Chapter 16
Chapter 16
bayanta ya bude mata hannuwa alamar tazo gare shi yasa a rude ta nemi hanyar guduwa. Rikota yai batare da kawaici ko jin kunyar mami ba ya rungume ta tare da cewa I miss u fatan kina lafiya". Zaro ido tai jikinta na rawa dago fuskarta yai yana sakar mata kyakkyawan kiss me dumi a lips din ta sannan ya saketa. Tana jinta free ta ruga da gudu tana shigewa part dinsu mami da haushi ya gama cikata tace kayi asara dai wallahi ka rako maza duniya meye abin so a jikin wannan yarinyar "?. Bai bawa mami amsa ba sai Zainab daya kalla yana cewa kinga yadda tarbiyya take ya kamata ki koya nine na kirata amma neman guduwa take saboda kunya ke kuma saboda sakarci kin wani taho a guje zaki rungume ni kada ki kuskura ki sake ko a mafarki ne". Yana fadin haka ya wuce kuka Zainab tasa tana zama a gurin yayin da mami bakin ciki ya hana tace komai. Ganin ya dawo yasa ta fara shirye shirye a raka Zainab gidansa taro ta sake kira sosai na dangin ta Zainab taci wanka sukai mata rakiya". Fati kam daddy ne da kansa shida Afeeyah suka je gidan ya sake zaunar da ita ya mata nasiha sosai sannan suka taho. Al'ameen na zaune a palor idonsa a rufe yaji an shafa fuskarsa yana bude ido yaga Zainab zaune kusa dashi ta manne masa bai kula taba ya mayar da idonsa ya rufe. Cikin shagwaba tace wai Al'ameen me yasa ka fiya tauri kamar dutse ne ka sani nice matar ka wacce na dace dakai wannan bakauyiyar bata da wani amfani yar aikin muce kawai". Ganin bai kula taba yasa taci gaba Al'ameen yaufa ranar farin ciki ce a gare mu daren mune zamu raya shi please ka tashi" ta karasa maganar tana kwantar da kanta a kafadarsa. Tun tana jiran tashinsa har bacci ya dauke bai motsa ba sai wajen sha biyu ya barta a gurin ya mike yana shiga bedroom dinsa Fati kam tunda su Afeeyah suka tafi ta kwanta tana kuka daga nan bacci ya dauke ta. Washe gari da wuri ta tafi makaranta domin daddy ya bata driver Zainab kam tana palor inda Al'ameen ya barta tana sheka bacci". Lokacin data farka rana tayi sha biyu da rabi kallon palon take yi cikin takaici tare da jan tsaki kamar zatai kuka cikin masifa ta soma magana. "Amma wallahi Al'ameen yayi mugun raina min hankali wato anan ya barni na kwana ji yadda jikina yake min ciwo dan yaga ina sonsa shine zai wulakanta ni kome"?. Mikewa tai tabar palon bata daina maganganu ba tana shiga bedroom ta kira mami da kukan ta tafada mata karya son ranta. Wanda Al'ameen na zuwa maimaakon mami ta karbe shi da fara'a daya gaida ita bata amsa ba sai hade rai datai tana jefa masa tambaya. "Dakyau Al'ameen ka kyauta wato dama baiwa nakai maka ko yanzu kai a ganin ka kayi daidai kenan"?. "Ka kulle kofar bedroom kace Zainab bataje dashi daga gidan uban taba sai a palor ta kwana ". "Da safe ka watsa mata ruwan fridge mai sanyi wai hutu dama taje gidan ka prisoner dinka ne babu maganar yar aiki hatta wankin motar ka itace zatai saboda dama abinda ya dace da ita kenan". "Humm lallai kam ina ita wannan dod'addiyar jahilar yar kauyen meye take a gidan dama aiki ne ya dace da ita". "Wato ka fifita sashin mahaifinka da zabinsa akan na mahaifiyar ka ko"?. Mamaki ne sosai ya kama Al'ameen jin sharrin da Zainab ta 'kuga masa alhali tunda aka kaita magana bata hada su dashi ba". Jin mami tace dakai fa nake tunanin me kake? Wato saboda ka mata gargadin karta fada min shine ka kasa ban, amsa ko"?. Kallon ta yake kamar sa na sauyawa zuwa yanayi na fushi yace wai mami ita Zainab dince tace na fada mata haka"?. "Eh ko kana son kace tai maka karya ne da kukanta ta kira ni dazu". "Ok shikenan zan tafi ki huta lafiya mami". "Ina zakaje baka bani amsa ba "?. "Ina zuwa mami dole sai mun zauna dan bazan dauki rainin yarinyar nan ba". Tun kafin mami tai magana ya fita a palor ransa a bace. Zainab na palor zaune tana danne danne a waya kamar walkiya haka ta ganshi cikin palon sakamakon tasan karyar data shirga masa yasa da sauri ta mike zata gudu". Wata irin damka ya mata wanda cikin azabar radadin da hannunta ke mata ta kwalla kara tana sakin wayarta". Muryarsa kausashe yace" ki tsaya iya matsayin ki idan tsautsayi yasa kika sake kuskuren fada wa mami abinda bansan dashi ba saina kusa kashe ki wawuya". Kuka ta saki domin rikon dayai mata bana wasa bane hannunta yayi jawur ya tara jini yafi awa rike da ita saida ya tabbatar ta wahala ya saketa cikin bacin rai yabar gurin. Kuka tai sosai domin hannunta ya kumbura amma a ranta yanzu ta fara indai bakanta masa ne a cewarta tunda ya nuna baya sonta". Hanyoyi da dama ta soma bi na jan hankali amma kullum labarin daya ne ta gaji da zama haka amma tasa a ranta zata fito ta masa zanga-zanga. Wata daya dayin bikin nasu amma babu abinda ya sauya kullum itace a 'kar. Tana tsaye da bayan sallar magriba a gaban dinning bayan yar aiki ta gama dinner ya shigo a gajiye sosai yanayinsa zai fada maka haka. Tararsa tai tana kashe murya tace" sannu my hero gaskiya yau ka gaji da yawa Al'ameen muje na maka tausa da wanka ga dinner na jiranka". Ta gefen ta ya wuce yana cewa bana bukata". Tsaki taja mai karfi wanda ya dakatar da tafiyar da yake yi ganin ya tsaya a dake tace". "Ahaf dan ina tausaya maka ma shine zaka nemi tozarta ni karka manta ba wani abin arziki kake bani ba ". "Karka manta akwai gwarazan maza a gabanka soja suna kawai kaci domin baka da wani amfani gurin mace saidai ka kalle ta da ido". "Tunda kai famkon namiji ne babu wani katabus da kake dashi kai muna maza sunan ka mata maza domin babu wani abu da zakai tunkaho dashi famko kawai". Wata irin juyowa yai da dukkan karfinsa wanda tasa ta kwasa da gudu ta shige part dinta . "Famkon namiji"? Ya fada cikin mamaki wato kallon da take min kenan lallai zan nuna miki iyakar rashin kunyar ki" juyawa yai yana shiga part dinsa. Misalin karfe tara na dare Zainab na kwance akan gado taji an bamko mata kofa da karfi cikin tsoro ta zabura tana mikewa ta diro daga kan gadon. Ganin wanda batai zato ba yasa ta sake rudewa ga wani yanayi da tsantar fushi da take hangowa a cikin idanun shi. Jikin tane ya soma rawa ta kankame guri daya cikin tashin hankalin meya kawo shi. Har inda take yaje yana sa hannu a gaban rigar baccinta da dukkan karfinsa ya yaga ta. Yana mata wani kallo me ma'anoni da nuna ta shirya famko ya kawo mata ziyara". Tana kokarin guduwa ya cafko ta yana dora ta akan bed din ya bita ya danne domin yayi alkawari yau saita gane bata da wayo. Fati na
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25