Chapter 5
Chapter 5
magana taga yayi banza ya dauke kansa daga saitin su dole ta fita daga cikin motar tana daukar kayan ta"". Wata irinn 'kura ya buleta da ita yaba bawa motar key tari ta kamayi sosai har saida idonta yai ja". Dakyar ta samu ta daaina barin kayan tai a gurin da sauri ta shiga gidan su tana zuwa ganin ummanta a palor yasa ta fada kanta tana kuka". Cikin tashin hankali hajiya Binta tace lafiya dota daga dawowa ina murnar ganin ki sai naga kina kuka meya faru ina su Al'ameen din kosun tafi". Cikin shagwaba tace ba shinee ya ajiye ni a wajen gidan alhaji Faruq ba kuma ya tule ni da ''kura a gaban mutane dan kawai nace masa ya karaso dani gida kayan nawa ma suna can". Cikin bacin rai hajiya Binta tace kan uba amma wallahi yaron nan baida mutunnci wato ya tule miin ke da 'kura bari zan kira auty Aishan na fada mata". Kayan hajiya. Binta tasa ma'aikatan gidan suka dauko mata sai bala'i take. Ita kadai. ๐ ๐ถ By mrs Al'ameen Ahmad ce. Page 09 to 10 Kamar yadda alhaji Mustapha ya fada haka ce ta faru ranar Monday sukai shiri suka wuce london Afeeya kuma tace gidan Sadiq zata zauna gurin matarshi kafin su dawo sai kuma ta fasa ta tafi gidan kanwar mami hajiya Binta idanuwan mami a kumbure sakamakon kwanan datai tana kuka kamar ranta zai fita. Da yake Al'ameen yasan gidan kuma saboda kada a samu matsala yasa bai sanar dasu ba Saira kanwar Abni na zaune a tafkeken palon su sai ganin mutane tai cikin mamaki ta mike tana cewa bros kaine sannu da zuwa". Dan murmushi Al'ameen yai tuna rayuwar da sukai lokacin yana nan cikin yan mintuna tasa aka hada musu kayayyakin ci dana sha na alfarma". Fafur mami taki shan koda ruwa ne zama ma dan ba yadda zatai ne amma yadda take jin tsanar mutanen nan da wuta zata kone gidan sai tafi kowa farin ciki". Tambayar Saira yai ina mom domin yasan Abni da daddyn suna gurin aiki. Sauyawa fuskar Saira tai daga yar walwalar da take zuwa damuwa tace" mom na asibiti bata zama a gida". Waye baida lafiya "? Ya tambaye ta cikin faduwar gaba. Kuka ne ya kwace mata tana girgiza kai tace" Abni ce ". Wata ba'kar hajijiya ce yaji ta kwashe shi lokaci guda idonsa ya rufe luuuu ya tafi zai fadi da sauri Saira zata tare shi mami ta ture ta tana cewa. "Karki taba shi arniyar banz...... "AISHA" daddy ya fada da karfi cikin fushi yace wato kinzo gidan su ma saikin nuna rashin arziki ko kinga ki kiyaye ni ". Jijjiga mami keyi tana huci yayin da Saira taja baya daga gareta Sosai cikin jin tsoro". Da murya a nutse daddy yace" kinga Saira karki damu muje ki kaimu asibitin". Kai ta jinjina tana shiga ta shiryo tare da dauko key din motarta ta fito suka wuce". Dukda su mom suna cikin damuwar rashin lafiyar Abni din hakan bai hana su nuna matukar farin cikin su da ganin familyn Al'ameen din ba kuma sun karbe su hannu biyu". Tambayar inda take Al'ameen yai cikin damuwa mom tace " son Abni tana ICU". "Mom muje na ganta". Kai mom ta girgiza babu dama muma basa bari mu shiga balle mu ganta saidai ta na'ura". Tabe baki mami tai tana dauke kai daga kallon su domin ko ganin su bata son yi". Haka suka zauna har dare a asibtin ganin lokaci zai kure yasa mom tace Saira kuje gida ki basu masauki gobe sa dawo". "Ok mom" Saira tace sannan ta dauko su a mota suka dawo gida a ranar Al'ameen bai runtsa ba ko kadan kwana yai akan Sallaya har asuba yana rokon Allah". Kwanansu uku da zuwa iya gajiya da bacin rai mami tayi bata da buri kamar taga ta dawo gida gashi basa zance tahowa". Samun alhaji Mustapha tai ranta a hade tace waini sai yaushe zamu koma gida ne kawai munzo garin mutane mun zauna". Ko karasa kallonta alhaji Mustapha baiyi ba yace sai ranar data warke idan bazaki iya jira ba ga hanya nan". "Gaskiya bazan jira saita warke ba kamar wasu dangina tafiya zanyi saikun taho". "Ki gaida gida Allah ya kiyaye amma ki sani bada kudina zaki koma ba ki biya da naki". Zaro ido mami tai dan akwaita dason kudi kamar me tace" haba alhaji da kudi na kuma dama nice na kawo kaina". "Oh da wa ya kawo ki gurin nemawa d'anki aure kika zo". "Nidai wallahi ba ason raina nazo ba gaskiya ka biya min kudin jirgi na tafi gida". "Aisha idann kinga na biya miki kudin jurgi munyi abinda ya kawo mu muddin baza ki jira muba saidai ki biya kudin jirgi da kanki". Bakin ciki ne sosai ya mamaye mami ga koshi ga kwanan yunwa dole ta hakura dan bazata zare wadannan mmakudan kudin ta bbiya jirgi ba". Satin su guda babu wani labari don haka mom da daddyn Abni suka roki alfarma a bari su shiga su ganta ko minti biyu ne". Tare da Al'ameen suka shiga Abni na kwance akan gado ganin Al'ameen yasa tadan juyo saitin sa muryar ta can kasa tace" Al'ameen kaga halin dana tsinci kaina a ciki saboda rashin ka ko na sani ba tashi zanyi ba inai maka fatan alkairi ka kasance cikin farin ciki Allah ya baka madadi na". Kai Al'ameen ya girgiza" a'a ki daina cewa haka kece nake so Abni zaki warke muyi rayuwa tare bana fatan na raasa ki tare da mahaifa na nazo domin su karba min auren ki please Abni ki tashi muyi rayuwa me kyau". Dan lumshe ido tai tare da budewa tana kallonshi ta riko hannunshi muryarta kamar bata me jinya ba tace. "kada ka damu zaka kasance cikin farin ciki koda babu ni bazan taba rabuwa dakai ba muna tare bazan taba barin ka ba". Tari ne ya kama ta harda jini ke fita a bakin ta da sauri su mom suka yo kanta kallon su tai bata ce komai ba". Al'ameen wanda tashin hankali da rashin nutsuwa sun mamaye shi ya sake rike hannunta wani zobe ne a yatsan ta tacire shi tana baiwa Al'ameen . Ganin tai shiru yasa da karfi Al'ameen ya kira sunan ta bude ido tai tana murmushi a hankali ta furta" I LOVE YOU AL'AMEEN". Daga haka bata sake cewa komai ba sai kallon da yaga ta koma yi masa wanda bai gamsu dashi ba jin ta sake hannunsa yasa yace Abni Abni Abniiiiiiii da mugun karfi yaja sunan. Ji yai daga bayansa mom ta fashe da kuka domin shakka babu Abni ta rasu". Ganin dayai daddyn ta ya matso ya lullube ta yasa hannu zai bude rike masa hannu daddyn yai yana girgiza kai". Wanda hakan ya tabbatar masa da mutuwa tai a take ya fadi a gurin ya suma๐ข๐ญ . [23/09/05 12:44pm] Typing๐ฒ ANNURI W ASSOCIATION Home of hospitality and harmony YUSRAHMS CE๐๐. Page 11 to 12 Fitowar Afeeya kenan zata tafi makaranta Zainab tasha gabanta tana cewa ke dan rainin hankali wato ke isashshiya ko maza ki koma saikin gyara bedroom din idan ba haka ba ki hakura da zuwa
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25