Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 22

Chapter 22

Dan Millionair Book 1 Complete Hausa Novel 1,198 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

zama zansa a gyara maka part dinka gobe". "Meyasa mami bayan ga gida nacan da matata taya zan barta ita kadai na dawo nan". "Allah ko sannu me mata karka batawa kanka lokaci na kora ta garinsu". Wata irin juyowa Al'ameen yai yana kallon mami cikin tsananin mamaki yace mami kin kora ta garinsu saboda me"?. "To babana matse ni saina fada maka dalili kuma ban yafe maka idan kaje wannan matsiyacin kauyen balle kace zaka dawo da ita yadda ka ci mutuncin Zainab ka wulakanta ta ka saketa haka itama nake so ka rubuta mata takardar saki uku ba maganar kome saidai ka auro wata". Wata iriyar hajijiya ce ta debi Al'ameen da sauri ya zauna tare da dafe kanshi maida hankalinta mami tai akan aikin da take tana cewa". "Kome zakai saika saketa bazan taba daukarta matsayin suruka taba". Jin tafiya yasa ta dago ganin daddy ne tadan zaro ido tana fatan Allah yasa baiji zancen da suke da Al'ameen ba. Shi kuwa ya riga ya gama jin komai muryarta nadan rawar rashin gaskiya domin tun ranar da ta daki Fati basu sake haduwa dashi ba saiyau tace. "Sannu alhaji". Banza yai da ita ya dauke mata wuta kamar baiji ba ya karasa inda Al'ameen ke zaune yana dago kansa. Ganin hawaye a fuskarsa abinda ya manta yaushe rabon daya gani tun yana yaro saiyau cikin tsananin bacin rai da fushi ya juyo inda mami take yana kallonta yace. "Yau tafaru ta kare Aisha kullum ina miki gargadi dajan kunne bakya dauka to yau zakiga sakamakon abubuwan da kike aikata min". Part dinsa ya shiga mintuna biyu ya fito da takarda a hannunshi yana cilla mata cikin kakkausar murya yace". "Ita kin bata minti biyu ni kuma minti daya na baki kada ki kuskura na fito na sameki kibar min gida na". Mikar da Al'ameen yai yana shigar dashi part dinsa sannan ya fito ganinta zaune tana kuka yasa yace ki fita a gidan ko a hanya sai kiyi domin na gaji da ganinki". Cikin kuka mami tace alhaji kayi hakuri bazan sakeba na tuba". Kai ya girgiza ai Aisha bazan iya sake zama dake ba kina lalata min zumunci da hana zaman lafiya ya zaga ahli na". "Wallahi alhaji kaban dama na karshe zan gyara hali na tun muna kuruciya banje gidan mu da sunan yaji ba saiyau naje da takardar saki wannan abun kunya har ina alhaji ka dubeni". "Ai Aisha abinda ya dace dake na baki hukuncin ki kenan". "Kayi hakuri kamin sutura alhaji zan gyara kuskure na namaka alkawari". "Aisha bazan miki uziri ba a yanzu rayuwa ta bata bukatar ki na datse duk wata alaka dake tsakanin mu"'. Cikin kalar tausayi mami ta durkusa gabansa tana masa magiya amma sam ya dauke kai daga saitin ta. Mikewa tai ganin babu alamar zai karbi bada hakurinta tana kallonsa tace" na baka hakuri amma alhaji ka 'ki.............. Katse ta yai "ki barmin gidana bana son jin komai daga gare ki" bar mata falon yai . Dole mami tahau tattara kayanta kamar yadda taiwa wata itama ta nufi gidansu cikin bakin ciki da kunyar yadda zata fuskanci mahaifanta. Ranar kwana cur mami tai a zaune bata ko runtsa ba tana kuka har zazzabi da ciwon kai suka rufeta. Washe gari ma haka ta wuni rim a kwance babu cin abinci babu shan ruwa ga fadan da tasha gurin dattijon mahaifinta. Nadama iri iri babu wacce mami batai ba da dana sani domin a rayuwarta tana matukar son daddy kamar ranta. Fati na zaune a kofar dakinsu tana gyarawa umman ta waken da za'ai abincin rana Saude ta fito daga dakin ganin Fati zaune yasa tace. "Humm yan birni har dubun naku ta cika asirin da kukai musu ya karye ko kuma kinyi halin 'bera sun fatattako ki ko"?. "Meye gaskiyar al'amarin fada min gashi zaki abin kunya ki haihu a gida tir da wannan abu ina tausaya miki domin zilamar uwarki dason zuciyarta ne ya jawo miki". "Koma dai ba cikinsa bane shiyasa suka koro ki iye fada min naji domin yadda idonki yake a tsayen nan zaki iya aikata komai maganin son banzar ku kenan kunga kudi shine kuka rude saida kuka shiga jikinsu ai dama duk wanda yahau motar kwad'ayi yasan baida gurin sauka sai tashar wulakanci". "Kiyi addu'a kada ki haihu su 'ki karbar d'an yan kauyen nan su samu abin gori kI shafawa danginku ba'kin fenti". "Koda yake nasan me za'ayi zan taimake ki na karbo miki magani kawai kisha d'an ya mutu ko idan kin haifeshi ki sha'ke masa wuya bada sanin kowa ba kinji zan rufa miki asiri babu wanda zai sani amma kudin da kika sato musu daga can zamu raba idan kin yarda"?. Ko dagowa Fati batai ta kalli Saude ba balle tayi tunanin zata bata, amsa kawai aikinta take". Tsaki Saude tai ke dalla gafara don ma za'ai miki sutura shine kike min wani gani gani wato ke uwar dabaa lamba d'aya ko"?. "Aiko kin shiga uku a gurina dan saina zaga kauyen nan na sanar dasu kinyo cikin shege a birni". " ta fada tana saka hijab tare da rufo dakinta tai hanyar waje tana cewa" bari na fara daga makotan mu su tabawa da Aliyah" da kallo Fati ta bita tana share hawayen daya zubo mata". Shigowar Salamatu ganinta haka yasa ta tambayeta" Fatima lafiya kike kuka? kiyi hakuri kaddararki kenan ki dage da addu'a babu abunda ya gagari ubangiji shine mai bayarwa,". Kukan Fati ne ya fito fili cikin damuwa tace "umma ba laifin Al'ameen bane baisan ma na taho ba yana asibiti mami ce ta min komai". "Duk da haka kinga ki kwantar da hankali komai yai farko wata rana zaiyi karshe idan Al'ameen mijin zaman kine zaki koma". Kai Fati ta girgiza tace "nifa umma wannan ba shine matsala taba damuwa baba Saude yanzu tasa hijab ta fita wai seta zagaye garin nan tace ba wani aure danai cikin shege ne". Kirji Salamatu ta dafe tana kallo Fati tace" ita Sauden ce tace haka? Innalillahi wa inna ilaihi raji'un Allah gamu gareka kaine gatan mu". Fati data sauke ajiyar zuciya tace" amma umma ya kamata a dakatar da ita kinsan halin kauyen nan da kama abu ina tsoron sharrin su". "Ya zamuyi Fatima waye zai iya dakatar da ita baban kune kuma baya nan sharrinta bazai tasiri ba domin muna da gaskiya ita kuma 'karyarta koda tayi fure bazatai 'ya'ya ba dan 'karya 'karya ce koda an lullubeta da sutura". "Shikenan umma zan dage da addu'a Allah ya saukaka min abinda ke damu na yasa karshen wahala ta kenan". "Yauwa Fatima haka nake son ji Allah ya miki albarka ya had'a ki da abinda zai zamo alkairi a rayuwarki". "Ameen umma nagode da addu'arki da kyakkyawan fatan ki gareni" Fati ta fada cikin jin dadi. Page 37 to 38 Bayan wata d'aya Mami na zaune a daki ta zuba uban tagumi naban tausayi ta rame tayi duhu saboda damuwa da rashin kwanciyar hankali. Sallama wata mace tai tana cire nikaf din fuskarta ta zauna kusa da mami tana kallon ta tace . "Haba Aisha kina rage yawan wannan tunanin da kike saikin dorawa kanki hawan jini garin wanke biyar a 'bata goma".

Table of Contents

Chapters

25 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});