Chapter 12
Chapter 12
ko karasa kallonta bazai ba". Zainab datai suman zaune muryar ta na rawa saboda bakin ciki abinda yace yanzu tace. "Amma gani ka rasa wa zakasa ta hada maka breakfast sai wannan kucakar 'kazama yar kauye"'. Itace ta cancanta nasa domin tafi ki matsayi kucaka 'kazama kece sunan kine dake hakan ya dace". A fusace ta mike tana nufar kitchen din tarar da fati tai tana kokarin kunna gas ta buge mata hannu tana huci tace. "Ke dalla matsa min jaka ". "Jaka dai" Fati ta maimaita. Cikin karaji tace eh nace jaka dabba jahila kibar kitchen dinnan domin Al'ameen nawa ne nice zan aure shi dan haka ki fita daga gona ta ko kallonsa na sake gani kinyi saina faffasa miki ido". Dariya Fati tai Allah da gaske amma sai naga wanda kike wahalar da kan naki a kansa bakya gabansa son maso wani kike". "Inji uban wa" zainab ta fada tana yowa kan Fati". Cikin dakewa Fati tace inji uban ki ke bari kiji bafa ki isa ki shiga tsakani na da dan uwana ba indai akan ala'kar mune bakin ciki zaisa zuciyarki ta buga dare daya ki mutu Al'ameen baya sonki". Wuka Zainab ta dauko tana kawo wa Fati wani irin wawan yanka gocewa Fatin tai a bisa tsautsayi ta yanke ta a hannu". Rike gurin da jinin ke fita Fati tai tana dagowa zatai magana zainab ta dauke ta da mari. Itama Zainab din babu zato taji zazzafan marin ya sauka a kuncinta wanda a gigice ta fasa kara". Tana kallon Al'ameen basu ankara ba suka sake jin karar mari mami ce ta shigo daidai Al'ameen ya mari zainab shine itama ta mari fati dan tasan a kanta ne". "Mami" Al'ameen yace ransa a bace. A fusace ta juyo gurinsa tana cewa rufa min baki wanda baisan ciwon kansa ba akan wannan tsinanniyar yarinyar shine zaka fidda hannu ka mareta". Cikin tsawa mami ta kalli Fati da hawaye ke fita daga idonta tace ke kuma yau saikin bar gidan man tunda ke shedaniya ce kinzo kin hana mu zaman lafiya ". "Mami ina zataje da zakice yau saita bar gidan ba laifin ta bane nawa ne". "Sakaran banza dama ai nasan laifin kane basai ka fada ba". "Ke kuma kafin naci uban daya haifeki kije ki tattare tsunmokaran ki ya mayar dake. Fita Fati tai tana zubar da 'kwallar bakin cikin zagin da mami tai mata ita daman hanyar garinsu take neman komawa". Cikin mamaki shigowar Afeeyah kenan ganinta janye da akwati yasa tace lafiya ina zuwa haka". "Nice na kore ta domin hatsabibiya ce". "Kika koreta kuma mami ina zataje kenan"?. "Ruga zata koma can gayyar tsiya kauyen su". "Haba mami me kike cewa haka dan Allah kiyi hakuri". "Wallahi tunda na rantse saita bar gidan nan a yau bazan yi kaffara ba". Al'ameen dake tsaye yace Zarah⭐ muje". Mami dake hararar Fati tace ka manta baka ce wata🌙 ba". Daidai zasu fita yayi murmushi yana cewa to ai nine watan mami munyi ruga". "As as as ta kaji idan kaga dama kaima karka dawo ka zauna acan". Kuka Afeeyah ta fashe dashi tana shigewa part dinta mami data bita da kallo tace zaki kuka ki gaji har hawayen ki ya kare kora ce na kore ta kuma babu yadda za'ai dani"'. Bintu Musa Abubakar. Page 21 to 22. Gidan Sadiq Al'ameen yakai Fati cikin mamaki Sadiq yace ina fatiman zataje na ganta harda akwati ga fuskarka da damuwa lafiya"?. Kai Al'ameen ya girgiza yana kallon Sadiq yace" zata cigaba da zama anan". "Me yasa"?. "Saboda wani dalili" Rukayya ya kalla yana cewa" please auty na ga sister na zata taya ki zama". Murmushi Rukayya tai ok babu damuwa 'kani na sannunki da zuwa Zarah ko". "Eh sunan ta kenan "Al'ameen ya fada yana zama a dinning . To ai bakai na tambaya ba ". "Idan kin tambayeta tamkar kinyi da nine". Cikin tsokana Rukayya tace a'a fa Al'ameen kodai-kodai". Aje cup din daya hada tea yai yana cewa kodai kodai me. Da ido Rukayya ta nuna masa kodai son fati yake". Kafada ya daga yana cewa kibar ma wannan tunanin sam ba haka bane nida soyayya munyi ban kwana balle wani aure". "Humm yadda kake dinnan inaga mace daya ma ta maka kadan saidai biyu". Ni biyu ma sun min kadan saidai hudu". "Aiko zamu duba cikin dangi mu zabo maka". "Ba wannan maganar bana ra'ayin aure a cikin dangi idan ma zanyi gara bare". Mukam munfi so ka samu a dangi zanyi ta maka addu'a". Bana bukatar auren dangi Idan abinda kika fada ya faru zan baku kyautar visa kuje honeymoon duk kasar da kuke so". Rukayya tace tab aiko zan dage har fata na yaci kuma wallahi saika yi alkawarin daka dauka". Bai amsa mata ba sai mikewa dayai yana kallon Sadiq sannan ya kalli hannun fati yace please kadan duba ta taji ciwo da wuka a hannunta. Yana fadin haka ya fita dan bayason yawan tambayoyi da kallo Sadiq ya bishi tareda girgiza kai kafin ya fara duba mata hannun. Al'ameen bai koma gida ba sai dare daddy daya dawo ya tarar da Afeeyah idonta sunyi ja kuma sun kumbura ya tsareta da tambayoyi. Kasa fada masa cewa mami ce ta kore ta tai yayin da mami tai wi'ki-wi'ki tana rarraba ido alamar rashin gaskiya da kad'uwa. Mami daddy ya kalla yana cewa ina fatima Zarah take"?. Hautsinawa cikin mami yai ta rasa abin cewa sai kallon daddyn da take da tsoron idan yasan ta koreta kila itama yau tai kwanan gidan. Da fari Al'ameen yayi burus ya dauke kai kamar baya falon sai da yaga ran daddy yai masifar baci sannan ya gyara musu al'amarin da cewa. "Amm daddy Zarah tana gidan Sadiq taje musu wuni ne yanzu zanje na daukota". "Ok babu damuwa ai tunda tana can dama rashin ganinta ne yasa hankali na ya tashi". Mikewa Al'ameen yai yana fita a palon daddy dake kallon mami wacce tun dazu take susa kamar me ciwon 'kazuwa ko sabuwar kamu yace. "Dama tana gidan Sadiq amma kika barni nai ta ihu da baki na"?. Sauke ajiyar zuciya mami tai tana godewa Allah da yasa Al'ameen ba garin su ya mayar da ita ba tace". "To ai alhaji nayi tunanin zakai fada ne kace nabar bakuwa kuma budurwa tana yawo". "Akan me zanyi fada dan taje gidan dan uwanta ai zumunci tai yarinyar nada hankali". Kallon Afeeyah dake goge sauran hawayen fuskarta jin fatin na gidan Sadiq yai yana cewa". "Me akai miki ke kuma kike kuka gashi idanuwanki harsun kumbura. Sauke kai Afeeyah tai tana cewa daddy banda lafiya ciki na ke ciwo". "Kuma baki daa lafiya bazaki fada a kaiki asibiti ba kuka yana magani ne"?. "Daddy nasha magani tun dazu na samu sauki"'. "Shikenan Allah ya rufa asiri". "Amin tace". Daidai fati tayi sallama tana zama ta gaishe da daddy". Amsawa yai yana kallon bandejin hannunta yace ciwo kika ji Zarah da yaushe"?. Kafin fati tai magana Afeeyah tace daddy dazu ne a kitchen Zaina......... Dafe kirji mami tai tana tarin karya harda shidewa saboda kada Afeeyah ta fada". Ruwa Al'ameen ya miko mata karba tai tana sha kamar gaske fati data fahimci mamin bataso daddy yasan gaskiya
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25