Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 2

Chapter 2

Dan Millionair Book 1 Complete Hausa Novel 1,196 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

taba domin marar abu baya zuciya sannan ta mike da kanta ta gyara dinning din da komai tana komawa bangaren ma'aikata ranta duk ba dadi ta gaji da wulakancin da mami ke mata". Koda dare lokacin da daddy ya dawo haka mami ta cika ta kumbura tai fam taki sakin ranta akan lamarin dazu". Kallonta alhaji Mustapha yai cikin mamaki domin da ba haka take ba yace" uwar gida ran gida ya akai ne naga kina fushi meya faru". Kamar jira mami take ta ture plate din abincin gabanta tana cewa nida Al'ameen ne mana yana neman dora min hawan jini ya kashe ni lokaci na baiyi ba". "Tofa meya miki haka auta na akwai hakuri kodai kece da tsokana"?. "Kaji irin abin ko babu dama a fadi laifinsa a gaban ka saika wanke shi tas ". "Ba wannan ba fada min meyai miki". "Ranta a hade tace wai dan Allah kaji shi da wani hauka yaje wata kasar ya hadu da yar arna ta kaishi church sun burkita masa kwakwalwa ya dawo ya susuce". "Subahanallahi da yaushe wani abu kika ga yana yi wanda ya saba hankali"?. "Yo meye ma baiyi ba alhaji dazun nan na gama cin kaniyarsa akanta ala dole ita yake son aura duk Nigeria baiga wacce tai masa ba saiya debo mana masifa da bala'i sun zuge mana jini". "Gaskiya ka sameshi ka masa fada tunda ni na gaza yaki fahimta ta". "Ok yayi shikenan karki damu uwar gidan Mustapha Aminu zan same shi as you wish kamar yadda kike so". Murmushi mami tai cikin farin ciki yauwa alhaji yanzu naji magana nina manta sunan shegiyar yarinyar ma sunan kalar amai"😣. Ki daina rage mata alhakin data deba a cocin tunda kince kirista ce". Allah wallahi abin ne da haushi duk gayun sa da tsananin kudin ka maimakon ya nemi yar shugaban kasa nasan duk inda yaje neman aure da gudu za'a bashi". Kai alhaji Mustapha ya jinjina yana mamakin mami daga anyi magana saidai ta ambaci kudi💰😂. BY MRS AL'AMEEN AHMAD CE. 💰'DAN MILLIONAIRE💰 #Comment #✅ote #Fallow. 💫ANNURI WRITER'S ASSOCIATION💫 Home of hospitality and harmony. Yusrahms Abubakar Mrs Al'ameen Ahmad ce. Page 03 to 04. Sati biyu da faruwar haka Al'ameen na zaune shi kadai a palor yaji wayarsa na kara wakar da Abni ta dora masa ce tun a London . Yana kallon screen din wayar saida gabansa yai mummunar faduwa ganin sunan Abni din baro-baro. Bai daga ba saida ta katse ya kira ta amma abin mamaki data daga saiya kasa ce mata komai kawai yai shiru yana sauraronta". Jin yayi shiru yasa tace dear lafiya kwana da yawa wayar ka a rufe kasan irin tashin hankalin dana shiga kuwa please kada ka sake". Sauke ajiyar zuciya yai muryarsa kamar yana mura yace fatan kina lafiya ina mom da saira ko kina ma'aikata ne kamar naji hayaniya". Dariya tai domin tana da yawan fara'a tace a'a kawai dai zan baka mamaki ne". "Kamar ya wanne iri"?. "Idan nace maka ina kasarka Nigeria zaka yarda ". Zuciyarsa na harbawa sosai kamar zata fito waje yace zan yarda amma da gaske kike kina Nigeria"?. Allah dear ina nan Abujan ku ba nan kace state naku ba na rako daddy na ne wani aiki baifi sati zamuyi ba". "Ok you are welcome". "Thank dear amma yanzu ina ne zan same ka domin na sanar da dad dina zamu zo gidan ku"?. A firgice da karfin gaske har saida ya tsora ta yace "what you mean........ "Yes ta katseshi batare daya karasa ba tace ka sanar dani addresss din gidan ku". Babu yadda ya iya dole ya tura mata kamar yadda ta bukata tare da dafe kansa cikin damuwar mezai iya faruwa". Fitowar mami kenan ganin a yadda yake yasa ta fasa wucewa ta tsaya tana cewa "lafiya meye ya faru na ganka a haka kodai wannan banzar yarinyar kad'anin kake tunani da wahalar da kanka a kant.......... Bata karasa ba taji anyi sallama da wata irin murya da ba hausa ba kanaji kasan yare ce". Juyawa mami tai ganin mace tsaye bakin palor fara tar jawur baturiya yasa cikin kaduwa tace" wace ke ya akai me kike nema anan din"?. Dan murmushi tai idonta nakan Al'ameen da shima ita yake kallo tace "barka da gida mah suna na Abni Jonah daga London nazo gurin dear ne" ta fada tana nuna Al'ameen. Wata irin zabura mami tai tana jefar da glass cup din hannunta ya fadi ya tarwatse idonta kamar zasu fito waje dan razana tace". "Me Abni Jonah wato kece wannnan matsiciyar yarinyar da kika lashe kurwar dana ko baya ganin ko wacce mace saike shine yanzu kika biyo shi har kasar sa ki cinye shi ko mayya "?. "Kallon Al'ameen Abni tai tana tambayarsa akan me mahaifiyarsa take cewa". Kafin yai wani yunkuri mami tace ubanki nace tsinanniya la'ananniya harda me nace da yake ya zama sako tumaki saiya fada miki jaka kawai". Cikin takaici Al'ameen yace wai mami me kikeyi haka haba dan Allah ki daina zagin ta ". Bazan daina ba kazo ka dake ni saboda na zagi wannan shedaniyar arniyar". Mami ki daina kafurta ta musulmace fa"?. "Au a haka shine ta sako wannan dan mitsitsin hijab din kila ma wanda take zuwa coci ne". Fahimtar da Abni tai kamar bata samu karbuwa agurin mami ba ganin yadda take magana da fada duk da batasan me take cewa ba yasa ta kalli Al'ameen ba tare da nuna wata damuwa ba tace" suje waje ko gardan suyi magana". A tsawace mami tace idan ka fita ka bita ban yafe maka ba saina tsine maka wallahi,". Iya rudewa yayi cikin yanayin ladabi Abni ta roki mami cewa ta kyale suyi magana amma mami tace ya fita ya gani". Dafe kansa Al'ameen yai jin lokacin guda yayi mugun sara masa da hanzari Abni ta karasa tana tambayarsa lafiya"?. Wata hankada mami ta mata wanda saida ta buge da kujera cikin tsawa tace fice daga nan idan ba gidan ubanki bane bakadaddiya karuwa wato a gaban nawa ma fayde zaki masa"😨😱. Abni zatai magana mami ta sakar mata wani zazzafan marin dayasa ba shiri ta fita a palon da gudu tana kuka". Al'ameen dake numfashi dakyar muryarsa na rawa yace mami me kika aikata kin aibata kin zage ta kin mare ta me tai miki dan Allah mami meyasa kika tsani Abni ni kuma baki tsane niba domin nine ita itace ni kowa ya kita ya kini". "Ai kai yanzu na fahimci mahaukaci ne bakasan ciwon kanka ba idan ba mayya bace kalli mana kafin tazo kana irin wannan numfashin ne shashasha ana maka gata da yake idonka ya rufe baka gani". Barin gurin tai yayin da Al'ameen yake yunkurin tashi yabi bayan Abni ya kasa. Abni na zuwa hotel inda suka sauka ita da dad dinta tasha wani marin a gurinsa yana huci yace dole soyayya dashi kina neman kashe kanki ga samarin ki can ki zabi daya mana Abni ina kika kai tunanin ki,"?. Kuka Abni ta fashe dashi tana rungume mahaifin nata tace kayi hakuri dad Al'ameen na sona kada ka raba mu nima ina sonsa ba laifinsa bane". Cikin tausayawa daddyn ta ya rungume ta shima yana cewa shikenan naji yi

Table of Contents

Chapters

25 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});