Chapter 24
Chapter 24
kunna hasken dakin yace " Aisha". Bude ido mami tai ganin dady tsaye yasa ta tashi zaune tana jingina bayanta da fuskar gadon. Cikin alamar tambaya daddy yace "baki da lafiya"?. Muryar mami na rawa cike da damuwa da tsananin kishi tace "alhaji da gaske ne abinda kunnuwa na sukaji dazu da safe aure zaka kara"?. Kallonta daddy keyi haba yasan zafin kishin mami a kansa tun kafin ya aureta". Mami da zuciyarta tai mata nauyi tace "alhaji kaban lokaci na gyara kuskure na idan kayo aure a wannan halin da muke ciki komai cakude min zaiyi dan Allah karka min kishiya". "Aisha wai waye ya fada miki aure zan karo Al'ameen tsokanarki kawai yake amma ni banida ra'ayin zama da mata biyu karki damu komai ya wuce". Sauke ajiyar zuciya mami tai tana cewa "amma sai naci 'kaniyar Al'ameen wato kakarsa ya mayar dani🙄". "A'a karki taba min auta na babu ruwanki dashi idan ba haka ba muhau sama mu fad'o". Dariya mami tai tana cewa "shikenan tunda abin son kaine". Dan shiru tai kamar mai tunani zuwa can tace "alhaji gobe zanje garin ku". Da mamaki sosai a fuskarsa yace" wai kina nufin kauye na"?. "Eh ina son na gyara mu'amala ta da kowa sannan yarinyar nan Fatima nadau hakkinta zan bata hakuri kuma na taho da ita ta dawo dakin mijinta ta haihu". "Dakyau Aisha kin kyauta kuma naji dadi na gode idan kinje da kwana biyu zamu biyo bayanki". Kai mami ta jinjina tace "ina son atamfofi da kayan abinci na tafi dasu". "Ok yayi zansa a kawo miki komai da kike bukata". Page 41 to 42. Washe gari haka mami tai sammako kamar kasar zata bari dan zumudi ba daddy ba hatta su Afeeyah mamaki ne ya kamasu. Lokaci da mami taje Fati ta fara nema amma bata gidan taje wuni gidan kakannin ta na uwa. Data dawo Salamatu ta sanar da ita mami na nemanta mamaki ne ya kamata amma tai burus bataje ba domin babu abinda zatai mata ko tace mata. Kwanan mami biyu tana bin Fati tazo zasui magana amma harsu daddy suka zo garin Fati bata yarda sun hadu ba". Gidan hajiya ma ta koma da zama gabadaya saboda bata son ganin mami. Da kuka mami ta fadawa daddy Fati ta'ki sauraronta kwantar mata da hankali yai ta hanyar cewa zata hakura saita huce. Su Sadiq na gidan hajiya sai jikin magriba Al'ameen da Fati suka fito saidai shima taki warewa ta masa magana wai tunda tazo gida bai biyo bayanta ba. Ta danyi tafiya mai nisa ta waiga ta gano shi acan baya saitin dabar samarin anguwarsu yayi kneel down, komawa tai tana cewa "ka taso mana mutane fa suna kallon mu". Komawa kalar tausayi yai yana miko mata hannu yace "bazan tashi ba saikin daga ni da kanki". Zaro ido tai tana kallon yadda mutane suka zuro musu ido tace ",nidai ka tashi kona tafi". "Allah Zarah bazan tashi ba saidai ki daga ni". Ganin an kira sallah idan ta biyeshi zasu 'bata lokaci yasa dole ta mika masa hannu rikewa yai yana murmushi ya mike tsaya yana manna mata kiss yace. "I love u my wife". Kunya ce ta kamata tana kokarin zamewa daga jikinsa yaki sakinta ya rike mata hannu ya fara tafiya da ita dole ta bishi har cikin gidansu bai saketa ba saida yaji muryar ummanta. Bayan sallar isha daddy yai kiran Fati dasu salamatu ya musu bayanin komai ya kuma basu hakuri. Mami harda kukanta ta rike hannun Fati tana bata hakuri da mata magiya abinda bata taba yiba". Saboda daddy da kuma Al'ameen yasa tilas Fati tai hakuri ta yafe mata jin daddy yace idan zasu tafi tare da Fati zasu wuce ta koma dakin mijinta. Mikewa Fati tai tana kuka ta fita haduwa sukai da Al'ameen ganin tana kuka yasa ya riketa yana yin bangaren muntari baban su da ita. Har daki yana goge mata hawayen yace "meke damunki"?. Kaita girgiza tana cewa babu komai". "Amma kike kuka? fada min damuwarki". Ganin ya zauna yasa tace "ka zauna akan gadon baban mu"?. Gira ya dage "eh madam to mene a ciki"?. "Amma dai gadon surukin kane". "To Zarah surukin nawa ba ubana bane"?. "Duk da haka". "Ok yayi to zo mu kwanta bacci nake ji". Zaro ido tai "anan din? gaskiya a'a bazan kwana anan ba". Juyawa tai zata fita ya dauketa yana dorata akan gadon yace "wannan daga baya kenan kwana kam sai kinyi". Zatai magana ya rufe mata baki da nasa yana bata kiss mai d'umi wanda yasata sauke ajiyar zuciya. Zuge zip din doguwar rigarta yana zura hannunsa ciki da sauri Fati ta kankameshi tana kwantar da kanta akan kirjinsa". Da yake cikinta ya riga ya tsufa saita dabara yadan karkata ta ta gefe ya shigeta yana binta a hankali sakamakon yanayinta. Page 43 to 44. Washe gari tun kafin asuba tayi ya tasheta suka shirya anayin sallah suka wuce Abuja. Da safe kowa yana zuba idon yaga ta inda zasu bullo amma shiru Sadiq daya shigo jin ana cewa ko suna gidan hajiya. Yace ai yanzu kam Al'ameen yana Abuja domin gida suka tafi shida Zarah motarsa bata nan" mamaki ne ya kama kowa ganin basuyi sallama ba. Kwana biyu da tafiyarsu daddy ma suka bi bayansu a ranar da suka koma suka tarar Fati na asibiti. Dukka asibitin sukaje a lokacin Fati harta haihu ansamu baby boy farin ciki kamar basu taba jika ba sai akansa mami har mamaki ta bawa kowa ganin yadda take rawar jiki. Da aka sallameta gida mami ta wuce da ita domin ta bata kulawa Afeeyah kam tana tare da babyn. Kulawa sosai mami take bata kuma kusan kullum saita nemi yafiyarta bisa abinda tai mata tayi kas dakai ta bata hakuri, Fati kuma tana nuna mata cewa babu komai ya wuce ita mahaifiya ce a gareta. Ranar suna baby yaci suna LABEEB sunan abokin Al'ameen wanda sukai makaranta tare. Zainab na shigowa gidan da yake tunda ya saketa bata gari tana zuwa ta rungume mami tana kuka. Cikin mamaki mami tace "ke lafiya kukaan me kike". Zainab bata iya dakatar da kukan da take ba ta rike hannun mami tana cewa "mami da gaske ne abinda nake ji wannan yar kauyen ce ta haihu tare da Al'ameen ko mafarki nake kunne na baiji daidai ba"?. Mami tace "wanne irin mafarki kuma Zainab? Bayan gashi kinga zahiri Allah ya azurta Al'ameen da samun d'a namiji ya sanya masa sunan abokin sa Labeeb". A rude Zainab tace "dan Allah mami kisa baki ya mayar dani dakina wallahi zamuyi zaman lafiya nayi nadama ina son Al'ameen". Kai mami ta girgiza "a'a Zainab da dayanzu ba daya bane kada kije ki sake gurbata musu zaman su Fatima Zarah ce ta dace da Al'ameen". "Nima na dace dashi mami kalli ki gani ya zauna da yar kauye ma balle ni tashin birni nasan komai". "Ai Zainab da kikasan komai sanin naki baiyi amfani ba tunda kika samu damar zama dashi bakija hankalinsa ba yanzu kam saidai nace kiyi hakuri duk abinda zai takura rayuwar Al'ameen bana kaunarsa". "Mami me kike nufi kenan na hakura dashi"?. "Eh abinda nake nufi kenan ki barshi yai rayuwa da matarsa
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25