Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 12

Chapter 12

Karshen Duniya Book 1 Complete Hausa Novel 1,205 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

tsaye take tana safa da MARWA a dakinta kayan da sageer ya siya musu ne a gaban ta meyasa? Meyasa ita ba ta da sa"a? Umayma Basu Kai su arziqi ba Amma tafita sa'a a rayuwa meyasa komi ita ke fara Fara samu? Kallon farko da tayiwa sageer taji tana son shi Amma azuwan shi gunsu yace umayma yake so me hakan ke nufi? Cike da tafasar zuciya tafara maganganu "Idan na haqura da wani abun to wlh wannan Karan bazan hakura da sageer ba kiyi hakuri umayma sageer da ni yadace " Zama tai tana saqe saqe a zuciyar ta zuwa can Kuma naga Ta tashi toilet ta shiga, *************************Cikin farin ciki tashiga gidan su mahaifiyar ta na daki sai kishiyar mamanta dake falo Bata amsa sallamar ba ko kallon inda umayma take Bata yi ba ta juya kanta taci gaba da abinda take "Aunty sannu" batajira cewar ta ba Dan tasan dama ba"amsawa zatayi ba ta nufi dakin umman ta tsaye ta iske ta gaban sif tana jera kaya Sallama tayi ta amsa sannu ta mata sannan ta karbi aikin taci gaba da yi Fira suke sai da suka Gama jera kayan sannan ta jawo ledan ta tura gaban umman kallon ta tayi alamar neman qarin bayani tun haduwar su da sageer har kawo sun gida da yayi sai da ta fad"a mata Ajiyar zuciya ta sauke sanna tace "Lokaci yayi umayma idan kina ganin ya kwanta Miki banason doguwar soyayyar Nan ki tura shi gun abban ku yafara neman izini tukun bazan so ki gaggawa ba Amma ki nutsu ki fahimci manufar shi" Sannan daga yanzun kada ki Kuma karbar abin hannun shi kada ki Kuma shiga motar shi kinji ni?" Cikin sauri tace "naji umma Kuma inshallah zanyi yanda kikace" "To Allah ya Miki albarka Tashi kije Zan nuna wa abban ku kayan idan ya dawo" "To umma baran yi wanka" "Ok ki sauko mushiga kitchen" Ba gida ya nufa ba Dan dama ba al'adarshi bace kwana a gida Kai tsaye gidansu wata budurwar shi Azeza ya nufa " ko da tafito sun Dade suna soyayyar su ta Shan minti acikin motar kafin yaja motar suka qara gaba sai da sukaje gidan su ta qofar shi dake baya suka shiga " karshe ma Azeeza a gidan ta kwana "Sai da safe ya sallameta ta qara gaba shikuma ya koma bacci Dan Bai samu bacci ba adaren jia"l Baban umayma Koda ya dawo umman ta ta nuna mishi kayan yace Akira mishi umaymar bayan tazo kamar yanda tayiwa mahaifiyar ta bayani haka ta mishi shima ya yarda da ya Kuma gasgata abinda tace albarka yasa mata sannan yace idan ya Kuma zuwa ta turo mishi shi cikin girmama wa tace "to" fita tayi bayan ya sallameta" Basu taba kayan ba Abba yace abarsu har sai yaron yazo yaga yanayin tarbiyar shi tukun inyaji zai iya bashi yarshi Wayar ta akashe take shiyasa Bata da tabbacin yakira ta ko Bai Kira ba Baccin ta Tasha har zuwa sanda akai kiran sallar asuba ***************** A bangaren fateemah kuwa Bata samu rintsawa ba a Daren ta rasa samun mafita' a yanda take ji daga haduwar su da sageer zuwa yanzun idan har Bata mallake shi ba to wlh mutuwa zatai Dan wani nauyi taji zuciyar ta ta mata Dan ko sallar asuba Bata samu Yi ba Kuma akan kunnen ta akai kiran Karfe 8 ta sauko suka karya ita da familyn ta Babu walwala tare da ita hasalima wani fitinannen ciwon Kai ke damun ta Kowa ya tambayeta sai tace kanta ke ciwo Bata samu bacci ba jia sabida karatu ta kwana yi . Sannu kowa ya mata sannan maman ta tace ta koma ta kwanta kafin lokacin da zasu shiga lecture yayi" Bata Musa ba ta tashi ta koma dakin shigar ta kenan taji ringing din wayar ta Tsaki taja bayan taga sunan umayma" a screen din Bata daga ba Dan zuwa yanzun tsanar Umayma ce fall ranta ta umaymar " mafita kawaii take nema domin tana da tabbacin Zuwan qarshen qawancen su yayi ********************* *Alh* bilya bello shine cikakken sunan shi matar shi d"aya *haj* yahanazu auren soyayya sukayi haifafun cikin garin katsina ne su duka Kuma anan suke zaune yaransu uku Abdul"ahad *Tahseenah* sai auta Azeema" Alh bilya bello Mahaifanshi duka suna da Rai " mutum ne shi a fuska kyakkyawa Amma azuci bashi da kyawu ko kad"an cikakken d"an qungiyar asiri ne Haj yahanazu ita mahaifin ta yarasu a gun mahaifiyar ta tashi cikin tsanani da wahala Dan talakawa ne na gasken gaske futuk shahararrun fakirai ne na bugawa a babban bangon jaridar duniya......... Comment Share 08038541511 [1/16, 11:09 AM] Zahrahbukar: *KARSHEN DUNIYA* _kalubalenku Iyaye_ *na* *Zahrabukar* *Exquisite WRITTERS FORUM* *_16_* _________Waye Alh wada? shine Wanda yake lalata rayuwar yara maza nutsattse ne a da mai sanaar siyar da fruit tarihin nutsuwar shi yafara ne watarana """"""""Wata Daria aka kwashe dashi d"aya ya matso gun shi yace "Wada wada wada Berry ya kagani ? Tabbas yau ranar sa'ar muce ba banza ba qungiya ta bamu shawarar zuwa park din Nan Ashe sun San zasu turo Mana Kai?" Dayan yasake kyalkyale wa da Wata kafurar Dariya yace "Nayi mamakin dama da akace muzo Park mu aikata wanan abin zamuga Mai zai faru to gashi ta Tabbata" Kallonsu yake a razane suwaye? Mekuma suke nufi me suke nema wajensa? Tunaninshi ne ya katse sanda yaji an dafa shi Daya ne acikin su yace mishi "ka Gane ni?" Girgiza Kai yayi yace "nine Wanda muka had"u dakai shekaru uku da suka wuce Kana siyar da fruit na siya na barmaka canjina in baka manta ba a lokacin ai na maka wata magana ko?" _abinda ya faru 3years ago_ Tafe yake yana tura Baron kayan fruit din duk ya gaji ya had`a uwar zufa ga yunwa ga ba ciniki Yana cikin tafiya wata mota tai parking mutum daya ne aciki ya tsaidashi ya siyi fruit din bayan yabashi kudin kallon yatsun hannun shi yayi take meeting din qungiyar su ya fad"o mishi na jia kowa an bashi zabin abinda ake buqata so shi nashi ana buqatar yakawo mutum Mai yatsu shida a hannu yashigo dashi qungiya so ganin hannun Wada berry har ya tafi sai Kuma yadawo Zuge glass din motar yayi yace mishi yana da magana dashi Kallon shi yayi yakuma kallon motar kafin yace "to inaji zaka fito ne?" "Why not?" na cikin motar yabashi amsa Yana kokarin fitowa daga motar "Baran fito" Wuri suka samu suka d'an keb'e sannan mutumin yace meye "sunan ka?" Kallon shi yayi irin meye had"Inka da sunana" ? Kuma tambayr shi yayi sannan yace "sunana wada Amma anfi kirana da wada Berry" "Ok tom wanan itace sanaar ka? Gyada Kai yayi yace "kwarai domin akan ta ka ganni ai" murmushi mutumin yayi yace 'hkne but kamar da wahala acikin ta me zai Hana ka canja wata?" Kallon shi yakuma yi yace "ko?" Gyada mishi Kai yayi yace "kwarai ga sana'o' Nan birjik sai wacce ka zaba?" A takaice yabashi amsa "Nafi buqatar wannan din ai" Dariya yayi yace "acewarka ba? Amma kowa ya ganka yasan kana cikin wahala well why not in taimake ka?" Kallon shi yayi sannan yace "If u need

Table of Contents

Chapters

27 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});