Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 6

Chapter 6

Dan Millionair Book 1 Complete Hausa Novel 1,196 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

makarantar". Wani kallo Afeeyah ta mata. cikin rainin hankali tace Allah ko mami da gaske kike"? To bazan gyara ba makaranta zanje ba irin kice me zaman kashe wando a gida ba zan fita idan kin isa ki dakatar dani ko kidau mataki". Da kallo Zainab ta bita lallai yarinyar nan zaki ci ubanki bin bayan ta tai da sauri daidai Afeeyah ta tashi mota tasha gaban motar. Afeeyah bata fasa ba tayo kanta zata bigeta da gudu Zainab tai tsalle tana fadawa cikin fulawoyi😂🌻🌷🍁 ". Dariya Afeeyah tai tana lekowa ta glass din motar tace au dama zaki gudu dakin tsaya saina maida ke gurguwa nakasashshiya nasa ki zama mabaraciya a cikin gari amma a juri zuwa rafi mu zuba nida ke dan halas ka fasa". Tana gama fadin haka tai kofar gate tsaki Zainab tai tana mikewa ganin yadda ta taba farar rigarta domin ba a dade da yiwa flowers din bayi ba". Tana komawa ciki hajiya binta na fitowa ganin kayanta a bace yasa tace daga ina meye ya bata miki riga"?. Cikin takaici Zainab tace waye zaimin haka idan ba wannan shegiyar yarinyar Afeeyah ba". Toke meye damuwar ki da ita kuna yan uwa amma jinin ku bai hadu ba". "Yo umma dan ubanta waye jakin ta da zata kwanta da safe bazata gyara gado ba". "Ok akan haka ne amma dai aiba wani ne ya hana kiba kece kikai ra'ayi" . "Allah ni umma bana son yar aiki tana shiga daki na tana kallon asiri na". "Yayi masu asiri karki sake cewa ta gyara miki gado bansan shashanci". Cikin jin haushi Zainab ta mike tana 'ku'kuni tabar palon hajiya Binta data bita da kallo tace humm Zainab kenan indai Afeeyah ce tana daidai dake". Kwana Al'ameen yai a sume baisan inda kansa yake ba sosai daddy ya shiga damuwa mami kam suman Al'ameen bai d'ara taba saima wani irin farin cikin data tsinci kanta aciki na muutuwar Abni din ji take kamar ta taka rawa🙊🙄. Wanda dole sai a asibitin suka baro shi domin bai dawo hayyacin saba Abni kuwa tun jiyan akai mata sutura😢. Abuh da 'kawayen ta suna zaune a dandali suna musu akan samarin 'kauyen suka hango Fatima tsaye a 'karkashin wata bishiya tana dariya". Rabi tace lah Abu ga hegiyar gidan ku can tana dariya ita kadai kamar me aljannu". Abu data kalli gurin tace barni da yar iska tunda bata da samari dan ta fini kyau a banza". "Ahayye ji tsinannun munafikai wato kun zauna kuna gulmar 'kawata ko inji uban waye ya fada muku bata da saurayi ita data fi kowa sa'a ma tunda Sa'adu ne yake sonta dan gidan me gari". Juyawa sukai inda ake maganar suka ga Asabe tsaye da itace a kanta alamar gida zataje daga gonar baban su take". 'Duuuu sukai kanta zasu rufe ta da duka ta sauke icen tana zaro guda daya tace naga hegiyar da zata taba ni saina fasa mata kai". Duk tsayawa sukai cikin huci Abu tace idan kin isa ki aje itacen mana wallahi saina fasa miki baki". Aje itacen Asabe tai tare da shakar wuyan Abu wacce batai zato ba tana cewa" na aje da kina nufin dan kina tare dasu yasira bazan iya dukan kiba zanji tsoronki". Idon Abu sun fitfito sakamakon Asabe jibgegiya ce dakyar ta samu su Balki suka babbare hannun Asabe daga wuyanta". Tari ta kama yi babu kakkautawa kamar zata shide Asabe data dau kayanta tace nan gaba ki sake kawo min raini saina kusa kahe ki shashasha". Saida Asabe ta tafi sannan rahma ta samu bakin magana kiyi hakuri Abu bamusan zata shake kiba amma nan gaba zamu shigar miki😹😀". Tsaki Abu taja ke dalla matsa gefe matsoraciyar banza duk yawan ku mutum daya ta gagare ku". Ihu suka sa mata suna wakarsu ta dandali suka ce dama waye ya tsokane ta tsuntsun daya ja ruwa shi ruwa ke duka. Mikewa Abu tai a fusace tana kallonsu tace kada hegiyar data sake kula ni a cikin ku tsinannu kawai". Dariya suka kwashe da ita suna tafawa to sai me dan mu daina kula ki wata uwar kike bamu. Daukar fantekar abincin ta Abu tai tana barin gurin dama a wuya take domin tayi kwashe ilya baizo ya sayi abincin ba". Mrs Al'ameen Ahmad ce Page 13 to 14. Satin Al'ameen guda aka bashi sallama ya dawo gidan su Abni nan sabon ciwon sonta ya bude babi ganin da daddy yai ba warkewa Al'ameen zaiyi su dawo Nigeria ba yasa yace wa su mom kawai zasu koma gida". Anan daddyn Abni yace mr Mustapha mezai hana ka amince a bashi 'kanwarta Saira". Al'ameen dake gefe tun kafin daddy yai magana yace a'a daddy na hakura bazan yi aure ba a rayuwa ta". "Me yasa my son? da Abni da Saira daya ne"?. Kai Al'ameen ya girgiza yana cewa" daddy bazan iya auren Saira ba badan bana son hada jini daku ba dan Allah ka fahimce ni aure ya fita a raina". "Shikenan son ba komai na fahimce ka" alhaji Mustapha ya kalla cikin fara'a yace babu komai ai muna tare mun zama dangin juna Allah ya tsare hanya yasa kuje gida lafiya". . Anan mami ta gane cewa da gaske Al'ameen yake ashe gidan su Abni musulmai ne amma itafa duk da haka gara da Abni din nan ta mutu hankalin ta ya kwanta yanzu d'anta zai dawo daidai. Sosai alhaji Mustapha ya tausaya musu kuma ya sake yi musu ta'aziyyah da godiya akan abinda sukai musu "gaskiya kuna da karamci mun gode sosai Jonah mu zamu tafi". Har airport sukai musu rakiya sannan suka sake yin ban kwana da juna. Wanda Al'ameen baisan lokacin daya rungume Jonah ba hawaye na zuba a idonsa". Mami taji haushin rungumar dayai masa Allah-Allah take su tafi kamar tana kan 'kaya dakyar Al'ameen ya saki Jonah suka shiga jirgi domin dawowa Nigeria. Mutuwar Abni hatta Sadiq da yazo gidan washe garin da suka dawo mutuwar ta taba shi wani irin mugun tausayin dan uwan nasa ne ya kama shi". Yace" Al'ameen kayi hakuri dan Allah kada kasa damuwa aranka ka zama musulmi me daukar kaddara da cinye jarrabawarka Allah ya canza maka da mafi alkhairin Abni a rayuwar ka". "Amin" kawai shine abinda Al'ameen yace dan bai cika magana sosai ba Afeeyah tayi kuka sosai domin ya taba bata wayarsa sunyi vidio call da Abni kuma sun saba da ita sosai". Tana kwance akan kujera tai ruf da ciki idonta a rufe kamar me bacci saidai zurfi kawai tai cikin tunani mami dake tsaye a kanta tana kiran sunan ta . Ganin bata amsa ba yasa afusace ta sakar mata duka wanda a razane ta tashi zaune tana sauke ajiyar zuciya me karfi tace " mami lafiya". Tsaki mami tai tana cewa wato kema ashe sakarya ce ban sani ba ko dan ubanki wannan yarinyar dangin kice zaki dorawa kanki masifa kullum kina cikin tunani wanda kila koni na mutu bazaki damu haka ba". Hade rai Afeeyah tai tana kau da kanta gefe cikin takaici tace mami ko makiyin kane ya mutu jikinka yana sanyi balle Abni me ta tare miki wanda tabar duniyar baki daina ambaton taba". "Kwarai Afeeyah zage ni zamani ne yaya su

Table of Contents

Chapters

25 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});