Chapter 3
Chapter 3
shiru haka na gama komai a cikin kwana biyu saboda ke gobe zamu tafi". Zaro ido tai tana mikewa tsaye zatai magana ya girgiza mata kai yana cewa". "Bazan barki ki sake komawa wannan gidan ba kada ki batawa kanki lokaci Abni auren ki da yaron nan bamai yuwuwa bane". A rude tace dad zai yuwu dan Allah ka kara min lokaci zanji da komai"'. "Na sake baki lokaci amma wannan shine na karshe idan aka sake samun matsala bazan daga miki kafa ba". Murmushi tai eh dad thank you na yarda". 🌹 Mrs Al'ameen Ahmad ce. Yma Dutse new world🌎 new life🌲 and new style💈 sabuwar duniya🏙. NAJA'AT MUSA ABUBAKAR ZARAH MUSA 'DAN ADAN THIS PAGE IS FOR U I LV💝 U EVERYTHING ABOUT YOU IS SO GOOD BUT ONE THING IS WRONG THAT YOU ARE NOT MIND. Page 05 to 06 Wani karamin kauye wanda yake cike da mutane iri daban daban wani gida ne daya sha fenti harta waje kamar yana cikin gari gidan yayi kyau sosai kana gani kasan me gidan nada abin hannu a kauyen. Wata mace ce ta fito daga daki tana rawa tayi daurin kwalin soke irin ture kaga tsiyarnan tace. "Ahayye nanaye yan gidan nan ku fito kuyi kallo Zainabu abu na me 'kashin arziki ce ba irin su o'o da ba'a da farcen susa ba". Jin shiru yasa tace Salamatu kina ina ne kodai bakin ciki ya kashe ki a daki lallai kina da aiki ". Fitowa wata farar mata tayi daga wani guri da hayaki ke fita wanda kana gani kasan dakin girki ne ta kalli waccan dake rike da atamfa tana cewa". "Akan me zanyi bakin ciki saboda Zainab ta samu atamfa kowa ai da nasa rabon Allah ne ya bata". Dariya Saude tai tana tafi tace tofa masu tawakkali kamar gaske kina magana a salihance nan kuwa zuciyar bakin kirin take"". Murmushi Salamatu tai an fada miki kowa irin ki ne ni abin wani bai dame niba Fatima bata rasa kaya ba". "Humm karyar banza kayan gida ba badan ubansu meyin suturar bane idan ta samari za a biye wata rana saidai ta fita yawo tsirara". Salamatu dake shirin komawa kitchen tace Allah ya kiyaye kedai tunda kinbi son zuciya ki taka a sannu ina gargadin ki". Kugu saude ta rike jimin munafikar mata koke kika samu duniya yarki tai farin jini haka sai kinci kudin samari". Sallama wata budurwa tai tana sauke fantekar dake kanta tace gaskiya nifa na gaji da wannan tallar ehe "'. Baki saude ta bude ke baki da hankali yi kasa da muryar ki kada salamatu taji tai min dariya dama yanzu ita da shegiyar yarta suka gama kukan bakin cikin atamfar da ilya ya kawo miki ". Dariya Abu tai lallai ahe bakin ciki zai kahe su dan wallahi yace saniyarsa ta haihu idan ina dan zai bani". Da sauri kamar wani zai rigata Saude tace kice kina so dan ubansa tunda bashi da hankali ki wanki gara😂. "Ai dama taliyar murjin da kika dafa min yau shi kadai ya saye ta". Zaro ido saude tai sadaka yayi a dandalin". Baki Abu ta tabe a'a kawai yaji da manjan ya juye a cikin fantekar ya cinye shi kadai sai yar kadan daya bawa wani almajiri🙊😹. Saude tace kaji jakin mutum wannan kada ayi auren ya kasa rike ki mahaukaci ne shi zai cinye taliyar rabin kwano da kofin wake". Hade rai Abu tai nifa ina sonsa ki daina zagin sa yace min gobe zai turo iyayensa". Cikin murna Saude ta rafka guda tana cewa abin yazo yar albarka ta kusa tafiya daki bari muntarin ya shigo muyi magana". Mikewa Abu tai tana cewa nifa yunwa nake ji saude dake kirga makudan kudin da ilya ya baiwa Abun tace ki buda daki yana nan a langa". Kai Salamatu ta girgiza tana daga kitchen tana tuka tuwo tace Allah ya shirye ku kada wata rana kuci kudin matsafi". Kwanan Al'ameen goma baida lafiya gashi yana so ya koma gurin aikin sa amma babu dama dole ya hakura zuwa wani lokaci idan yaji ya dawo daidai". Daddy na zaune kusa da Al'ameen bayan Sadiq ya duba shi ya daura masa ledar ruwa cikin lallami yace. "Aminullahi meke damun ka Sadiq yace min har yanzu bugun zuciyar ka bai dawo daidai yadda yake ba ka fada min matsalarka". Sauke ajiyar zuciya Al'ameen yai domin maganar dazai fada ba lallai daddyn nasu ya amince ba yace. "Dan girman Allah daddy ka dube ni da idanun rahma ka tausayawa zuciya ta ka fahimcr cewa danka ya fada cikin jarabtar soyayya kamin maganin damuwa ta". "Me kenan zanyi maka Al'ameen ka fada min kada kaji shakka niba mami bane babu abinda zai gagara". "Daddy na roke ka ka duba Allah ka amince min na auri Abni yarinyar nan ta sadaukar da rayuwar ta saboda na samu farin ciki ta kula dani lokacin da bansan kowa ba a London. Ta musulunta saboda ni ta yarda zata aure ni ta zauna dani sannan mahaifanta basu nuna min kiyayya kamar yadda mami ta tsane taba. Da tazo gidan nan ta rako mahaifin ta mami ta zage ta ta aibata ta ta kafurta ta sannan ta mare ta amma batai zuciya dani ba saboda tana sona". Cikin mamaki daddy yace ita Aishan ce ta mare ta ". "Eh daddy wai tazo har gida zata cinye ni". Murmushi daddy yai kuma an fada mata mayun 'kiri da 'kiri suke kama mutum su cinye shi yanzu dai me za'ai". "Daddy abin da za'ai shine zan aure ta ina sonta da ita zan zauna dan Allah daddy ka fahimce ni itace komai nawa banajin zan samu madadin ta". "Ok yanzu kana so aje nemar maka auren tane "?. Eh daddy wannan shine damuwa ta ka taimaka min". Hannunsa daddy ya rike karka damu zan yi kokari akan hakan zamuje london cikin satin nan domin kudi ba sune kwanciyar hankali ba". Tashi zaune Al'ameen yai ba shiri yana cewa a satin nan na gode daddy Allah ya kara daukaka". "Amin daddy yace yana kallon yadda lokaci guda fuskar Al'ameen din ta washe da farin ciki". Lokacin da mami taji wannan maganar kuka ta fashe dashi na bakin ciki tana cewa yanzu alhaji tsakani da Allah aura masa arniya zakai karya fa take bata sallah". "Shine damuwar ki"?. Shiru mami tai tana goge idanunta da sukai jawur saboda kiyayyar Abni. Ganin taki magana daddy yaci gaba inda rashin sallah shine matsalar me sauki ne zata musulunta tunda tana sonshi kuma ba haramun bane danya aure ta". "Dan haka ranar monday jibi kenan ki shiri za muje london nema masa auren ta kiyi fatan itace alkairi a rayuwarsa". Hannu mami ta dora akai tana sake zunduma wani ihun cikin burgima tace wallahi bada yawu naba kuma ko kofar gate bazanje ba balle naje wata london gurin shegun arna naje su bawa gunki jini, na". "Bazai auro min wata baturiya ba saidai ya mutu baiyi aure ba". "Aishaa" daddy ya fada a tsawace tare da nuna ta da yatsa yace. "Idan ke bakya sonsa ni ina sonsa kuma na amince ya auri wannan baturiyar tunda itace zabun ransa kece zaki zauna masa da yan mata da kike kawo masa"?. "Shashancin
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25