Chapter 1
Chapter 1
[23/06/05, 12:30pm] Yusrah Musa Abubakar📝 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊 💰'DAN MILLIONAIRE💰 ('Dan miloniya) WHATAPP NO: 📱+2349055273614 YUSRAH MUSA ABUBAKAR Mrs Al'ameen Ahmad ce. (*)(SHORT STORY)(*) 📚 LITTATTAFAI NA 👑Yarima Abdul-maleek 🌹Rayuwa biyu 🍇Safreeyyah 🎉Haskena sauban 🎀 Mina-Umer 🌷Karuwar boye 💰'Dan millionaira. Ga me bukatarsu ya tuntube ni ta wannan number👉 09055273614 littattafai na free book ne ga duk wani masoyi na a duk inda yake afadin duniya I love u with all my body and heart💞. 💫ANNURI WRITER'S ASSOCIATION💫 🏡 home of hospitality and 🕊harmony. In the of Allah the most benefits and the most merciful we love our nabeey s a w we like him and peace be upon him ameen🙏👏. Some say hello some say hay but in islamically said assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatihu. Tofa reader's na kumin afuwa wannan karon son kai zan nuna sosai first page na yan group dina ne Annuri ina alfahari dasu may Allah help them any where they are amin. Page 01 to 02 Wani irin 'kayataccen ginannen gida ne wanda hatta fetin gidan gwal aka nike akai fetin dashi da safe ne amma ko'ina 'kyal'kyali ne ke fita a jikin bangon gidan da dare kuwa har dauke ido yake . Tsararran palor ne dankarere daya sha kayan alatu na more rayuwa iri daban daban wanda wani abin ma na'ura ce ke sarrafa aikin sa ba mutum ba. Zaune suke su uku samari ne guda biyu fitattatu na ajin farko yan gayu tsaf dasu kyawawa farare tar dasu kamar larabawa sai mace a tsakiyar su wacce kallo daya zakai mata kasan itace mahaifiyar wadannan zukakan samarin. Amma kana ganin fiskokin su kasan akawai matsala domin a samarin wanda yafi hasken ransa a mugun bace yake kallo daya zakai masa ka fahimci haka . Saidai bacin ran bai hana kyansa bayyana ba da kuma annurin fuska. Cikin fad'a matar ta kalleshi tana cewa "kasan Allah Al'ameen ka fita idona na rufe idan banda shashanci me zakai da wannan banzar yarinyar wacce ba yaren kaba ba jinsin kaba 'kabila tubabbiya yar wata kasar ba zaka je ka yayo min masifa ba duk yan matar kasar ka da jihar ka saika haura wata uwa London to bari kaji bada yawu na ba ban amince ba kuma ko bayan raina ka aure ta ban yafe maka ba sai ka zaba koni ko ita". Cikin tsananin firgici da tashin hankali wanda ta kira da Al'ameen ya dago kyawawan idonsa yana kallon mahaifiyar tasa jin furucin da take akan wacce bazai iya hada sonta da kowacce mace ba bayajin zai samu madadinta. Iya kallon da yake mata ya tabbatar mata da cewa Abni ce numfashin sa bazai iya rayuwa ba tare da ita ba wanda hakan yai matukar firgita ta. Cikin 'kunar rai ta mike bata sake cewa komai ba jin yawun bakin ta ya kame yasa da sauri tabar gurin zuciyarta na turiri da zafin al'amarin yaron nata wanda ta damu dashi . Dafa shi dayan yayi cikin tausaya masa da halin daya tsinci kanshi na jarabtar soyayya yace "Al'ameen dan Allah kayi hakuri da halin mami tunda bata son wannan baturiyar ka daina furta koda sunanta ne a gaban ta domin mami idan ta fadi magana bata sauyawa kaifi daya ce nasan baza ta taba bari ka aure ta ba". A damuwance Al'ameen ya dago yana kallon dan uwan nashi yace" ni da kaina na fada mata cewa babu kyau karya alkawari a addinin musulunci saboda ni tabar nata addinin ta musulunta bata yarda tayi imani ba saida na mata alkawarin zan aure ta sakamakon nima ina sonta yanzu me kake tunanin zata dauke ni idan nace tayi hakuri na fasa auren ta wanne irin hali zata shiga dan Allah ka taimaka min". Kai Sadiq ya jinjina shikenan 'kani na zan taimake ka insha Allahu tamkar ka auri Abni ne domin bana son rasa ka kuma na fahimci itace bugun zuciyar ka". Wata karamar yarinya ce tazo da gudu tana kuka ta fada jikin Al'ameen cikin rashin walwala yace" momy na me akai miki"?. Da yatsa yarinyar ke nuna wajen dinning tana cewa he spoiled my shirt". Kallon farar rigar ta ta yai ganin duk miya ya bata ta yasa ya kalli wajen dinning din wani yaro ne tsaye rike da spoon a hannunshi karasowa gurin yai yana cewa small dad ban sani ba na shafa mata miya a jikin rigar ta sorry sister". Kafada ta make wallahi bazan hakura ba saika biya ni riga ta kona rama". Zare mata ido yaron yai yana cewa baki isa ba tunda na baki hakura kuma bazan wanke rigar ba ". Kuka ta kara fashewa dashi cikin lallashi dason raba rigimar hayaniyar da suke Al'ameen yace" muje na sai miki wata momy na rabu dashi". Goge hawayen fuskarta tai tana dariya suka fita daga palon yayin da Sadiq shima ya mike yana cewa Ameer meye abin bata ran kaga kada kayi kuka muje kaima na saya maka". Tsalle Ameer yai yana rungume Sadiq yace thnk dady " rike hannunsa yai suka fita wanda mami najin kara tashin motoci yasa taja tsaki cikin takaici tana bude window ta daga labule tana kallon su har suka fice daga gidan". Sauke numfashi tai tana cewa amma wallahi Al'ameen sam bashi da hankali ina yabar ajin nasa wata shegiya take neman mayar min dashi shashasha duk yabi ya susuce akanta ko yar uban waye ita a London nata isa ta rabe muba duk kudin su saita raba su kota halin 'ka'ka. Fita tai daga nata part din tana shiga wata kofa ta bude bedroom tare da lekawa tace" wato Afeeyah baki da hankali ko sai ulcer ta kama ki zaki gane gata ake miki tsabar iskanci kisa waya agaba ki manta da komai bari dadyn naku ya dawo zansa ya karbe wayar ne". Cikin shagwaba wata budurwa dake kwance a wani makeken gado ta dago tare da cewa kai mami bafa wani abu nake ba kuma indai breakfast ne nayi tun karfe bakwai". "Hum haka ne da gaske kinyi"?. Eh mami nida wafer na karya ba abinci naci ba". "To yayi miki kyau ki fito haka zama ni daya a palon ya ishe ni". Shikenan to muje mami yadda kika ce haka za'ai mikewa tai suka fito tare yayin da mami ta danna wani karaurawa dake palon". Da sauri wasu masu kaya iri daya su biyar suka shigo palon cikin ladabi jikin su na rawa suka durkusa tare da gaishe da ita bata amsa ba sai wani kallo datai musu tana cewa. "A cikin ku wadanne banzayen ne masu lura da dinning mikewa hajar tai tana cewa mune nida ma'u ". A tsawace mami tace sannu yayan talakawa wato daula tasa zaku fara shagala da abinda ya kawo ku uban waye ya zubar da miya akan farin carpet din can"?. Zaro ido hajar tai wallahi hajiya ban sani ba tunda mukai servingg dinku ban sake fitowa ba". "Saboda gaki isashshiya ko ke nana baki karanta musu ka'idojin gidan nan bane domin ba irin kowanne gida da suka sani bane sai wane da wane". Nana dake shirin magana mami ta katse ta rufa min baki nan gaba aka sake samun kuskure daga wadannan 'kazaman new comer bazan daga miki kafa ba". Hakuri nana ta
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25