Chapter 10
Chapter 10
sai naga bayanshi" Ta fashe da wani irin kuka Mai cin Rai taci gaba da cewa "duk da qarancin shekaruna na ji zafin abinda yamun Wanda uwata mahaifiya ta itace silar komi tare da taimakon mahaifina Ina fatan zaku kau da Kai ga duk abunda zakuga Yana faruwa Domin wlh tallahi sai na dasa wa Irfan baqinciki a rayuwa duk da bansan a Ina yake ba amma tabbas zan nemeshi zan nemeshi ko a Ina yake a fadin duniyar Nan"......... Comment Share #repost 08038541511 [1/13, 11:46 AM] Zahrahbukar: *KARSHEN DUNIYA* _Kalubalenku iyaye_ *NA* *Zahrabuhkar* *Exquisite Writers FORUM* *13* A firgice suke kallonta Anya kuwa wannan ilham ce? Ilham dai tasu yarinya yar shekaru Tara itace ke furta wadan Nan maganganu? Innalillahy wa Inna ilayhirraji un tabbas sunga illar sakaci Momy ce tai qarfin Hali zuciyarta tai duhu wani irin tukukin maseefa Ke Taso mata cike da bana'i Kai tsaye tace "Sageer" Kaga rayuwa ko? Kaga yanda Al"amura suka juye Mana lokaci daya ko ? Dan ka ya tarwatsa mun yarinya sannan ya jefe man ita da baqin asiri wallahi wannan ba y"ata ilham bace ilham batai girman da xata iya furta wadannan kalmomin ba bayan abinda ya mata sai Kuma ya haukata mun ita? wallahi bazai yuwu ba naga sakamakon soyayya naso shi domin Allah da zuciya d"aya Ashe burin shi ni ya kassara min rayuwa'? " Tashi tai ta dawo inda ilham din take ta dafata tace "wannan ba yaqinki bane Ke kadaice wannan yaqine da zamuyi shi da dukkan karfin mu da kudin mu da jikinmu da muggan takubba wallahi tallahi na Miki alqawarin muddin ina raye a duniyar Nan wlh tallahi sai na kawo Miki Irfan a wulaqance sai kin taka gawar shi bayan na mishi hukunci Mai tsanani tabbas wannan alwashi ne" Juyowa tayi ta kalli daddyn tace"Ina fatan zaka kauda ganin ka ka kiyaye jinka da duk abinda zaka ga Yana faruwa domin wlh bazan yi kawaici ba " Wani mugun kallo ya wurga mata yace "tabbas yanzun na tabbatar da cewa qwaqwalwar mata gajeren tunani take kin manta? Kin manta in tuna Miki? Ke a yanzun laifin Irfan kike gani? Kin manta abubuwan da Kika dinga yiwa mahaifiyar shi har tabar duniya? Na zuba Miki idone domin yaran mu Amma wallahi a wannan yqkin babu hannu na aciki kibarni in tunkari bala"in da ke tunkaroni na Tabbata wannan tarihi ne ya maimaita kanshi"shima ya karashe cike da numfarfashin maseefa Tabarmar kunya ta fara nadewa da hauka tana wasu maganganu shaf su duka sun manta cewa akwai ilham a gurin' "Au haka zakace ? Me na mata Banda taimakon da na mata ? Oh to me kqkeson cewa? Ka tona min asiri wlh kayi kad"an daga Kai harshi sai in wulaqanta ku Kuma in zauna lapiya abinda ya faru inace ba Wanda yasani daga ni sai Kai sai abbana to ta ya ya Irfan yasan wayeshi? Ohh to kenan Kai ka zaunar dashi kq fada mishi shine kuka hadu kuka yanke shawarar yi ma y'ata *fyade* to anyi walqiya ta haska na Kuma ganku Amma wlh ku jira yi waiwaye n.. saukar wasu tagwayen maruka da taji yasa sauran maganar maqale wa"yace kee Fatima ki farka in mafarki ma kike to ki farka bazan dauki wanann iskan cin ba Amma idan kikai wasa Irfan baisan Waye shi ba Amma wlh a wannan taqin tsaf zan bayyana wa duniya Waye Irfan mecece alaqata dashi wacce ke kanki ba kisani ba ba ke ba duk wani ahalin ki sai ya jijjiga so Ina so ki tanaji ma"ajin tashin hankali zuwa lokacin da gaskia zata bayyana Dan tana gaff" Ya Kuma watsa mata wani kallon ya bangajeta ya fice" Wata juya CE ke neman kadata tai sauri ta dafe bango" Wasu sabbin maganganu taji sageer na fad"a me yake nufi ? _nace bishi ki tambayeshi Kya tambaye ni Nima insha maruka_? 🤔🤔🤔 _kar kuce komai ku adana tambayo yinku_ """ Suman ta uku tana komawa da ansa mata ruwa ta dawo sai Kuma ta koma a na qarshen ne dai akasamu ba ta koma ba Kukan ma ya kasa fita ta rasa a wanne muhalli zata ajje wannan baqin labarin y"ar ta kwaya daya jall yau ta zama gawa.? Kenan ganin bankwana ta mata lokacin da ta ganta kwance cikin jini? Wace iriyar sakayya Saleh ya mata haka ? Shikenan ta rasa kwan da ta wahala kafin ta gani? Innalillahy wa Inna ilayhirraji un hasbunallahu wani imal wakeel tabbas kuka ma rahama meyasa baban humayda zai mata wannan hukuncin? Y"ar ta ta mutu ba a Gaya mata ba sannan har akai Jana izar ta Bata da labari me kenan? _nace tambayi kanki_ Suna Nan zaune suna Bata Baki sukaji sallama Basheer ne baban mubeena fuskar Nan a tamke idanun shi sunyi jazur ganin surukanshi yasa ya duqa suka Kuma gaisawa suka Kuma Mai gaisuwa kafin suce to mu bari muje Allah ya qara hakuri ita Kuma Allah ya jikanta yasa masu ceto ne" amsawa yake Sama Sama hankalin shi na wurin humayda da ta zura mishi ido ganin zasu fita ne yasa yace mata "Zaman me kike? Me kike jirah? Ki tashi ki bisu Ina fatan dai Baki manta alqawarin da na Miki ba to Allah ya kawo lokaci Babu ma mubeenar a duniyar Kinga ba sauran wani bango a tsakanin mu Ina fata Zaki mance Dani a tarihin rayuwarki ki Kuma manta dacewa kin taba haihuwa Wawiya jakar uwa sakarya wlh Baki cancanci zama uwa ba ina tausaya wa Wanda zai Kuma kwasarki yakai gidan shi da sunan matar aure sannan a KARSHEN watannan Ina Miki albishir da cewa zakiji zancen aure na da *FAnnah*" Bai kula da cewa ta Kuma yin suman wucin gadi ba sai da yaga ta bingire..... *_afwan dears kuyi hkri Dan Allah suna muke wlh naso yafi haka Amma inshallah idan na dawo da wuri qilan in qara muku uzuri! Uzuri!! Uzuri!!! Dai nasan ba yawa kuyi hkri Dan Allah_* comment Share #repost 08038541511 [1/14, 12:30 PM] Zahrahbukar: *KARSHEN DUNIYA* _Kalubalenku iyaye_ *NA* *Zahrabukar* *Exquisite WRITTERS FORUM* _To masu cewa Dan Allah indinga banbance musu kar in musu tashi na kamaka Gashi na muku yanda zaku gane_ *BOOK 1is free* *BOOK 2 is paid* *sai dai Kuyi hkr Har yanzun ban fidda tsarin biyan kudin ba nasan soyayyah ce tasa kuke ta dokin ku siya nagode kwarai idan nagama wasu shirye shirye zakuga bayani Dafatan kun fahimta* *14* _______Fita yayi da sauri ya cimmusu yace "mama Kun fito humayda Kuma kamar Tana da bukatarku a kusa da ita " Kallon shi sukai har suna had"a Baki wajen "cewa kamar ya? " Sosa qeya yayi yace "itace tace na mata magana da ku inkun je zakuji" Ba musu suka juya suka koma gidan Salati suka saki sanda suka ganta kwance Babu mai musu bayani Dan Bashir Bai ma biyo su ba daga can ya qara gaba zuwa gidan su Wasu ruwan suka Kuma sa mata wannan Karan ma ta Dade kafin ta farfado sai dai abinda ta farka dashi ya firgita su Cikin fitar hayyaci take furta wasu maganganu "Meyasa zakamun haka Bashir? Dama baka da imani in rasa y'ata guda sannan kace ka sakeni? Wlh qarya ne qarya kake wlh" Ta rushe
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27