Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 13

Chapter 13

Dan Millionair Book 1 Complete Hausa Novel 1,198 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

tace". Daddy dazu a gidan auty Rukayya na yanke da wuka a kitchen shine yaya Sadiq ya samin magani a gurin". Ayya sannu Zarah ku daina daukar abu me had'ari irin su wuka kuna nisa dasu kinji". "To daddy na gode" Shikenan afeeyah tashi kije ku kwanta". "To daddy good night". "Ok daughter sleep well Allah ya tashe mu lafiya". Mami ganin datai sun rage saura su biyu a palon yasa ta kalli daddy tana cewa" alhaji dama wata magana nake so muyi". "Ta me"? Daddy ya tambaya. Gyara zama mami tai tana dan yin kasa da muryarta kadan tace akan Al'ameen ya kamata ace yanzu yayi aure domin zamansa haka nan bazai yuwu ba na samo masa matar aure". "Tofa a ina take yar waye"?. "Tana gidan nan yar 'kanwata Binta nake so ya aura gatanan Zainab". "Kece kika riga masa shiga masallaci ko shine kikaga alamar yana sonta". "A'a kawai ta dace dashi ne dan Allah alhaji ka amince". "Shikenan zan same shi da safe naji daga gare shi". Cikin faduwar gaba domin tasan bazai taba amincewa ba mami tace alhaji ba wani jin ra'ayinsa umarni zamu bashi idan tashi zamu biye bazai taba aure ba kullum saidai yasa hoton wannan baturiyar a gaba yana kallo screen din wayarsa photonta ne hatta cikin laptop dinsa photonta ne akai bana tunanin yana aiki ma yadda ya kamata idan kaje bedroom dinsa photonan ta sunfi goma a bango ta riga ta shanye shi babu yarinyar da yake kallo matsayin mace balle yaji yana sonta". "Haka dai kikace kuma, haka kike gani da zato a naki tunanin zuciya bata da 'kashi muddin ya samu wacce yake so da kansa zai nuna ta". "Alhaji baka yarda ba kenan saboda kai Al'ameen duk abinda zaiyi daidai yayi a gurin ka gaskiya ni ban amince ba ka sashi yai aure". "Zaiyi idan lokacin sa yayi wannan ba wata matsala bace kada ki manta gadona yai domin kafinki nima haka naso wata mai suna Hauwa amma da ban sameta ba nace bazanyi aure ba har abada kwatsam babu zato na hadu dake dan haka shima zaiyi ki rabu dashi kada ki sake dora masa wata damuwar". Son Al'ameen ya rufe maka ido kwata-kwata baka ganin laifinsa ko"?. "A'a ba haka bane kece dai kikewa abin gurguwar fahimta ni duk yarana daya suke a gurina dan haka kibar wannan maganar lokuta da dama ina tunanin kamar kin fara gigi alhalin tsofa bai kama kiba". Ni zan wuce ki kawo min abin sha" yana fadin haka yabar gurin kamar mami zatai kuka ta mike tana bin bayansa. Bikin Abu kam ya karaso 'kememe mami tace baza taje ba daddy ko kadan bai nuna damuwa ba saboda ya kudurin aniyar indai bata jeba suna dawowa zai kara aure. Kamar tasan abinda ke ransa sai ranar tafiya tace zataje baiso haka ba amma ya rabu da ita a tari gaba. Harda Rukayya Zainab ma ta bisu wai zata gano kauyen su Fati wanne kalla ne. Ranar daurin aure sukaje kwana biyu zasuyi Rukayya kam suna sauka ta debi yaranta ita da Sadiq suka tafi gidan hajiya acan zasu zauna domin sun saba sosai. Fati da Afeeyah gari suka shiga Zainab da batasan garin bama haka ta fita yawanta ita kadai har kasuwar garin. Lokacin da suka dawo Fati ta tsaya a gurin babarta Afeeyah kuma ta shiga gurin mami cikin fada mami ta kalleta tana cewa. "Wato Afeeyah kin biyewa wannan shegiyar yarinyar ko wai kune har kasuwa wani ya sai muku nama dan ubanki saiya sa muku magani a ciki. Cikin mamaki Afeeyah tace ni kuma mami da yaushe waye ya fada miki"?. "Nice domin na ganku da idona" Zainab ta fada tana sakin murmushi tare da yimata gwalo. Takaici ne ya kama Afeeyah wato sharri Zainab ta kulla musu jin mami tace wallahi kika kara binta yawo saina ci ubanki". Yasa ranta a bace tace nifa mami ba muje kasuwa ba karya tayi min". Ita kike cewa ta miki karyar saboda baki da kunya wannan yar 'kauyen ta koya miki rashin arziki". Shiru Afeeyah tai karshe ma ta mike zata bar dakin mami tace gidan uban wa zakije ko yawon barbadancin zaki koma". Kamar Afeeyah zatai kuka tace babu inda zanje fa kawai cikin gidan zan shiga". "To cikin gidan da zaki shiga kin aje wani abu ne"?. "Gurin yan uwana zanje". "Dakyau sannu me yan uwa mu kuma daga gidan marayu muke ko? to dawo ki zauna har gobe da zamu tafi babu inda zaki sake fita" dawowa Afeeyah tai tana kwanciya akan katifa cikin tsantsar bacin rai. MRS AL'AMEEN AHMAD CE😜. Page 23 to 24. Washe gari suka koma Abuja Fati da kukanta ta shiga mota dan cewa tai baza ta bisu ba ta dawo gida kenan saboda tsangwamar mami da take sha dakyar dady ya lallameta suka tafi". Wanda suna komawa mami ta hura wutar sai daddy ya daurawa Al'ameen aure da Zainab wani lokacin har kuka take da hawaye a gaban sa. Afeeyah na zaune a palor misalin karfe bakwai da rabi na safe Fati ta fito ganin ta yasa ta tsaya tana cewa . Na dauka kina kitchen muje kada lokaci ya 'kure ". Afeeyah dake duba abu a waya tace a'a ke kadai zaki nan da kwana hudu domin ina period idan yayana yaji sai yafi kwana goma baici abinci a gidan nan ba". "Wanne yayan naki"?. "Al'ameen mana ya Sadiq yana can gidansa da matarsa me zai kawo shi yin breakfast gidan nan. 'Yar dariya Fati tai tana zama kusa da ita daidai Al'ameen ya fito batare daya kalli inda suke ba yace. "Naji abinda kika ce " yana fadin haka ya fita a palon rufe baki Afeeyah tai". Fati dake kallonta tace to kinji abinda yace" mikewa tai suka shiga kitchen din dama saboda shi ne bazata taba kayan aiki ba. Al'ameen gidan Sadiq ya wuce a dinning ya same su Amir da Aisha sai fada suke kamar kaji ga driver yana jira zai kaisu makaranta. Zama yai yana hada tea bai kalli kowa ba cikin tsokana Sadiq yace sannu matashi ziyara ka kawo mana da safen nan kenan". Al'ameen dake shan tea yace no breakfast nazo yi kawai". "Ina na gidan ku" cewar Sadiq. "Yana nan kawai na fito naji yaran nan suna zance period shiyasa bazan iya cin abincin gidan ba". "To ai nima period din nake" Rukayya ta fada cikin boye dariyarta. Aje cup din Al'ameen yai tare da sauya fuska zaiyi magana sai kuma ya fasa yana mikewa ya fice. Da kallo suka bishi Sadiq ya girgiza kai yana cewa Al'ameen na rasa wanne kalar 'kyan'kyami gareshi ace mutum bazai ci abincin me period ba saboda me"?. Dariya Rukayya tai tunda haka kawai idan yayi aure basai ya dauki yar aiki ba saiya samo namiji". "Tab Al'ameen dinne zai dau namiji dan aiki a gidansa lallai har yanzu bakisan waye shiba bari na wuce hospital kada na makara da yawa". Al'ameen na zuwa gida ya soma sheka amai kamar ba gobe karshe ma zazzabi ne ya rufe shi amma duk da haka bai fasa ba domin Lagos zasu wuce yasa kayan army dinsa kawai ya tafi". Kwana uku da faruwar haka suna zaune shida Sadiq

Table of Contents

Chapters

25 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});