ba tadai lullube goyonta Sai jijjiga yarinyar dake ta tsala ihu take ga wani irin sanyi tayi kuka tayi kuka tayi rokon da magiyar Amma duk a banza Wata irin tsawa da akai yasa yarinyar bayanta ta daddage ta kwallah wani irin ihu ta firgice a gigice take Haka ta dage da Dan sauran karfin da yaragen mata ta cigaba da dukan kofar a fusace nacikin dakin ya bude dakin Wata sassanyar ajiyar zuciya ta sauke Tana niyyar kutsa Kai cikin dakin ya fizgo ta ya dage ya fallah mata Mari bata damu ba tai kasa da kafafunta zata Fara rokonshi yayi kwallo da ita tsakar gidan bai dsmu da ruwan da yafara jikashi ba ko kukan da yarinyar ta tsala jin ta gwaru da kasa ya zaro belt din wandon shi yaci Gaba da dukanta yadake ta yahado da yar idanunshi sun Rufe zuciyarshi ta dugunzuma dukanta kawai yake tun Tana Jan Jiki Tana girgiza Kai Har tai lakwas kukan yarinyar ma ya dauke diff sannan ya saurara ya buga tsaki yabar su nan sheme cikin ruwan Babu Mai kwakkwaran motsi πŸ‘πŸΌπŸ‘πŸΌπŸ‘πŸΌπŸ‘πŸΌπŸ‘πŸΌπŸ‘πŸΌ comment share 08038541511 [1/24, 9:25 AM] Zahrahbukar: *KARSHEN DUNIYA* _kalubalenku Iyaye_ *na* *Zahrabukar* *exquisite WRITTERS forum* *masu himma tuni sun fara subscription kui maza ku hanzarta fa kar ayi baku Tafiyar Mai tsawo ce Akwai rikita rikita da bankade bankade cin amana daukar fansa Mai zafi yaudara zamba cikin aminci kawata matso kusa da yan kudinki kalilan ki kwashi garabasar wannan daddad'an labarin* Normal group #300 VIP #500 special #600 _duk tsarin da kike bukatarku zaki samu Akwai banbanci yawan posting a kowacce rana akan kowanne tsari_ ki biya yan sulallan ki ta wannan account number din *6035968908 keystone bank umma yusif* Sai ki Turomin shaidar biya akan wannan number din 08038541511. Sai insaki paid group *22* Rayuwar su gwanin Shaawa cike da girmama juna suke yinta tana bin surukar ta tana kuma kyauta ta mata a haka dai cikin rufin asirin Allah suke rayuwa Dan ba mai kudi bane talaka ne mai neman abinda za"aci a kullum Shi ke taimakawa iyayenshi Dan mahaifin shi wahala da talauci sun sa yayi tsufan wuri Mahaifiyar shi ita kuma tana y'ar Sana'ar soya waina Hayaki da wahala har ya Fara kashe mata ido abinda ke cinye musu d'an tanadin sun kenan lalurar idon ta Watan su shida da aure ya siya mata wata waya Nokia mai torch light Dan dama bata da waya tayi murna kwarai tana d'an sa ear phone tanajin radi" haka dai suke gurgura rayuwar, Yau da gobe kayan Allah har sukai shekaru biyu ba ciki ba alamun shi tun basa damuwar har dangi suka fara yada mata magana to shima can gida baba ta fara tsogwomi baban ne ma kedan taka mata burki ******************** Kwanan su uku a asibityn aka basu sallama tare da shawarwari na yanda za'a kula da ita har ta karasa warkewa Duk wannan kwanakin a kaf dangin su babu wanda suka sanarwa Ga iftila'in da ya afka wa tahseenah Suka ja bakinsu suka tsuke Haka suka koma gida rayuwar duk ta juye wa tahseenah duk ta zama wata marar lakka da rashin son magana sai dai ta zura wa waje d'aya ido tana kallo, Abba kuwa har Yanzun yakasa mance zumar da ya d'andano kullum sai ya so Kuma jaraba shiga dakin sai kuma yaji tsoron kada asirin shi ya tonu Ga qungiyar su ta sako shi gaba akan cewa indai bazai iya ba ya fad'a sai a canja tahseenar da azeema a ranar baiyi bacci ba shi shikenan duk shi zai lalata yaran shi gaskia bazai iya haikewa azeema ba yarinya yar shekaru hudu me zaiji a jikin ta' Zai dai San abinyi akan ita tahseenahr ******************* Zaman shirun ne ya ishe ta yau gashi ba zuwa makaranta ake ba ana cikin Hutu yau taji tana son share dakin Tai kwalema ta canja wa komai tsari Haka ta tarki aikin umma nata Jin dadin ta fara sakin jikinta dama kullum korafin su kenan tasha aiki sosai tana Sharo kasan gadon ne ta Sharo wani had'adden zobe dauke shi tayi zata ajje ta kalli zoben ta qara kallo wannan in ba idon ta bane ke

Table of Contents

Chapters

27 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});