Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 24

Chapter 24

Karshen Duniya Book 1 Complete Hausa Novel 1,204 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

tayashi hankula sukayo kanmu ina kallo su bayan an kwacen a hannunsu suka ja motar suka tafi suka barni" Na Dade agun ina jinjina wannan lamari dama banyi mamakin cikin ba Tunda nasan ta inda aka sameshi mamakin yanda lokaci daya jarabawo wi masu wuyar ci keta jerin gwanon kunno wa rayuwata Haka na tashi na nufi hanyar gidan zuciyata namin zafi Inajin jiri ga rashin sanin me zan tarar na karaso Kwata kwata mani kaina a kulle yake nakasa yin wani tunanin .meye mafita a gareni. Haka dai jiki a sabule na tura kqaramar kofar gidan na shiga" Direct babban falon na wuce inda acan nake jiyo hayaniya da sheshshekar kuka' Zuciya ta naji ta fara dake min Naji na shirya karbar duk wani abinda zai biyo Baya kamar sukar mashi Naji wani Abu yabi ta kunne na nauyin day baki na yayi Naji Babu na jaraba yin magana da kaina Naji inaji kuma maganar ta Fito abin murna ne wannan tsawon lokaci magana ta dauke min Kwatsam Kuma ta dawo a lokacin da bazata amfane ni ba na zura qafana bakina had'e da sallama Duka mutanen falon suka zuro min ido ban iya d'aga kaina na dubesu ba zan Kuma d'aga kafa kenan tsawar abba rabiu ta dakatar Dani yace "dakata daga Nan fandararriya kada ki kuma kokarin tako kafarki a cikin falon Nan" Cakk na tsaya kaina a qasa nakasa d'ago kai ban ankara ba naji wasu tagwayen maruka Mama na ce kuka take sosai ta kasa furta wata kalma duka na take aka rasa mai hana ta Har ta gaji ban motsa ba Sai huci take ta dafe kirjinta bansan me suka gaya mata ba Amma nasan bazai wuce zancen cikin na. Ta dafe kirjinta Tana ambaton sunan Allah Can taja wata gajeriyar ajiyar zuciya ta hadi'iyi wani abu Qutt take ta fad'i agun" Tana zuwa Nan kukan ta ya tsanan ta tace "Umayma ranar naga bala'I tsantsa har kullum Ina bawa kaina cewa nice silar mutuwar mamana" "Faduwar Nan da tayi ashe zuciya ce ta hadiya da sauri akazo kanta mamana ce fa amma kowa tureni yake a kanta Yan uwan ta sukai dafifi a kanta Aka duba aka tabbatar rai yayi halinsa" Wallahi inajin ana cewa innalillahy wa Inna ilayhirraji un" bintu rai yayi halinsa Wlh bansan sanda na fasa wata qara na fad'i agun ba dama A ranar bakina ya bude" Suma nayi umayma amma rashin imani tsantsa aka nuna min haka aka tsallake ni akaiwa maman sutura aka kaita makwancinta Ina a halin suma sai da aka dawo daga janaza sannan aka kwara min wasu ruwa masu azabar sanyi, Kamar ba Yan uwana Ba haka na farfado Babu tsoron Allah ba komai ga yan gaisuwa akai ta yayatani cewa na kashe mamana sabida nayi cikin shege ta hadiyi zuciya ta mutu Ina kuka ina su tsaya in musu bayani Basu saurareni ba' suka tarka Tani nida kayana suka wullo ni waje" *Bazan bata musu sunan zuria ba inje duk inda zani abinda ya had"a ya raba"* Kalmomin Nan har gobe suna amsa kuwwa a kunne na kinsan wake fad'ar hakan?" Umayma ta girgiza kai Hmm to kaka malam ne wanda dawowar shi kenan daga katsina ya iske wannan tashin hankali' Haka tsohon nan ya murza wa idon shi toka Shine a sahun gaba wajen korata Jama a natamin tofin Allah tsine Saboda tsabar radadin da zuciya ta kemin wlh na nemi kukan ma na rasa"..... Na shafe kusan aqallah awa uku a unguwar duk wanda ya zo wucewa sai ya jefamun kalamai masu muni' Ganin dare na niyyar yi ga yanayin da nake ciki yasa na tsaida Dan sahu yakaini family house nasu abban mu Ashe suma labari yakaimu su duk ma ashe dasu akai janazar mama' ko karasa sallamar banyi ba" Maman abban mu ta tsigalo mun ta rufeni da zagi yayun Abba na taya ta Yaransu na tsakar gida suka dinga min eho suna jifana" har waje suka biyoni da duwatsu Haka suka taramin jama"a Yan kallo Zuciya ta tamin nauyi kowa ya kasa min uzuri ciwon kai da tsananin tashin hankali suka sa naji wata iriyar juya idanuna suka rufe jiri ya debeni nakuma zubewa' agun....✍🏼😭😭😭😭 _Innalillhy wainna ilayhira jiun wallahi muji tsoron Allah rayuwa ta Zama abin tsoro Babu sauran abin yarda acikin mutane mu kula da yaranmu ko iyayensu maza mu dinga taka tsantsan da yawan shigewa Jiki rayuwar ta juya idanuwa sun Rufe masu tsoron Allah sunyi karanci a cikin mutane_ Comment Share 08038541511 [1/30, 9:08 AM] Zahrahbukar: *KARSHEN DUNIYA* _kalubalenku Iyaye_ *na* *Zahrabukar* *exquisite WRITTERS forum* *masu himma tuni sun fara subscription kui maza ku hanzarta fa kar ayi baku Tafiyar Mai tsawo ce Akwai rikita rikita da bankade bankade cin amana daukar fansa Mai zafi yaudara zamba cikin aminci kawata matso kusa da yan kudinki kalilan ki kwashi garabasar wannan daddad'an labarin* Normal group #300 VIP #500 special #600 _duk tsarin da kike bukatarku zaki samu Akwai banbanci yawan posting a kowacce rana akan kowanne tsari_ ki biya yan sulallan ki ta wannan account number din *6035968908 keystone bank umma yusif* Sai ki Turomin shaidar biya akan wannan number din 08038541511. Sai insaki paid group *28* *saura page biyu free page ya kare ku hanzarta Kuyi subscription* "A ranar na tabbatar da cewa bani da sauran gata a duniya bani da wanda ya ragemin da zai tallafi maraicina Babu uba itama uwar yau nayi sanadin mutuwar ta me yaragemin a DUNIYA? Suman Nan da nayi babu wanda ya taimaka ya samin ruwa haka suka barni a gun a kwance" Ga kullin kayana a gefe" Umayma anan na kwana sanyin asuba ne ya bigeni yasa na farka da sunan Allah a bakina Jikina ko' Ina ciwo yakemun kaina yamin wani irin nauyi zuciya ta cinkushe da abubuwa masu wuyar fassara Haka na tashi na kakkabe jikina' ina kallon gidan banyi gigin Kuma zuwa ba Dan a lokacin bansan me zasu aikata min ba Kayana na dauka Na bi hanya bansan ina zani ba bani da sauran wata madogara Ga yunwa ga tarin baqinciki da ya tokare min kirji '' Ina tafia Ina cin tuntube dayake gari bai idasa wayewa ba so ban hadu da wasu mutane masu yawa ba har na bar unguwar Direct Park na wuce bani da ko sisi' na shiga motar Kaduna Dan zuciya ta zuwa lokacin ta gama konewa buri na daya ne in natsu inyi wa kaina tunanin mafita tare da daukar fansa' Mota na cika driver ya tada muka miqi hanya' Ana tafia aka buqaci kudin mota nace bani da ko sisi' sumin taimako' Aikam driver Nan kamar ya cinye ni sabida masifa ana ta bashi hkri yace bazaije Dani ba sai dai ya sauke ni' naita bashi hkri' Ganin dai zai saukenin dagaske yasa nace Dan Allah da akwai wanda zai siya kayana sai in biya kudin"? Wata mata tace fito dasu mugani suturu na masu tsada na fitar nasiyar a wulaqance na biya kudin mota' Na rike wasu canji da zanci abinci' Haka akai ta tafia har Allah yakaimu garin kaduna" Kowa ya sauka nima na sauka a tashar na siyi tea da bread nasha Sannan na fito nayi tafia mai nisa Sannan nasamu wani guri na

Table of Contents

Chapters

27 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});