Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 15

Chapter 15

Dan Millionair Book 1 Complete Hausa Novel 1,194 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

". "Haka ne mana Fati tunda gashi kin fada da bakin ki". "Ba ina nufin haka ba ki yarda dani" Fati ta fada a damuwance. "Shikenan na yarda dake". . Page 25 to 26 Sai bayan sallar isha Afeeyah ta shirya tare da Fati suka tafi kaiwa Zainab sakon magungunan da mami ta basu . A palon aunty Maryam matar uncle Nasir suka samu Zainab tana tsakiyar kawayenta sai shan kamshi take tana nuna isa". 'Dan tsaki Afeeyah tai cikin takaici ta aje mata jakar maganin babu ko magana ta juya zasu tafi Zainab ta dakatar da ita". "Ke mene haka zaki aje min, kaya babu bayani waye ya aiko ki". Ba tare da Afeeyah ta juyo ba tace I think kina da ido saiki duba bom ne a ciki". Fati dake tsaye jikin kofar falo tana jiran Afeeyah tazo su tafi tace kaya ne mami ce tasa a kawo miki"' Cikin tsawa Zainab tace ke bakauyiya na sako dake ne 'bace min da gani"'. Wata kawarta dake kusa da ita tace wannan me kamar 'kanzon fa daga ina me take anan ". Cikin harara Zainab tace na tsane ta matuka yar talakawan kauye ce mabaraciya ce jahila ba kowa ba. Juyowa Afeeyah tai tana kallonsu tace kamar yadda su o'o masu ido ba dan ciki suke yan maula talakawan birni ba ki iya bakin ki ina daidai dake sakaryar mata.".". " oh da gaske? kai amma abin yayi kyau saiki daura niyya ni roba ce ina daidai da kugun kowa". Kiran mami Zainab tai ta fada mata abinda ba'ai ba suna zuwa gida mami ta rufe su da bala'i musamman Fati da batasan tabi Afeeyan ba. Harda aibata ta da mata gori iri iri Fati saida tai kukan bakin ciki yadda mami taci mata mutunci ta zagar mata iyaye akan abinda batasan ta aikata ba. Da zazzabi me zafi sosai Al'ameen ya kwana har akai kiran sallar asuba baiyi bacci ba saida yai sallah akan sallayar baccin ya washe shi . Haka ya wuni bai fito ba a ranar yana part dinshi duk da yana ganin kamar wasa ne ba aure za'a daura masa da tabarya ba. Saida lokaci yai yaga daddy ya shigo cikin shiri tare da muntari baban fati muryarsa da alamar yana cikin matukar damuwa yace. "Daddy wai dan Allah da gaske aure za'a daura min da wannan yarinyar? zainab fa"?. "Eh Al'ameen mamin ku naso kayi fatan hakan ne mafi alkhairi a rayuwar ka". "To amma daddy bana sonta wallahi ko kadan". "Na sani hakuri shi baya 'baci tashi ka shirya muna jiran ka kuma ka cire damuwar dake ranka". Kai kawai ya iya dagawa cikin dagulewar lissafi yayin da su daddy suka fita daga bedroom din nashi. Matar mutum kabarin shi haka Al'ameen yana ji yana gani daddy ya bada sadaki aka daura masa aure da Zainab kamar ya dora hannunsa aka yayi ta kuka😭 haka yaji zuciyarsa sai tafasa take. Abokansa sai gaisawa suke suna taya shi murna basu san dawar garin ba harda masu tsokanar sa saidai yai murmushin dole". Jin an rude guri ya sake dauka yasa zuciyar Al'ameen ta tsinke zuwa wani lokaci yaji ana ambaton an sake daura auren Al'ameen Mustapha Rich da amaryarsa Fatima Zarah Mukhtar😱🙊. Wani irin zaro ido yai yana kallon daddy wanda ya rike masa hannu bayan an kammala komai ya sashi a mota suka tafi gida. Zaunar dashi daddy yai cikin bada hakurin lallasi me tafe da nasiha yace". "Aminullahi kayi hakuri da abinda ya faru bawa baya tsallake kaddarar sa matar mutum kabarinsa tunda har kaga auren nan ya yuwu karkai fushi da maminka daga Allah ne shine ya baka Zainab ba tinsasawar mami bace . sannan ina mai sake baka hakurin akan rashin neman shawarar ka ko amincewar ka na sake daura maka wani auren da yar uwarka Zarah. Kai Al'ameen ya girgiza yana cewa karka damu daddy gata kayi min na gode kuma na karbi zabinka domin ka iya zabi me kyau". "Da gaske kayi farin ciki da aura maka Zarah danai". "Kwarai daddy domin ina sonta tun kafin yanzu kuma ina son samun ka na sanar dakai dama". Murmushi me kyau dady yai cikin nuna farin cikinsa ya rika jerowa Al'ameen addu'a mai kyau. Fati na zaune a bedroom tana kwalliya Afeeyah ta shigo tana guda har saitin kunnen Fati". Toshe kunne Fati tai tana cewa au kin sauko kenan harda gud'a? a lallai abu yayi kyau". Dariya Afeeyah tai tana kallonta tace dole nayi guda na dad'a domin ke nakewa". "Ni kuma meye hadina da guda a garin dame? Zainab zakije ki yaryarawa amma kya zo ki kama gaibu". "Waye ya fada miki wallahi ke nakewa domin kin zama amarya". "kamar ya? Amarya a ina?. "A gidan yaya Al'ameen yanzun nan na shiga part din dasu hajiya inda suka sauka naji daddy yana fada mata kiyi farin ciki Fati kin samu miji me kyan hali". Gaban Fati daya yanke ya fadi zuciyarta ta sauya burgu muryarta na rawa tace dan Allah Afeeyah da gaske kike ko wasa"?. "Haba Fati wallahi babu wasa a cikin abinda na fada miki da gaske an daura muku aure yanzu ke matar Al'ameen c......... Ai bata karasa jin abinda Afeeyan zatace ba da gudu ta mike tana fita a bedroom din. Kamar an jefota haka ta shiga part din su hajiya tana kuka hajiya dake goga goro tuni ta ajiye tana cewa. "Fatima lafiya kike kuka"?. Durkusawa Fati tai a gabanta cikin kuka tace hajiya dan Allah ki taimake ni wallahi bana son auren". Hajiya dake kallonta a kaikaice tace jimin sakarya au dama dalilin kukan kenan daga daura auren ko kwana daya ba'ai ba kike neman saki kul na hane ki kada na sake jin kin furta wata magana anan ranki zai baci". Kuka sosai Fati keyi jin abinda tace zata tashi ta tafi hajiyan ta hana ta". Kamar yadda Fati tai kuka haka mami ta rika tumuwa a kasa tana kururuwa an cuci dan ta sai rirrike ta mutane keyi. 💰DAN MILLIONAIRE💰 😘YUSRAHMS ABUBAKAR Page 27 to 28. Washe gari tun asuba Al'ameen yabar gidan ya nufi lagos mami bata sani ba iya daddy ne ya sani domin yaje shiga part din yaji kukanta da alama batai bacci ba sai kawai ya juya ya fita. Satin su hajiya uku suka tafi kauyensu batare da sun samu koda kallon arziki agun mami ba. Fati kuwa sai boyewa take saboda tsananin tsoron haduwarta da mami take kamar wacce zata dau ranta. Abin yana damun Afeeyah saidai ba yadda zatai a halin yanzu mami ta sake korar yar aiki mutum daya Fati ce ke aikin mutum uku a kitchen kamar jaka gashi Afeeyah bata isa ta taya taba ko a boye ne.. Satin Al'ameen uku ya dawo ranar mami da Zainab suna zaune a palor ya shigo tsallen murna Zainab ta daka tana mikewa da gudu taje zata rungume shi ya daga mata hannu. Mami dake kallon su tace amma da wannan shashashar baturiyar ce ko ba'a daura muku aure ba zata rungume ka ko". Dan hade rai yayi daidai Fati ta fito da cooler a hannunta batare data lura dasu ba . Yace" Zarah". A firgice ta juyo ganin wanda batai tsammani ba tsaye

Table of Contents

Chapters

25 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});