Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 11

Chapter 11

Karshen Duniya Book 1 Complete Hausa Novel 1,199 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

da wani irin kuka Mai Daci da Makakilo duk da kallo suka bita jin wani batu Kuma ana zancen mutuwa ga wani sabon zance """ Har suka iso gida Bai Kuma tankawa ba shi kadai yasan irin xafin da zuciyar shi ke mishi Itakam uwar karad'i tun da taji ta bige goshi bata Kuma magana ba Har suka karaso gidan bayan Mai gadi ya bude musu ta shigo ya na daidaita wa motar Zama yaji ficewar Azeema Da gudu ta fice a motar ya Dade a zaune Yana tufka da warwara kafin daga karshe ya Sami mafita wani kafirin murmushi yasaki kafin yace *_naku wasa ne in kunsan wata ai Baku San wata ba" ya dai tawace so muzuba mugani_* Cikin farin ciki yashiga gidan harda y'ar waqarshi a Baki Ya Sami tarba Mai kyau agun umma ya mata ya gajiar biki tana ta bashi labari har ya shirya suka fito A falo suka iske Azeema tana kallo da gudu taje ta rungumeta "tace momy we miss u alot gidan so lonely da bakya Nan"murmushi tayi tace "ba wani Nan bayan kin gudu gidan Granny kin barmin daughter ita kadai?" Murmushi ta kuma yi tace "hmm momy akwai fa labari dazun Ina baiwa Abba labarin ban qarasa ba naji goshi na ya bada dumm Ban qarasa ba tsananin zafi Kuma Abba ko ya min sannu" Dariya take tace "ai maganin Parrott kenan gobe ma Kya qara" Kyabe fuska tayi tace "na ma fasa fad"a Miki tunda bazaki min sannu ba" Dariya sukaji a bayansu tare suka juya tahseenah ce take musu dariya tace "yau ga umma da autar ta mun gansu a Rana nidai ni da abbana ba ajin kanmu ko Abba?"ta maida tambayr ta gun Abba shima fuska a washe yace "sosai ma Waze ji Kan uba da y"arsa?" Dariya sukai gaba daya sannan umma tace "muje anshirya dinning " A nutse suke cin abincin har suka Gama sannan umma tace "Wai nikam Ina Abdul tunda na tafi bami waya ba nadawo Kuma banganshi ba?" Azeema tace "wlh umma yah Abdul Bai zama gida tun Randa ki ka tafi banqara ganinshi ba" tahseenah ce tace to "kanwa uwar gami Umma qarya take ko jia yazo ya dauki kaya yace min abokin shi ke asibity to shi ke jinyar shi Kuma a asibityn ya nemi wayar shi Bai ganta" ba" Ajiyar zuciya ta sauke tace "to alhmdlillahi tunda lapiya wane abokin nashi?" Abba yace "muheeb yake kowa kinsan sunfi shaquwa ai" Haka sukai ta fira cikin nishad'i Kafin lokacin kwanciya yayi kowa ya nufi makwancin shi _________ Jin qarar horn yasa ta dawo hankalinta kenan sageer fita yayi to yanzun da ya fice ya barta da ilham ita ba likita ba ya zatai da ita ?. Yarinya ko zama ya gagareta da ta zo miqewa sai fitsari ya zubo ta rasa ina zata saka RAYUWAR ta abin takaicin ma wa zata Kira in ta Kira tace me ? Dan mijin ta yayiwa y"ar ta *fyade* ya gudu sannan shima mijin ya juya musu baya" Girgiza Kai tayi ta share hawayen da suka zubo mata Tafara safa da MARWA ta rasa me ke mata Dadi a duniya wane bango zata jingina taji Dadi dama shaquwa tsakanin y"an uwa yanasa cutarwa? Dama soyayya ta Kan zamo makamin cuta? To ko dai haqqin umayma ne zai Fara bibiyar ta tun a yanzun ? Cike da tashin hankali kwalwar ta ta juya ta fara tunanin baya " *_waiwaye_* Alh sani na Abba shine mahaifin ta mahaifiyar ta " haj habiba Yan uwa ne auren zuminci sukai itace ya ta uku agurin iyayen ta " yah hafeez yah Nadeem sai ita fateema sai qannen ta haris da zubaida" sun taso cikin so da kulawa gata Kam sun sameshi iyayensu sun fi bama ilimin Boko muhimmanci shiyasa basui zurfi a ilimin addini ba Mahaifiyar ta Bata da kishiya Amma haka ta taso da tsananin kishi" Kishinta har akan Yan uwanta nunashi take ko wani Abu aka Basu ko kala a ka canja to sai tayi kishin an Bata kala mara kyau haka zatai ta Jin zafin Yan uwanta har sai an hada kayan wuri daya ta zabi abinda takeso sannan a zauna lpy haka aka Saba mata da wannan Hali har girmanta Sageer salees Dan kano shine sunan shi da na qarshe a gidan su su hudu ne a gidan su yayyenshi mata ne shine kqdai namiji yataso cikin gata da kula shima Bai samu zurfin ilimin addini ba" ya dai samu na boko Dan yanzun haka ma da bokon yake ci" A sangarce ya taso Dan ba kwaba ba kyara " aqalla ba a kasara ba yayiwa yan mata" shida ciki wasu sun San gidansu wasu Kuma Basu sani ba ma"abocin yaudara ne ya iya tsara mace shiyasa Bai shan wahala yake Jan raayin su su fada tarkon shi" Koda kin kai qara gidan su to iyayen sa basa masa fad"a sai ma sui muku barazanar zasu sa akulle ku yawanci suna barin cikin su Haifa sai su Kai titi su Yar wasu kuma su jefa masai wasu Kuma zubar da cikin ma sukai wasu ta sanadiyyar haka iyayen su suka koresu suka fada duniya _watarana_ Yana tafe a mota Yana shan kida har ya qaraso wani park parking yayi yafito ma"abocin ado ne Dan haka a yau din ma cikin adon yake" Yana tafia Yana basarwa har ya gota inda suke zaune yadawo da baya da yake ya iya basarwa sai ya nuna kamar ba Dan su yadawo ba hasalima sai ya dauki dutsi Yana da Dan jefashi Sama Yana cabewa cikin Sa a kuwa" ya cilla wani sai akan screen din wayar ta""" a tsorace ta dag'o taga meye ya fad'o idon ta ya sauka cikin na shi........... _to fans Allah yakawo mu mu waiwaya zamu tsunduma Muji shin menene tushe mafari? Gamu dai ku biyo ni zan warware muku duka abinda yashige muku duhu_ Comment Share #repost 08038541511 [1/15, 2:23 PM] Zahrahbukar: *KARSHEN DUNIYA* _Kalubalenku iyaye_ *NA* *Zahrabukar* *Exquisite WRITTERS FORUM* *15* ________Kurawa juna ido sukai na tsawon sakanni daga bisani shi yafara kauda na shi idon , Itama janyewa tayi cike da kunya Murmushi yayi yace "sorry pretty Ina fata dai ban Miki b'anna ba?" Itama murmushi tayi tace "ah ah baka min banna ba ko kamin ma na yafe" Zama yayi akusa da ita yace "to ngd da gani dai wnn gimbiyar akwai saukin Kai " Dukar da kanta tayi batace komi ba" fateema dake gefenta ta tsura mishi ido Bai ma San tanayi ba hankalin shi na gun umayma fira suke kamar wadan da suka Saba umayma ce ta gabatar mishi da qawarta fateema kallo daya ya mata ya Kau da Kai bayan yace "sannu fa" cikin rawar murya tace "Ina wuni" "Lafiya"kadai yace ya kauda idon shi Haka sukai ta fira cikin salon iya tsara mace a Dan zamansu har yasan sunan ta anguwar su hada no din wayar ta ya karba Da suka tashi tafia ma shi ya daukesu a motar shi suka bita shop yamusu siyayya sannan ya Kai kowacce gidan su yayi mamakin ganin gidan su umayma Bai Kai gidan su fateema tsaruwa ba Bai wani damu ba Ya mata sallama ya tafi, _____________ A

Table of Contents

Chapters

27 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});