Chapter 14
Chapter 14
a palor ranar weekend cikin tsarguwa Sadiq ya kalli Al'ameen yana cewa". "Wai kai na tambaye ka mana murmushin me kake tun dazu"?. "Babu murmushin jin dadi ne kawai saboda na fahimta na gane wata gaskiya". "Gaskiya ta me kenan". "I am in love". Zaro ido Sadiq yai cikin mamakin furucin Al'ameen din jin zancen nasa kamar mafarki yace. "Da gaske kake ka samu wacce kake so"? Lallai zanso ganin yarinyar me sa'a data sace min zuciyar dan uwa na wacece ita a ina take ka sanar dani"?. "Ok zan fada maka amma ba yau ba saboda tsaro ita din tauraruwa ce me haske zuciya ta saida ita ina sonta so me tsanani ma". Sadiq da dadi ya gama cika shi cikin farin ciki yace mene sunan ta"?. Dan shiru Al'ameen yai kamar me tunani sai kuma yai murmushi yana kallon sadiq yace Zarah "' "Zarah yar waye" Sadiq ya tambaya. Al'ameen yace no zaka santa ba yanzu ba tana da daukar hankal........... Bai karasa ya dakata tare da kafe guri daya da ido muryarsa cikin wani yanayi yace" Zarah no one but you, I love u with all my body and heart bana iya hada ki da kowa". Kallon inda yake kallo Sadiq yai wanda har saida yadan zabura yana dafe Al'ameen cikin mamaki yace" wai dama Fati na nan gidan kake nufi"?'. "Eh ita bansan ya akai ko kuma yaushe bane haka nan rana daya na tashi naji na kamu da ciwon sonta kuma zan aureta ina da ra'ayin zama da ita zuciyata ta Abni ce amma yanzu ta Zarah ce . "Wow gaskiya na taya ka murna ka kuma yi dacen mace idan har ka aureta domin tana da tarbiyya. "Haka ne kyawawan dabi'unta ne suka rinjaye ni amma alfarmar da nake nema a gurin ka shine ya zama sirri tsakanin mu kada kowa ya sani". Murmushi Sadiq yai cikin tsokana yace babu wanda zan fadawa masoyi zasu sani da kansu". Bayan watanni uku Al'ameen na zaune a gaban su mami yana sauraron kiran da sukai masa'. Daddy yace" wato Aminullahi dama batu ne akan aure ka samu wacce kake sone"?. Kai Al'ameen ya girgiza a'a daddy babu". "To maminka ce tace ya kamata a hada ku aure kai da Zainab shin me kake gani hakan yayi maka". Caraf mami tace wanne irin yayi masa bashi zamu biye ba . Daddy da hankalinsa ke kan yanayin da Al'ameen ya shiga yace bake na tambaya ba saiya yarda idan bai amince ba dole abar batun". Kuka mami ta saka tana cewa shikenan nikam na kade na gama yawo alhaji meyasa kake min haka ne. Hade rai daddy yai yana cewa Al'ameen tashi kaje kada ka damu Allah ya baka wacce kake so ta maye maka gurbin waccan. "Amin daddy na gode" Al'ameen ya fada cikin jin dadi yana mikewa ya fita. Mami dake goge hawaye tace yanzu alhaji haka ak......'. Katseta daddy yai saurara Aisha bansan shashanci mubar maganar shiru mami tai tana sauke ajiyar zuciya takaici ya gama cika ta. Yau da gobe tafi karfin wasa daddy ya gaji da nacin mami ta hana shi sakat tabi ta hargitsa kanta ta hargitsa gidan saida ya amincewa abinda take so. Suna zaune Zainab ta fito cikin shiri zata fita tana kallonsu babu gaisuwa sa'kam-sa'kam tazo zata wuce. Cikin tsawa mami tace ke gidan ubanwa zakije da yammar nan. Dan tabe baki Zainab tai tana cewa bikin kawata ake zanje mata gurin event data gayyace. Mikewa tsaye mami tai koma ciki babu inda zakije". Zaro ido Zainab tai tana cewa tabdijan kinsan yadda muke da ita kuwa. Mami tace dan ubanki ni kike cewa tabdijan ina matsayin yayar mahaifiyarki zaki iya fadawa Binta. Zainab dake kad'a key din mota tace sosai ma saidai idan batai min abinda zance matan bane kinga ni kina bata min lokaci na wuce dan banga me hana ni naje ba . Tana fadin haka ta bude kofar palor ta fita tana wa'ka mami data bita da kallo tace jimin shegiyar yarinya zaki dawo ki same ni ne". Wani irin kallo daddy ya mata wato wannan yarinyar take son aurawa dansa yarinya mara tarbiyya amma bari ya kyaleta tayi gaban kanta babu ruwansa. Batare da Al'ameen ya sani ba domin bayanan aka karba masa auren Zainab a gurin mahaifinta ranar mami kamar ta zuba ruwa a 'kas tasha dan farin cikin har ta 'kagu lokacin biki yayi ta ganta tare da Al'ameen muradinta. Afeeyah kam iya damuwa tayi saidai ba yadda zatai har daddy ta samu da kukanta amma yace tayi hakuri matar mutum kabarinsa komai me wucewa ne. Al'ameen yasan da zancen domin Afeeyah ta kira shi a waya ta fada masa amma yai burus kamar abin bai dame shiba saidai bazai taba kallonta matsayin mata ba. Biki ya matso ya kankama sai shiri akeyi mutari ma da tawagarsa sukayo mota guda harda hajiya ranar farin ciki a gurin Fati ganin mahaifiyarta. Suna zaune a bangaren baki sai kalle-kalle suke mami tasa nana ta kai musu abinci da abin sha me kyau wanda basu taba ganin irin saba. Shigowa mami su gaisa da yake a cikin farin ciki take saita saki fuskarta har tana tambayarsu. "Sannun ku da zuwa hajiya fatan kunzo lafiya akace tun asuba kuka taho amma baku zo da wuri ba. Saude data yago cinyar kaza tace" wallahi nake fada miki da wuri muka taho 'yan ro santi ne suka tare mu". "Ro santi kuma"? Mami ta fada cikin rashin fahimta. Saude tace eh wallahi sune suka tare mu sunaiwa driven mu rashin arziki". Dariya Afeeyah tai sosai tana cewa wai yan road safety kike nufi"?. Mami tace" oh sune yan ro santi"? Gaskiya ne bari na dawo" ta fada tana mikewa domin zama dasu ya isheta . A ranar su Afeeyah suka je aka tsara musu lalle ita da Fati sunyi kyau sosai duk da basa tare da walwalar wacce ake neman cusawa Al'ameen din aurenta. Da yamma wajen magriba suna kitchen mami ta shigo dawowar ta kenan daga gidan hajiya Binta 'kanwar ta ganin basa part dinsu yasa tayo kitchen. Juyowa Fati tai jin motsi a bayansu ganin mami yasa tace sannu mami ina yini"?. Dan kallonta mami tai a yankwane kamar baza ta amsa ba cikin basarwa tace lafiya kune za ayi wa sannu". Kallonta ta mayar wajen Afeeyah wacce ke ta aikinta kamar batasan da zuwanta ba tace" Afeeyah idan kun gama kI sameni a part dina zan aike ki gidan uncle dinki Nasiru ki kaiwa Zainab wasu kaya tana can". Cikin kunar rai Afeeyah tace to mami". Juyawa mami tai tana fita a kitchen din sannan ta leko tana cewa" ke kuma ki shirya kayanki domin ranar da 'kyauyawa zasu koma tare zaku tafi aje can aci gaba da bikin agwagi kinji na fada miki" tafiyarta tai babu abinda ya dameta. Afeeyah data gama kulewa da lamarin mami tace wallahi bazan bari haka ta faru ba dole na fadawa daddy bari ya dawo gidan". Kai Fati ta girgiza a'a Afeeyah karki haka bana bukatar ace ta sanadiya ta mami da daddy sun samu matsala ki kyale kawai ni kaina nafi son na koma garin mu". "Meyasa saboda bakya bukatar zama damu ko"?. "A'a ba haka bane
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25