Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 19

Chapter 19

Dan Millionair Book 1 Complete Hausa Novel 1,198 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

komai". "Babu komai kika zubawa guri daya ido waima na tambaye kI kinyi amfani da wannan abin kwalbar dana baki"?. Kai Fati ta girgiza tace a'a maman Affan ina jin tsoro a haka ma yaya nake karewa wallahi kina da gaskiya maman Affan ba kuka ba yar karamar mutuwa ma sai kayi". Dariya maman Affan tai tana kallonta tace" yayi kyau kina jina babu wani cutarwa game da wannan magani ki jarraba nina fada miki saikin tambaye ni inda ake saidawa". "To shikenan maman Affan zan gwada na gode". "Karki samu damuwa ke yar uwa tace". Dan kasa tai da murya tana mata rad'a su Haidar da suka karaso ya kalli maman Affan yana cewa" wacce gulman ake gutsira mata". Dagowa maman Affan tai da murmushi a fuskarta tace sirri ne tsakanin mu". "Yayi sarkin za'ki lokaci yayi". ganin sun gama aikin ga magriba ta rufa yasa suma suka mike suna fita daga waje mota daya suka hau suka nufi gida . Kamar yadda maman Affan ta bata shawara tare da karfafa mata gwiwa haka tayi bayan tai wanka ta shafe dukkan jikinta dashi. Aikam dai ranar taji sauyi sosai kuma taji dadi round biyu yai da dare da asuba ma haka amma bataji ta kosa ba. Shi kanshi yaji canji kuma yayi mamakin ta ko lokacin da suka kasance a palor tare tana kwance a jikinsa yace. "Zarah kinban mamaki kodai har na mayar dake jarumar ne fada min mene sirrin jiya naji kin dage sosai kin karbi gayyata ta"?. Rufe ido Fati tai cikin kunya tana rike hannunsa tace babu komai". "Babu komai amma kika sani na zauce"?. "Nidai babu komai ka yarda". "Na yarda amma fa naga wani abu cikin kwalba kuma kamshin iri daya ne da kamshin jikin ki"?. "To ai maman Affan ce ta bani". "Oh na canka daidai kenan? Please yau ma kisa ina so". Adan tsorace ta kalleshi gira ya dauke yana cewa" yes yauma zamu kasance tare har asuba babu maganan bacci". "Kai nidai bazan iya ba". "Bazaki iyaba kin taba ganin wanda kake so kayi nisa dashi"?. Kallon mamaki ta mishi har tana tsayar da idonta cikin nashi tace" so"?. "Eh so" ya bata amsa. "To amma son wa". Rike fuskarta yai yana dora lips dinsa saman nata ya bata burkitaccen kiss me dumi wanda yasa ta dauke numfashi yace. "son wa kuwa Zarah ki gode wa Allah domin kin maye min gurbin Abni a zuciya ta ina sonki". Rungume shi Fati tai tana kuka tace" Allah ya mata rahma amma kafi karfin yin soyayya dani". "Waye ya fada miki kece kika dace dani duk duniya bani da tamkar ki kina da babban matsayi a zuciya ta tun kafin na fahimci cewa sonki nake". "But do u luv me". Kara kankame shi tai cikin farin ciki har yana jin sautin murmushinta akan idonsa beauty point din ya lotsa tace. "Nima ina sonka son gaske bana hada ka da kowa kaike da mukullin zuciya ta fatana mu kasance tare har abada". "Zamu kasance tare Zarah kece numfashi". Dagowa tai tana kallonsa ranta fari tas zuciyarta cike dajin dadi fuskarta da annuri. Zatai magana ya katseta da cewa" muje ina son mu ganaπŸ™ˆ". Fuska ta shagwabe tana komawa kalar tausayi tace" Allah nina gaji kafa na ciwo take". "Wanda kake so baka gajiya dashi Zarah dan haka muje na cewa mami zan koma mata da tsaraba kinga dole na dage". Yana fadin haka ya dauketa yana barin palon cikin rad'a ya mata magana a kunne wacce tasa da sauri ta kifa fuskarta a kirjinshi tana dariya kasa kasa. πŸ‘‰ Mrs Al'ameen Ahmad ce. 🌼🌹🌼🌹🌼🌹🌼🌹🌼🌹🌼🌹 Page 32 to 32. Kamar yadda Al'ameen yace wa mami saida suka shafe tsawon wata takwas harda sati biyu a bangkok saidai sunje london ziyara gurin iyayen Abni". Wanda suka samu kyakkyawar tarba kamar su maida su ciki haka suke nuna musu kauna da basu kulawa har ranar da zasu dawo Nigeria. A ranar da suka dawo mami ta sako Zainab gaba da akwatinta ta rakota tayi sa'a ta samu Al'ameen a gida haka ta balbale shi da masifa kamar zata rufeshi da duka. Sannan ta juya kan Fati dake gefe tai mata zagi na tsamar nama harda kakannu saida suka samu rabonsu. Fati tayi kuka tayi bakin ciki batasan me taiwa mami ba da bata kaunarta sam". Kwanan su goma da dawowa Fati tana part dinta a kwance bata da lafiya Zainab dake palor zaune tana jiran yar aiki ta gama gyara dinning tabar gurin. Da sauri ta mike tana waige-waige ta nufi dinnig din tare da bude cooler ta fara zuba wani abu. Al'ameen na tsaye a bakin kofar palon yana kallonta saida ta juya zata tafi ta ganshi cikin razana da rashin gaskiya tace. "Harka dawo sannu muje kai wanka ga abinci na jiranka da kaina na shiga kitchen na shirya maka shi". Karasowa yai har inda take yana rike hannunta ya mayar da ita gurin dinning din yace. "Me kika zuba a ciki". muryarta na rawa tace mezan zuba kawai gyara murfin coolan nai saboda karta huce. Bude wa yai tare dasa mata spoon a cikin abincin ransa a hade sosai yace. "Eat". Zaro ido tai jikin na kakkarwa ta soma jada baya ganin tana shirin guduwa yasa ya cafko ta yana matseta sosai a jikinsa ya debo abincin ya danna mata da karfe dole saida ta hadiye. Ihu ta kurma domin tasan guba ta zuba a ciki bai damu ba ya sake deba ya cusa mata saida ya bata spoon biyar sannan ya ture ta daga jikinsa yana mikewa ya barta a gurin. Da sauri ta mike tana shiga part dinta ta wuce toilet ta fara amai cikin galabaita ta fito dakyar ta iya lalibo number mami ta kirata tana kuka". Mami na dagawa Zainab tace mami please karna mutu kizo ki kaini asibiti yanz........... Bata karasa tari ya rufe ta sakin wayar tai tana durkusawa a gurin. Mami dake cewa hello zainab kina jina meke damunki ina Al'ameen din"?. Jin shiru ba amsa yasa mami kallon wayar ganin ta katse a firgice ta sa'bi mayafi tana fita taiwa driver magana cikin gaggawa ta shiga mota suka tafi. Lokacin da mami ta samu Zainab cikin mugun hali kwance farin abu na fita a bakinta. Salati mami keyi ta dagota da sauri amma tai luuu ta koma ihu mami tai tana kuka ta ciccibe ta suka fita". Saka ta a mota tai suka wuce asibitin Sadiq domin ya dubata Sadiq yayi mamaki abinda ya gani tattare da Zainab din. Wanda bayan ya fito daga dakin da aka kwantar da ita ya koma office dinshi inda mami ke zaune tana jiransa. Ganin ya shigo da sauri ta mike tana tambayarsa "Abbakar yaya jikin nata meke damubta"?. Zama yai cikin nazari yasan Fati bazata zuba mata guba ba balle Al'ameen shine abinda yake bashi mamaki toshi yanzu mezai cewa Mami na damun Zainab?. Katse masa tunanin da yake mami tai da fadin "Sadiq ka bani amsa mana, ko wani abune ya sameta"?. Kai Sadiq ya girgiza yana cewa "a'a ki kwantar da hankalinki na mata aiki zata samu lafiya da yardar Allah saidai ban gama binciken abinda ke damunta ba". "To amma Sadiq wannan farin abun dake

Table of Contents

Chapters

25 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});