Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 21

Chapter 21

Dan Millionair Book 1 Complete Hausa Novel 1,199 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

kike tambaya me kika min zaki gane kurenki yau saikin gwammace mutuwa da rayuwa". Tana zuwa palor da ita ta kifa ta tana kallon Zainab tace "me kike jira fara abinda ya kawo mu ki lakada mata dukan mutuwa". Kanta Zainab tai tana tirmishe ta da dukkan karfinta ta rufe ta da duka ta ko'ina mami na tsaye tana kallo. Dakyar Fati ta samu ta fisge da gudu ta fita daga palon yayin da suka rufa mata baya " Daidai me gadi ya budewa Al'ameen kofa ya shigo Zainab ta shake wuyan Fati'. Ko kashe motar baiyi ba ya fito Afeeyah ma dawowarta kenan taga abinda ke faruwa cikin sauri ta kira daddy da kukanta ta sanar dashi". Hankali tashe Al'ameen ya nufi inda suke yana zuwa wani gigitaccen mari ya sakarwa Zainab wanda azaba tasa da sauri ta saki wuyan Fati tana dafe kunci ta zunduma ihu. Cikin bacin rai yake kallon mami wacce ke aika masa da sakon harara yace". "Mami me kenan kika aikata haka kina kallo a gabanki wannan jakar yarinyar zatai kisa". Wani razanannan kallon 'kiyayya mami kebin Fati dashi tace" ga babbar jaka nan a gabanka mara tarbiyya ita da yake goyon bayanta kake datai nufin kasheta ta zuba mata guba cikin abinci ai baka kula ba". "Itance ta zubawa Zainab guba cikin abinci"?. "Eh ita din karya akai mata"?. Kallon Zainab yai cikin bacin rai yace" ke kuma kinyi sanadin aurenki na sake ki" sannan ya juya gurin mami datai mutuwar tsaye yace. "Kenan mami shine dalilin da yasa kika sakota a gaba tazo tadau fansa bayan bakisan komai game da hakan ba bata da lafiya yanzu da kikasa take dukanta idan ta kashe mata d'a a ciki fa"?.= " 'Da kuma kana nufin ciki ne da ita kome"? mami ta fada tana dafe kirji idonta kamar zasu fito waje Bai tanka ba sai hannu daya rikewa Fati zaibar gurin da ita kukan kura mami tai tana fisgo ta tace. "Wallahi karya ne baki isa ki haifa min jika ba yau saina 'barar da cikin nan". Duka ta sakar mata a ciki harda naushi wanda Fati ta saki 'kara tana faduwa kasa. Daidai shigowar daddy a rude Al'ameen ya durkusa yana dagota kuka Fati keyi sosai ta rike cikin ta. Al'ameen na ganin daddy ya mike da sauri ya rungume shi cikin kunar rai da radadin abinda mamin ta aikata yace. "Daddy mami ta kashe min d'ana ina son baby na amma ta raba ni dashi". Cikin nutsuwa daddy yace" Al'ameen ka saurar..... Shiru yai jin Al'ameen ya tafi luuuu zai fadi yasa yai saurin tare shi yana dago fuskarsa ganin suma yai ya cewa Afeeyah maza ta dauko masa ruwa. Da gudu Afeeyah ta shiga cikin gidan Kasa magana daddy yai tsabar tsananin fushi sai kallo me ma'anoni da yakewa mami wacce ke tsaye gefe duk ta rikice. Ruwan Afeeyah ta kawo masa ya shashshafa masa sannan ya kira Sadiq cewa ya turo motar asibiti guda daya. Harda Sadiq din aka zo ganin haka harda mami a gidan ga Zainab tana kuka yasan ba kalau ba. Sa Al'ameen sukai a mota Afeeyah kuma da Fati suka shiga motar daddy suna fita daga gidan aka bar iya mami da Zainab tsaye'. Dora hannu Zainab tai aka tana rusa kuka tace "na shiga uku shikenan mami Al'ameen ya sakeni wallahi ina sonsa". Tabe baki mami tai ke kada ki wani damu tunda kindau fansa ga kuma na kashe shege ko shegiyar yarinyar dake cikinta ai komai yayi duk wani mataki da zasu dauka aikin banza ne burina ya cika bazan ma koma gida ba yau saboda alhaji yadau fushi bansan mezai faru ba muje gurin Binta" mota suka shiga suma suka bar gidan. Sosai Sadiq ya duba Fati duk abinda ya dace ya mata kuma Alhamdulillahi babu abinda ya samu babyn. Sosai daddy da Afeeyah sukai murnar jin haka kuma suka godewa Allah. Kwanan mami uku a gidansu Zainab bata koma ba saboda tsoron haduwarta da daddy saiyau ta shirya taje asibiti gano Al'ameen. Tana shiga dakin ta ganshi a zaune fati na gefenshi wata uwar harara ta wurga mata tana cewa. "To sarkin kinibibi mahaifiyarsa tazo saiki fita ki bamu guri zanyi magana dashi kinzo kin gurbata mana zama kin zama ba'kar ashana fita nace me idanun mayu kosai kin lashe min tawa kuruwar nima kamar yadda kika lashe tasa mayya kawai". ? Mikewa Fati tai cikin takaicin maganganun da mami ke fada mata ta fita waje tana share hawaye haduwa sukai da Sadiq ganin tana kuka yace. "Zarah lafiya ina zakije ko wani abune ya samu Al'ameen din"?. Kaita girgiza" babu komai gida zan tafi". "Amma Zarah meyasa? ki bari sai dare mana". "Mami tazo itace zata wuni a wajensa". Kallon tsaf Sadiq ya mata haba shiyasa take kuka yasan da dalili. "Ok muje na kaiki to"fita sukai domin ya mayar da ita yana kuma sake bata hakuri. Page 35 to 36. Fati na palor a zaune bayan Sadiq ya ajiyeta ita kadai tai shiru ta nutsa cikin tunani da mamakin wacce irin 'kiyayya mami ke mata abin ya wuce ma hankalinta. Jin karar bude kofa yasa ta dago mami ta gani ta shigo jikinta ne ya soma rawa kamar taga hallaka. Zama mami tai tana kallonta fuska babu wasa tace" ba wata tsiyar ta kawo niba na baki minti biyu ki shiga ki tattaro kayan daud'ar ki kibar gidann nan yadda kikai silar fitar Zainab to kema ya zama haramiyarki saidai ya auro wata yasa". Hawaye suka gangarowa Fati da sauri ta goge tana juyawa ta shiga part dinta bata dade ba ta fito mami na zaune tana kad'a kafa ganin ta fito yasa ta mike tana sakata gaba da, tsinuwa suka fita harabar gidan. Karbe key din gidan tai a hannun Fati sannan taiwa driver umarni cewa. "Ga wannan bagidajiyar ta nuna maka hanyar kauyensu ka mayar da ita yau sai kwanan tabarma cikin 'kunci da zafi ba a.c sai ai ta fama da mafici daula kinyi bankwana da, ita". Tana gama fadin haka ta shige motarta ta fice daga gidan Fati na kuka ta shiga mota bangare guda tana farin cikin barin masifar mami datai. A ranar Al'ameen yabar asibitin Sadiq ne ya kaishi har gida sannan daya huta ya tafi nasa gidan. Karfe goma daidai Al'ameen yace zai tafi gidansa tari mami batai masa ba balle ta nuna masa cewa ta koreta. Tana kallonsa ya fice daga palon dariya tai tana cewa "hummm yaro man kaza ai kaida wannan shegiyar yarinyar har abada je ka dawo ina daidai dakai saika saketa". Kamar an jefo Al'ameen haka mami ta ganshi murmushi tai tana dauke kanta daga saitinsa tace "a'a me kuma ya dawo dakai"?. "Mami ina Zarah"?. "Tambaye nidai baba tunda ajiyarta ka bani". "Mami I know what u have done to my wife na roke ki daki fada min inda take me kikai mata". "Ban sani ba zo ka rufe ni da duka saina fada maka inda na kaita". "Dan Allah mami mubar wannan maganar ina key din gida na"?. cikin gadara mami dake zaune tasa glass da laptop gabanta tana aiki tace". "Wanne gida kake dashi daya wuce nan ai daga yau ka dawo gidan ku da

Table of Contents

Chapters

25 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});