Chapter 10
Chapter 10
muntari gwani me 'kwazo ina babbar 'yarsa Abu ta fito mana fili da nata gwanin". Fita Abu tai tana hura hanci yayin da Sa'adu ya fito ya tsaya a gefen ta yana cire zobe ya bata sannan ya bata agwagi guda biyar. Lallai su Saude za a sha dafgen nama🍖. Suna fita me hela ya sake rafka cikiya ina 'yar uwarta Fatima ta fito fili da nata gwanin itama". Jikin Fati tai yadau rawa cikin nadama da dana sanin inama bata zo gurin ba . Kaurewa akai da surutu kowa da abinda yake fada wasu na mata dariya wasu na tausaya mata". Ina Fatima ne ko mu buga miki gangar bandaro me kwantai" maroki ya fada yana le'ke -le'ken inda zai hangota". "Ehhhh kawai a kad'a mata mu cashe " guri ya kaure ehhh a buga ehhh a buga. Al'ameen da abin ya bashi dariya shiga cikin filin yai yana murmushi yaiwa me hela magana". "Heeee a saurara jama'a ina mewa Fatima dariya😂? To ka rufe bakin ka🤐 ina maison jin jarumin💪 Fatima? To bude kunnen ka👂 dakyau ina mai nuna Fatima da yatsa👉? To ka sauke hannunka ina me son ganin gwanin Fatima ya matso kusa ya bude idonsa 👀yai kallo inji wannan zankadedan saurayin yace shine saurayin Fatima"' Me hela ya fada tsit guri yai kamar sun mutu kowa idonsa nakan Al'ameen wasu suce ba mutum bace aljani ne wasu suce daga ina ta samo wannan. Fitowa filin Fati tai tana mamaki kare tan da Al'ameen yai a haka idan ka kalleshi zakai tunanin zaiyi girman kai. Kudi masu yawa Al'ameen ya baiwa marokan da makadan wanda me hela da lasafika a susuce ganin kudin da baiyi zato ba yace. "A saurara Fatima me 'kashin arziki ce tafi karfin kaji koda na turai ne balle agwagi masu wuni a cikin kwata😂". "Sannan ku kalli zoben💍 daya bata na gwal ne babu wacce ta samu koda na azurfa dan haka dole yau a yabe ta itace ta cinye gasa a wannan shekarar musbahu ku bamu sauti". Kid'a🎶 da algaitu🎺 ne ke tashi kamar gidan sarki suna kuma yabon Fati da mata kirari suna kod'ata sun samu kudi sosai a gurin Al'ameen saida ya tabbatar daya wanke Fati tas daga jin kunya". Abuh na komawa gida taje ta fadawa Saude abinda ya faru tsaki Saude tai to saime inace ba saurayin nata bane idan ya tafi shikenan ta fito rana karki wani ma damu kanki". Da salon munafirci Saude taje ta karancewa mami komai harda abinda ba'ai ba saida tai 'kari. Mami kam bata juri zuga ba tuni ta cika tayi fam waya ta dauka tana danna masa kira yana dagawa tace duk inda kake kome kake kazo yanzu ina son ganin ka". Yana zuwa ta balbale shi da masifa Al'ameen kana hauka ne? Akan me zakaje ka 'barnatar da kudin ka saboda ka kare wata banzar yarinya". Tun kafin yai magana Afeeyah tace kai mami kamar ya banzar yarinya yar uwar sace fa kuma koba haka ba duk wanda ya taimaki wani Allah zai taimake shi". "Ke kuma rufe min baki bake nake tambaya ba dakai nake". "Gashinan ta fada miki mami duk wanda ya taimaki wanI Allah zai taimake shi"'. "Hummm shiyasa kaje ka zubar da ajinka a gurin yan kauye a gaban mutane sama da kirge wai yaushe ka lalace da shashanci haka ne". "Mami ki fahimta yarinyar nan sister nace fa yar uwa tace jinina ce da ita da Afeeyah duk daya ne". "A wajen ka sakarai ba wacce kuke uwa daya uba daya da wacce kuka hada kakanni saboda mutuwar zuciya kace daya suke". "Maamii gaskiya maganar sa koni Fatiman nan tana burge ni wallahi amma komai mami idan ba kece kika zabe shiba baiyi miki ba " Afeeyah ta fada da yanayin damuwa". "Ke dalla 'kyale ni yar iyawa gwana saina fadi abinda ke raina ". Mikewa Al'ameen yai yana cewa good night mami". Ya fita daga murya tai yadda zai jiyota tace kowa ya kwana lafiya shi yaso" murmushi yai yana rokon Allah daya shirya masa mahaifiyar tasa. We will meet👪 again. See👀 you next time Typing📲 +234 905 527 3614. Yusrah Musa Abubakar Gimba. Page 19 to 20. Tun asuba Saude da Abu suke gyaran agwagin nan kamar wanda suke gyaran saniya gari na wayewa Abu takai markade aka dafe su"'. Wani abin mamaki a fanteka aka zuba guda uku wai gidan me gari za'a kai haka suke yi biyun sune na budurwar . Dariya sosai Afeeyah tai ita bataga abin farin ciki dan an baka wadannan agwagin ba tunda babu riba". Kai da kafa harshi Saude ta dafe duk kayuwan ta debo a wata langar kwano me tsatsa tana kaiwa Salamatu ". Kai Salamatu ta girgiza tana cewa" a'a alhamdulillah na gode". " iheee bakin ciki kike ne Salamatu dan 'yarki bata samo ba kome"?. "Eh shi nake yi". "Aiko zaki mutu da bakin ciki domin Abu sai zaman gidan me gari su o'o kuwa bamusan inda za'a hara ba ko kuturu ko makaho waya sani". Ta fada tana dariyar mugunta tare da daukar langar kayukan ta koma dakin ta". Daddy na zaune tare da Muntari daren da ana gobe zasu koma Abuja muntari ke cewa'. "Nikam yaya inaso yara na suyi ilmi sosai amma sa idon 'kauyen nan ya hanani sakat gashi ita Zainaba har ana zancen aurenta". "Daddy yace toba tana da 'kanwa ba 'yar gidan Salamatu ko har ita za'ai auren"?. "A'a iya zainabun ce ita har yanzu bata samu tsayayye ba tukuna dai". "Ok mezai hana mu tafi da ita tunda kana so tai ilmi sai a sai mata makaranta". Muntari yace da naji dadi yaya wallahi inason dana yai karatu". "Shikenan babu damuwa ka sanar da mahaifiyarta gobe da wuri kafin mu wuce ya kamata ta sani". "Eh zan fada mata duk da nayi shedar Salamatu bata da matsala". Washe gari jin harda Fati zasu tafi yasa saude tace tab kace su Aisha zasu debi masifa yarinyar da kauye ma idonta a tsaye yake balle tana birni . Nasiha sosai Salamatu taiwa Fati duk da a ranta bata son rabuwa da yarta ta kamar yadda itama Fatin bata kaunar binsu. Da kukan ta tashiga mota suka tafi yayin da Afeeyah ke mata dariya tana cewa ayya keda dawowa sainan da shekara uku Allah sarki". Da fati iya hawaye take jin abinda Afeeyah ke cewa yasa ta soma shashsheka". Al'ameen dake driving Sadiq na kusa dashi ya joya yana cewa mene haka zan sa'ba miki ba jiya kika gama cewa she's our sister ba". Murmushi Afeeyah tai tana kallon Fati tace sorry sis ita kam Fati babu bakin magana har sukaje gida". Cikin fushi na sun taho da Fati yasa mami ta fice fuuu daga motar daddy ko kasheta baiyi ta shige cikin gida". Afeeyah kam bedroom dinta takai Fati tana cewa sannu da zuwa gidan mu ki kwantar da hankalin ki nan tamkar gidan ku ne ki dauke ni matsayin 'kawarki". Murmushin dole Fati tai tana cewa nagode". "No baki da matsala Afeeyah ta fada tana shiga toilet tayo wanka da alwala sannan ta fito tana cewa fati kema kije kiyi wanka". Shiga toilet Fati tana mamakin kyausa kamar ka kwanta a kasan tayis din sai
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25