Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 17

Chapter 17

Dan Millionair Book 1 Complete Hausa Novel 1,201 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

kwance a daki bacci ya fara daukarta sama-sama take jin ihu da kuka tayi zaton mafarki take sai gashi kamar ana matso mata da kukan kunnen ta. Tashi zaune tai cikin magagin bacci jin muryar zainab tana a taimake ta zata mutu yasa ta mike da sauri tana fita. Har part din zainab din ta shiga cakk ta tsaya tare da zaro ido tana dafe kirji zuciyarta na bugawa jin zainab na cewa". "Wayyo Allah na shiga uku na lalace Al'ameen zaka kashe ni na tuba kayi hakuri wayyo wayyo umma mami kuzo ku taimaka min zai illata ni ". Muryarta harta dashe kamar me mura bata fita sosai jikin Fati na shaking ta juyo har tana tuntube ta fita daga part din. Koda ta koma bedroom dinta kasa kwanciya tai balle ta runtsa saboda fargaba gani take kamar idan ya rabu da Zainab gurinta zaiyo". Zazzabi ne ya rufe ta da gari ya waye tana zaune bakin gado tana tunani Al'ameen ya shigo ganinsa yasa ta mike zumbur tana jada baya. Muryarta na karkarwa tace kayi hakuri dan Allah bani da lafiya". Bai daina binta ba harta kure bango sannan ta tsaya tana yarfa hannu kamar wacce ta yanke". Da dan mamaki a fuskarsa ya karasa inda take yana daukota ya dawo da ita bakin gadon cikin alamar tambaya yace. "Lafiya hakurin me kike bani"?. Kuka Fati ta fashe dashi tana cewa" dan Allah kar kamin abinda kaiwa Zainab". Sai sannan ya gane manufar ta murmushi yai yana rike hannuwan ta yace . "Zarahh amfanin zunubi romo babu 'kira mezai ci gawayi ita ma laifi tamin babu abinda zanyi miki ki kwantar da hankalin ki ke ta musamman ce kinfi karfin yi anan". Dan sauke ajiyar zuciya tai jin ya dora hannunsa akan fuskarta yana goge mata hawaye. Kallon cikin idonta dake cike da tsoro yai yana cewa" shikenan karki damu komai ya wuce, kinsha magani"?. Kaita daga masa". Kwantar da ita yai yana rufa mata bargo bai sake magana ba ya sakar mata kiss a saman lips dinta sannan ya fita da kallo ta bishi tana sauke ajiyar zuciya. Al'ameen ba rabuwa yai da Zainab ba saida yai mugun horata na sati tayi kuka tayi ihu ta kira agaji amma babu mai taimako tsabar azabar data sha ko tafiya ta gagare ta. Fati da ta daina ganin wulgin Zainab din yasa ta yi tunanin ko bata gidan amma data tambayi yar aiki sai tace batajin dadi tana part dinta. Breakfast ta hada a madaidaicin kyakkyawan tire ta shiga part dinta daidai ta fito daga toilet alamar wanka tayo sai bin bango take dakyar tana cije baki cikin dabara take daga kafarta. Ganin Fati tsaye yasa ta doka mata wata muguwar harara tana cewa". "Uban me ya kawo ki fita min a daki". Aje tiren Fati tai kamar baza tai magana ba sai kuma tace yaya jikin naki"?. A fusace Zainab tace jikin uwar wa munafika dama ce miki akai bani da lafiya"?. Dan murmushi Fati tai tana kallonta tace" ke kuwa kike rashin lafiya ga breakfast nan na kawo miki". "Uban breakfast malama get lost wallahi ki shiga hankalinki zan miki mugun rashin mutunci". Dariya Fati tai tana kallonta tace" ah haba dan gurgu da wacce kafar"?. Iya cika Zainab ta gama 'kulewa ji take inama zata iya kama Fati dasai ta dirzata son ranta yau din nan". Juyawa Fati tai zata fita tace to Allah ya sauwake nina wuce". "Kima tsaya da na nuna miki iyakar ki"'. "Rufe mata kofa Fati tai tana cewa idan ma na tsaya babu abinda zaki iya yi min". Page 29 to 30. Kwana biyu Zainab data samu lafiya ta warke haka ta hada kayan ta cikin akwati ta koma gidan mami da kukanta. Mami ranta ya 'baci dan haka tace Zainab tayi zamanta baza ta koma ba sai Al'ameen yazo ya bata hakuri. Shiru tun suna zuba ido har mami ta gaji ta kira shi a waya cewa yazo tana nemansa. Yana zuwa ta rufe shi da fada dakyau Al'ameen nagode da kake nuna ban isa dakai ba ina matsayin mahaifiyarka wato kana son zabin uban ka amma ka'ki nawa ko". Kamar baisan akan me take magana ba yace" mami meya faru ne". "Oh bakasan meka aikata ba kenan yanzu Al'ameen Zainab ba matar ka bace amma kai mata fayde saboda rashin hankali". "Amm mami nine tace nai mata fayde da yaushe wato dama shine dalilin tahowa gurin ki don tamin sharri"?. "Kana nufin karya ta maka"?. "Umh ban san komai ba". "Shikenan duk da haka bazata koma ba sai kazo biko". Murmushi yai yana mikewa yace to mami nizan tafi sai wata ran maybe nan da wata biyar". Da kallo ta bishi tana cewa idan ma shekara biyar zakai duk inda kaje duk shawagin da zakai a duniya karshe dai gida zaka dawo". Dakatawa yai batare daya juyo ba yace" albarkar ki da addu'ar ki nake nema dan zan dawo miki da kyakkyawar tsaraba๐Ÿ™ˆ". Jin haka yasa mami washe baki ciki farin ciki tace Allah sarki Aminu na Allah ya tsare min kai a duk inda kake sannan tsarabar kayo min me yawa saboda yan uwa๐Ÿ˜ฑ๐Ÿ˜€". , Fuskarsa har lokacin da murmushi annuri ya bayyana yace. "Karki damu mami wanda ba familin mu bama saiya ga wannan tsaraba kuma fatana tsarabar ta amfanar da al-umma"๐Ÿ˜. Sosai mami ta zage ta masa addu'a har dariya ta bashi yasan dazai fada mata manufarsa baza tace 'kala ba kila fitina cema zata tashi". Kwana biyu a tsakani Al'ameen suka bar kasar shida Fati zuwa bangkok domin zaiyi wani uziri acan tare da abokinsa Aliyu suka tafi shima da matar sa Ummul-khairi (maman Affan). Fati taji dadi tafiyar da sukai musamman da suka hadu da maman Affan mace mai kirki babu ruwanta da girman kai duk da kuwa ta girmewa Fatin". A wasu kyawawan estate masu kyau da tsaruwa suka sauka da yake sun debo gajiya sunayin wanka da sallah a daddafe fati taci abinci saboda bacci hakan ma saida Al'ameen ya matsa mata. Washe gari sakamakon ba kowa sun tafi gurin aiki yasa maman Affan ta shigo gurin Fati dan duba lafiyarta. A makeken falon ta sameta zaune tana kallon Tv ganin su yasa cikin murna ta mike tana karbar Affan dan shekara daya da rabi. Cikin fara'a ta kalli maman Affan tana cewa" sannun ku da zuwa maman Affan ga guri zauna gaskiya naji dadi". Maman Affan dake murmushi tace karki damu ai mun zama yan uwa tamkar 'kanwa haka na dauke ki". "Na gode maman Affan kuma nima na dauke kI matsayin aunty na na yarda dake zan iya fada miki dukkan matsala". Kai maman Affan ta jinjina tana cewa gaskiya Zarah kinyi dacen miji Al'ameen mutumin kirki ne na sanshi tun kafin na auri Daddyn Affan". "Amma fa saidai sojoji suna wuyar sha'ani sai kina hakuri kila auren ku baifi shekara ba ko"?. Kai Fati ta girgiza" a'a banfi wata uku bama". Zaro ido maman Affan tai tace tab kice kune a ruwa yanzu kuke cin amarcin ku honey moon kuka zo ba aiki ba". Wanne amarci ana zaune lafiya". "Amarci wanda kika sani saidai ina miki fatan Allah yasa Al'ameen ba irin daddyn Affan bane dan har yanzu ina

Table of Contents

Chapters

25 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});