Chapter 7
Chapter 7
zagi iyayen su kwalliyace duniya tazo karshe dan jakin ubanki har tambaya ta kike me tai min ta kusa kashe min yaro ta mutu ma ban huta ba kema da baki je ba gashi nan ta hada da kurwarsa da taki ta tafi dasu lahira meye na bata lokacin ki wajen tunanin ta kome zakuyi ba dawo wa zatai ba". Kai Afeeyah ta girgiza batare data sake magana ba Zainab ce tai sallama da dumemen akwatin ta bayan ta driven gidan sune daya kawo ta dauke da wani akwatin. Cikin mamaki Afeeyah ke kallonta yayin da mami ta washe baki cikin murna tace tun shekaran jiya da Binta ta kira ni tace zaki zo kimin kwana biyu nake zuba ido saiyau sannu da zuwa". "Yauwa mami ina kwana Zainab tace tana zama kujeran dake facing din Afeeyah a fakaice ta nuna Afeeyah da yatsa tana maganar kurame". Tsaki Afeeyah taja cikin tsanarta ta mike zata bar gurin mami tace ke Afeeyah ja akwatunan nan ki kai mata su part din ki acan zata zauna cikin daya daga bedroom din part din". Matukar takaici ne ya kama afeeyah har bata san sanda hawaye ya zubo afuskarta ba amma ta goge tana rike hannun akwatin ta wuce kamar yadda mami ta umarce ta". Zaunar da Zainab mami tai tana cewa kinsan me yasa nace ki dawo gidan nan da zama "?. Kai Zainab ta girgiza mami taci gaba babu komai zan fada miki ba yanzu ba wani aiki zaki min". Daidai Afeeyah ta dawo tadau dayan akwatin Zainab tace hay madam kidan hada min ruwan wanka no hot no cool". Cikin bacin rai Afeeyah ta juyo muryarta da fushi tace ko kinfi uwarki kokari baza ki samu abinda kike so ba ni ba sa'arki bace nafi karfin yi dake jaka kawai". Zanci uban ki fa Afeeyah jimin shashashar yarinya". Mami ta fada tare da kallon Zainab tace rabu da ita dama fushi take bari zansa a hada miki yanzu". Afeeyah na shiga bedroom dinta ta fada kan gado tana fashewa da kuka tace" ya Allah kaine ka fimu son Abni ka karbi kayar ka kayi mana canji da mafi alkhairin ta ka tausayawa dan uwana ka bashi mace ta gari me share hawayen mijinta". Hayaniya ce sosai ke tashi da shewar mata a gidan su Abu domin anzo nemawa ilya aurenta. Lami makwafciyar su dake duba kayan da komai kala bibiyu ne ta rafka gud'a kamar zata cire hancinta tace. "Kai masha Allahu Allah yasa Jamila ta tayi 'kashin arziki kamar Abun ki Saude ni ina Salamatu ne". Saude dake rausaya kai irin uwar 'yar nan tace wai ta tafi gidan su tun safe munafika". Aliya ta amshe da cewa ba wani bakin ciki take saboda 'yarta zatai kwantai tunda dame Abun ta fita yan watanni ne". Gadoji tace humm aiko bakin ciki zai kashe ta don tunda nake ban taba ji ance ga wani yana san fatin taba inaga bakin jinin daga sune". Mukam biki zamusha mu gwangwaje matsalle me kalangu zamu gayyato yazo ya buga mana gangar cahiya😂🙉. Laraba tace ni kuma hankalina be kwanta da fitar Salamatun nan kar muje munna nan mun bude baki da hanci tana can tana gunbudowa Abuwa asiri". Zaro ido Saude tai tana dafe kirji tace Allah ko 'kawata har kinsa naji nima nawa hankalin ya tashi". Tsomo baki tabawa tai to meye muma sai mu tashi tsaye ko taki ko taso aure sai Abu nada 'ya'ya Fatima bata samu mashinshini ba ehe🙄. "Kunga mubar wannan maganar bari na duba mana jalaf din shinkafar kota nuna muci" cewar Saude tana mikewa. Lami na ganin Saude ta wuce kitchen ta rike baki cikin munafirci tace" jama'a yau nake ganin wani ikon Allah mutuwar zuciya ta 'kare a dangin su ilyasu kalli wai komai biyu". Tabawa na kallon kofar kitchen tace hum abinda yake cin raina kenan yar uwa kika riga ni furtawa mutum da hankalinsa bazai kai yarsa wannan gidan ba". Gadoji tace nima sheda ce ina marsida yar gidan Bala sai daga gida ake kai mata abinci mijin ya kasa riketa kuma ai kinsan mijin nata Sado (Sa'idu) dakin su daya da ilyan". Laraba tace mukam ai taushe zamu zo mu kwasa ina ruwan mu dama irin su abuh ai sai ana basu tantirai kuma nasan zataci ubanta a gurin Halima domin ita bata zama lafiya da surukai". Aliyah tace yo matar da ko naman miya ne sai a gaban ta ake rabawaa dan kar a cuceta duk cefanen da yayanta zasuyowa matan su saita burkice kowacce leda idan kaje kasuwa baka biyo ta dakin taba kuna zaune zata fado muku daki ba sallama🙊". Lami dake dariya tace kice Saude abar hankata baki Abuh karamar bazawara za ai sakin uwar miji ba sakin wawa ba". Duk gurin dariya suka kaure daidai Saude ta fito da katon tire fal da abinci ta ajiye tana cewa dariyar me kuke"?.. Lami tace dariyar farin ciki kawata sai aurar da yaran mu muke asirin mu a rufe tuna hakan ne ya samu dariya". "Wallahi kuwa lami ai abin da dadi zuma da madara muci kartai sanyi dan nasa mana kitse a ciki . Hummm ayya Saude kin 'baro🙄😖😠😕. 💰'DAN MILLIONAIRE💰 Page 15 to 16 Zaune suke a palor misalin karfe tara na dare daddy dake rike da wani photo ya mikawa Al'ameen yana cewa. "Aminullahi wannan 'yar gidan abokina ce Mudansur sunan ta Afnan ban sanii ba ko tayi maka saika aure ta". Da sauri mami ta amshi photon daga hannunn Al'ameen tana cewa me laifin wannan yarinyar ta hadu kawai ka nema masa ita". Hade rai Afeeyah tai tana kallon daddy tace nidai a shawara ta abar min dan uwana ya huta ya nutsu daga baya zai samu wacce yake so da kansa". "To uwar iyayi wa ya sako dake" mami ta fada tana harararta. Murmushi daddy yai yayi kyau Afeeyah kin fadi gaskiya amma bari naji ta bakinsa Al'ameen kana son ta"?. " a'a daddy" shine kawai abinda yace . "Ji banza " mami ta fada cikin haushi". Dariya Afeeyah tai tana kallon mami tace gaskiya ne yaya Afnan bata dace dakai ba kalleta fa fiyu da ita kamar an zana d'aya . Duka mami ta kawo mata tana cewa jakin uban ki Afeeyah". "A'a daina zagin ta mana karki debe mata albarka tabi 'ya'yan kaji🐣🐤🐥. Amma tsakani da Allah alhaji meye abin kushe a wannan yarinyar". "Babu amma tunda baa kece zaki zauna masa da ita ba shi kuma yace baya yi shikenan abar maganar". Mikewa mami tai irin tayi zuciyar nan tace saida safe". Har hada baki daddy da Afeeyah suke wajen cewa Allah ya tashe mu lafiya". "Zan kama kine Afeeyah zaki min bayani". Bayan wata daya Abuh ce ta shigo gida da kukan ta Saude dake kan tabarma tace lafiya kukan me kike ko keda ilyasun ne yaron nan ya fara bani haushi ba wata uwar ya bamu ba tun kafin a kaiki gidan sai wulakanta ki yake zaici kwal ubansa😜😂". Kai Abu ta girgiza a'a ba shi bane Sa'adu ne dan gidan me gari". Ba shiri Saude ta mike na shiga uku meya hada ku zaki yayo min masifa😁". "Abu na kuka tace wai Fati yake so😱". "Wacece Fati kuma ina
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25