Chapter 8
Chapter 8
ruwanki koma wa yake so tunda kina da naki". "Kefa Fatin nan gidan yake so". A zabure Saude tace me karya ne akan hakan kike kuka". "Wallahi ba karya bane yanzu na wuce su suna waje akan dakali suna hira". "Kan bala'i wato Salamatu dan me gari kika yiwa asiri ko aiko sai kowa yaji a garin nan kina zuwa gidan boka bari gari ya waye tabdijan wallahi da sake dan kinga bikin shekara ya kusa kada yarki tasha kunya agaban dunbin jama'a na gari da gari". Tari dabai kama Salamatu ba bataiwa Saude ba ta tura mata aniyarta domin batasan ma wani Sa'adu nason Fati ba". Kasa nutswa Saude tai saida ta sayar da akuyarta ta dangana gurin boka akan ya karkatar da hankalin Sa'adu kan Abu ". Yaji ya tsani Fati haka ta juyewa boka dukkan kudin sisi bai bari ta dawo dashi gida ba amma fa ya mata aiki domin tun a ranar labari ya sauya akala". Da dare sai akace Abuh tace inji Sa'adu wata irin faduwa gaban Salamatu yai cikin tashin hankali ta kalli fati dake kallon Abu". Dariya Saude keyi tana juyi da habaice habaice tace dadi na da gobe saurin zuwa maza Abuh shirya kije kada ki bata masa lokaci tsuntsun soyayyar🕊 ya dawo kanki ahayye ayyuriri nanaye nisa tazo kusa". Kallon Fati Salamatu tai cikin tausayawa tace kada ki damu Allah yasa haka ne mafi allhairi kinji babu komai kai Fati ta daga cikin damuwa sosai amma batace komai ba"'. Tashin hankali ne karara ya bayyana da kiyayyar 'kauye🏕 a fuskar mami lokacin da daddy yace mata ta shirya yana son zai gano danginsa". Cikin cika da batsewa tace amma alhaji mezai hana kaje kai kadai". "Saboda me" ya tambaye ta cikin mamaki. Kai tsaye tace" dole sai munyi gayya me zamu ciyo"?. A garin daya tare dukkan zuriya ta kike cewa me zaki ciyo Aisha tun ba yau ba na fahimci bakya kaunar zuwa dangi na saboda a kauye suke amma ki sani sune komai nawa idan kika 'kisu nine kika 'ki fito fili kice mustapha bana sonka basai kinbi ta bayan gida ba". Zaro ido mami tai ni da yaushe nace bana sonka"?. "Yanzun nan kika fada tunda bakya bukatar asalina kinga son karya kike min yaudara ta kikeyi". Kuka mami ta kama yanzu alhaji shedar da zakai min kenan"?. Mikewa daddy yai ransa a hade yace na fada miki ki shirya idan kuma baki canza halayen kiba zan dau mataki a kanki". Yana fita tace na shiga uku ni Aisha wannan tsinannan 'kauyen kuma zanje daga wannan masifar takau sai wannan😢. Humm mami manya 'kauye🏘 tushe da asalin kowa😘 duk wanda bashi da 'kauye to bashi da asali😠 tsintaccen kan hanya ne🙄. Washe gari motoci biyu suka dauka yayin da Zainab tace baza ta bisu kauye ba ta wuce gidan su kafin su dawo". Da matukar murna Muntari ya tari yayan nasa nan aka hau yi musu hidima da bajinta duk wani abu dazai burge su na gargajiya". Afeeya dake shan fura ganin mami tayi gurum yasa tace wai mami bazaki ci komai ba to kisha wannan akwai dadi". Cikin bacin rai mami tace zanci 'kaniyarki fa Afeeyah ni abokiyar wasan kice"?. "Yi hakuri mami " daga haka bata sake magana ba". Sadiq kam dama ya shiga gari idan yazo baya zama guri daya kamar kifi🐟". Al'ameen da yake suna tare da daddy a dakin muntari yace dad nifa yunwa nake ji". "Kuma Aminullahi ga abinci iri daban daban sai wanda kake so". "No daddy ba irin wannan nake so ba". "Uhmm wato sai kwai ko wannan abincin yafi wanda kake ci a birni sa lafiya da gina jiki". "Nidai daddy mubar maganar samo min mafita Allah ina jin yunwa sosai". Daddy dake kallon shi yace to Aminullahi hanya mafi sauki ga yaji da mai nan a kusa dakai dauki ka cinye ni amma ka fara ta 'kafofi na saboda kar na gudu😂😝". Dariya wacce babu shiri Al'ameen yai yana kallon daddy yace haba dad idan na cinye ka babu wanda ya kaini asara". Muntari dake gefe yace to yanzu me kake so a dafa maka". "Am small dad in son samu ne dan wake". "Shikenan karka damu bari yanzu zansa ayi maka" mikewa yai yana fita". Al'ameen dake kallon photon Abni dake screen wayarsa yace daddy bari naje gurin grand-mah". "Ok yayi ka gaishe ta" Al'ameen na fita daidai Fati ta shigo da bokitin ruwa a kanta tana cewa wash Allah umma ki sauke ni". Da sauri Salamatu ta fito daga daki tana cewa meyasa kika ciko". "Umma bana son na koma ne". Zama Salamatu tai tana hada kayan wanke wanke Fati tace barshi zanyi umma ki huta". To Allah ya miki albarka". "Ameen umma motar waye guda biyu a kofar gidan nan masu kyau". "Ayya Fatima yan uwan kine suka zo daga birni da yayan babanki Mustapha yana dakin baban ku kije ki gaishe shi". "To umma " fati tace tare daa mikewa kusa gwaruwa tai da al'ameen da sauri taja baya tana cewa yi hakura dan Allah ban ganka ba sannu da zuwa ". "Thank" yace daga haka bai sake magana ba yai hanyar waje cikin mamaki ya tuna yarinyar nan kamar ba ita yake dauka a hannu ya sayo mata chocolate ba shakka babu amma girmanta ya gani sai yaga ta cika masa ido. Yana zuwa gidan ya tarar da Sadiq acan da ido ya masa magana cikin tsokana Sadiq yace . "Lah hajiya kinsan me Al'ameen yace wai ya yaga kin kara tsufa sosai kin ragargaje kiji fa hajiya kamar wata kwarya". "Rabu dashi Saddiqu lokaci ne shima wata rana zai taka wannan matsayin". "Matsala ta dake hajiya bata suna meye zakice Saddiqu just kice Sadiq". "Bazan ce jas Saddiq dinba karka dameni😂😜". Al'ameen ta kalla tana cewa zauna mana Aminu kana tsaye kamar wata bishiya". Zama Al'ameen yai cikin hade rai yace ba suna na Aminu ba Al'ameen nake". Hajiya dake kallonsa domin yana kama da kakansa wato mijinta tace. "Bazance Alemin din ba da Aminu zan kira ka ya zakai ubanka Aminu ya rada maka a haka suka sha minti da goro da naman suna". "Nidai na fada miki suna na Al'ameen"' "To kinji hajiya ni Sadiq shi Al'ameen sai ki gyara". "Bazan gyara ba duk wanda na kira karya amsa ". Kallon Al'ameen tai tana cewa" Aminu ya batun aure naji har yanzu shiru"'. "Babu ruwan ki in zanyi in bazan yiba wannan ganin dama tane". "Karya kake sai kayi d'an kare da fari kamar........... Sai kuma tai shiru bata karasa ba murmushi Al'ameen yai dan ya gane nufin ta yace. "Karasa man da fari kamar wa zaki ce kuma kin manta ba d'an kare zaki ce ba saidai kice dan kwikwiyo🐩😂. Dariya Sadiq yai yana kallon hajiya yace hajiya kinji fa saidai kice d'an kwikwiyo ba d'an kare ba". Da sanda hajiya ta nuna shi tana cewa kai kuma kayi man shiru bansan shishshigi zuwa dangin miji da ganamasgo ka rufe min baki". Dan zaro ido Sadiq yai ciki tsokana yace na rufe ruf🤐 hajiya me ran karfe ki shirya idan zamu koma dake zamu tafi kiga birni ki huta kiyi 'kiba". "Ni ka rufa min asiri da zuwa birni
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25