Chapter 9
Chapter 9
bazan iya rayuwa acan ba". "A haba dai hajiya me yasa"?. "Abincin kune bazan iya ci ba gara na zauna anan naci wanda na saba dashi". "Wanne kalar abincin ne baza ki iya ciba"?'. Cikin tsufa hajiya tace kaga ta farko wacce na tsana andosi da kwai dinnan". Dagowa Al'ameen yai cikin mamaki yace" me andosi kuma? abinci ne? ni ban ma sanshi ba". Dariya sosai sadiq keyi yace hajiya kina burgeni wato indomie kike nufi itace andosi". Hajiya tace "Eh da wannan abin me kamar tsutsa da kuke ce masa damaroni da sifagatin du bana ci ko an kawo min daga gidan muntari". Sadiq dake rike da ciki yace lallai kam hajiya yi shiru haka ciki na ya fara ciwo makaroni da spagetti ni kuwa abinci na kenan". "Shiyasa gaka nan kamar iska ta bushe kun 'ki al'adun hausa sam". "To hajiya yanzu ba gani nazo ba saina cika ciki na da rama da zogale kafin na tafi"'. "Daka kyauta Saddiqu ina iyalin taka ne Ri'kayye ko tana gida nasan da daita kuka zo da yanzu ta karaso" Cikin mazu Sadiq yace bansan wata Rikayye ba idan mata na kike nufi sunanta Ru'kayyah". "Ita nake nufi mana saboda bakin ciki shine ka 'ki zuwa da ita". Batare da Al'amin ya dago ba yace hajiya meye abin bakin cikin dan kawai baizo da ita ba"?. Hajiya data balli goro tace kai kuma kamin shiru ba dakai nake ba tuzurun banza kalleka kato dakai idan anan ne kana da 'ya'ya wajen biyar". "Ai hajiya daina fada 'ya'ya biyar sai kace na hada dangi da kaji uku ma sun isheni shiyasa bazanyi aure da wuri ba". "Ashsha kayi ta banza bari ai Mustaphan zaizo ya same ni zanji idan shine ma yake karanta maka kada kayi auren da wuri saiya bani amsa". Page 17 to 18. Basu bar gidan hajiya ba sai bayan sallar isha a kofar gida saman dakalin Al'ameen ya zauna sa'banin sadiq daya shiga cikin gida". Yana nan a zaune Sa'adu yazo yasha wanka ya sako gwanjola irin takalmi sau ciki na roba"'. Kallon sa Al'ameen yai tun daga kai har kafafu lokaci guda murmushi ya 'kwace masa ganin sai wani buda kafada yake". Fati ce ta fito tana nufar inda yake tsaye wanda ko minti biyu basuyi ba Abuh ta karaso gurin da 'kawayenta tana haki tace". "Amma Sa'adu me nace maka ba nace kada ka sake zuwa gurin Fati ba nice nake sonka ba ka amince rannan a dandali ba saboda kai mun rabu da ilya". Shiru Sa'adu yai cikin takaici Fati tace wai dan Allah Abu meye hakan me na tare miki da bakya son gani na cikin farin ciki"?. A gadarance Abu tace ban sani ba bani da lokacin ki kai kuma muje ". Kamar rakumi🐪 haka Sa'adu yabi Abu zuwa dandali kamar yadda ta bukata 'kawayen Abu na yiwa Fati dariya da habaici suka bar gurin". Wasu zafafan hawaye ne suke zuba a idanuwan Fati gashi gobe ne gasar nuna samari yanzu ita ya zatai da rayuwar ta cikin takaici ta juya zata shiga gida". Al'ameen dake kallon ta yace " madam ji mana ". A firgice Fati ta kalli inda yake tana goge hawayen fuskarta" Jitai yace mene sunan ki"?. Muryarta na rawa sakamakon kukan da take tace suna na Fatima". "Ok yayi jeki" kawai yace yana mayar da hankalin sa kan waya wucewa tai ta shiga gida. Cikin shishshigi da cusa kai Saude ta shiga dakin da mami suke tana cewa Aisha a karo muku abincin ne". "A'a ya isa haka mun gode". "To shikenan bari na kawo miki wata kyakkyawar fura ko zaki sha". Fita tai tana daukowa ta kawo mata sannan ta musu saida safe ta fice tsaki mami taja tana rakata da harara tace ko ina ruwanta dani mayya bazan sha ba aikin banza kawai". 'Yar dariya Afeeyah tai tana gyara kwanciyar ta yayin da mami take ta maganganu da fada ita kada kadai. "kawai an kawo mutum wannan mugun kauyen an ajiye duk zafi babu wata ni'ima ko jin dadi ba a.c haba wallahi bazai yiwu ba dole gobe na samu alhaji idan shi bazai koma gida nikam na gaji zan tafi". Shiru kawai Afeeyah tai tana sauraron mami da mamakin furucin ta amma batai magana ba saboda gudun abinda mamin zata ce mata saidai bata jin dadin yadda take kushe 'kauyen mahaifin nata domin itama tana son garin ". Washe gari Al'ameen bai tashi bacci da wuri ba har rana tai saida Sadiq ya tashe shi yana mikewa ya rike kansa tare da cewa. "Subahanallahi wannan karar haka kamar zata fasa min kunne kuma daga ina me suke". Sadiq dake shirin fita yace bazan jira kaba domin an fara wai wani biki suke na nuna samari" yana fadin haka ya fice. Shiru Al'ameen yai kamar kuma an tsikare shi ya mike cikin gaggawa yai wanka ya shirya yana fita yaga Salamatu ta fito daga daki. Bayan sun gaisa yace ina Zarah". Cikin mamaki tace wace haka"?. Tunawa yai sai kuma yace oh Fati nake nufi tana nan". "A'a wallahi bata nan ta dade da fita ban sani ba ko tana gurin bikin wasan samarin can nasu da suke". "Ok" yace yana fita daga gidan harya kusa zuwa yaji kid'an na hawa kansa domin makad'a ne da yawa da maroka na gari da gari suke taruwa su zo". Juyawa yai ya fasa zuwa hango wasu gajerun bishiya masu ni'imtacciyar inuwa yasa ya nufi gurin dan yadan huta". Yana karasawa yaji ana shashshekar kuka cikin mamaki ya soma dube dube can ya hango me kukan zaune ta kifa kanta". Har zai rabu da ita sai kuma ya tuna duk wanda ya sharewa wani hawayen sa Allah zai share masa shima". Tunani ya farayi to me zaice mata zuwa wani lokaci da yaga bashi da mafita yai gyaran murya". Da sauri ta dago a razane wanda shi yana mamakin ganinta a gurin ita ma tana mamakin ganin sa". "Kukan me kike"?. Shine tambayar dayai mata kaita girgiza tana cewa" ina kuka ne saboda dazan aje abin fada zanyi abin kunya yau ranar fitar da gwani ne a dandali". "Kamar ya"? Me kuke yi idan kunje"?. Gyara zama tai tana cewa da farko idan kowa yaje me kira zai rika kiran suna mutum da budurwar shi su fita fili ya bata kyautar zobe da agwagi guda uku shikenan sai su fita wasu su shigo. To kowa ya sheda ya gani wace nada saurayi kuma baza a kada mata kalangun tayi kwantai ba idan kuma baka da saurayi kowa saiya sani ayi ta maka dariya". "Toke yanzu bakije ba kina nan idan aka kira sunan kifa kisa saurayin naki ya rude". "Ni bazan je ba". "Saboda me"?' "Idan naje ma babu amfani wazan nuna wanda yake sona yayata Abu tamin 'kwacen sa bani da kowa". "Zaki are ni"?. Cikin rashin fahimta tace aron me". Basarwa yai tare da cewa muje na ga abinda kuke yi a bikin. Badon taso ba jikinta a sanyaye ta mike suka tafi dandalin shake yake sosai da mutane suna zuwa sai zance da yamud'id'i da munafirci ake ana ta kallon Al'ameen'. Me shela ne ke cewa anzo gidan. Muntari na alhaji attajirin yan kauyen nan me taimako
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25