Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 4

Chapter 4

Dan Millionair Book 1 Complete Hausa Novel 1,198 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

banza kin girma amma kina shiga daji bakisan kaddara ba na biye miki kina neman kashe min yaro kamar ba kece kika haife shi". "Saiya aureta idan har matarsa ce saiki dau mataki kuma umarni nake baki ki shirya tafiya ranar monday nan da kwana hudu na gama yanke magana". Yana fita ta mike da gudu tana shiga part din Al'ameen yana zaune ruwan ya kusa karewa tana zuwa cikin karaji da ihu da yage yage kamar me ciwon hauka ta fisge ledar ruwan tana wurgi da ita sannan ta fadi kasan carpet tana shure shure. "Tace Al'ameen ka cuce ni nayi asarar haihuwa Sadiq bai taba sani nayi bakin ciki ba balle kuka haka kanwarka Afeeyah daka girmeta da shekaru sosai bata bani wahala ba. "Amma ka sani kuka na zubar da hawaye saboda kai idan har kana so na yafe maka kaje ka samu daddyn ku kace ka fasa auren wannan banzar yarinyar". Al'ameen dake mata kallon mamaki ganin yadda take kuka kamar yarinya ya mike tare da dago ta yace mami lafiya wani abu ne ya sake faruwa". Fisgewa tai tana cewa ban sani ba wallahi Al'ameen nayi asarar haihuwa amma ba lallai kai dana bane ne tunda haihuwar asibiti nai kila an canza min kai dan da na haifa bazai rika wahalar dani haka ba ". Zaiyi magana ta daga masa hannu babu abinda zakace min baka da wani abu da zaka fada min kaje ka karata" tana fadin haka ta fice a bedroom din. Typing📲 💰'DAN MILLIONAIRE💰 YUSRAH MUSA ABUBAKAR Page 07 to 08 Iya tsananin damuwa Al'ameen ya shiga domin bai taba tunanin kiyayyar mami zata sa tace kila anyi mata canjinsa a asibiti lallai dole ya samu daddy koda son Abni zai kashe shi ya hakura". Fita yai daga part din nasa yana shiga bangaren daddy cikin sallama zaune ya same shi a palor yana duba takardu masu yawa zama yai a kasan carpet yana kallon daddy cikin dauriya dason ganin ya jure yace. "Daddy na fasa auren Abni na hakura basai kunje ba Allah zai musanya min da mafi alkhairin ta dama ba komai mutum keso ya samu ba". Batare da alhaji Mustapha ya dago daga kan aikin da yake ba yace " me kake cewa banji sosai ba hankali na ya kasu gida biyu". Sauke numfashi Al'ameen yai yana cewa daddy na hakura da auren Abni na fasa". Murmushi daddy yai yana dan kallonsa yace saboda Aisha ko "?. Shiru yai domin gaskiya badan mami ba babu abinda zai hana shi auren zabin ransa". Dawowa daga tunani yai jin daddyn na cewa" nace saboda mamin ku. Ka hakura ko"?' "Eh daddy domin mahaifiya ta tafi min komai mahimmanci tace duk cikin yaran ta nine batai sa'ar haihuwa ba ina wahalar da ita ni kuma banason saba mata na fasa auren amma bazan auri kowacce yarinya ba". "Ni kuma ban fasa ba Aminu ina nan akan bakana saina baka abinda kake so aure meye baya samarwa dan tana yar wata kasar saiya haramta ka aure ta ka kwantar da hankalinka idan yarinyar nan matar kace saika aure ta ba gida daya zaka zauna da mamin kaba balle kace kana can gurin ka daban". "Daddy na sani cewa tai idan na aure ta bata yafe min ba". "Zata yafe maka idan taga abinda auren ya kawo mata kaga bar bata wa kanka lokaci wajen tunani da damuwa ranar monday zamuje London babu fashi". Sauke ajiyar zuciya Al'ameen yai cikin tunanin ya zai kare da mami baya son hayaniya ko kadan. Washe gari suna zaune a palor mami ta fito daga part dinta tana waya ganin su a zaune yasa bayan ta gama tace. "Al'ameen kadau mota yanzu kaje airport ka taho da Zainab munyi waya da hajiya Binta tace min driven ta ba lafiya". Tun kafin Al'ameen yai magana Sadiq yace amma mami ga direbobi da yawa anan mezai hana daya yaje ya dauko ta yarme iyayi ta fito ta tari motar haya man a kaita gida". Cikin harararsa mami tace to uban yan shishshigi banyi dakai ba kaiba asibiti zakaje ba meye ya biyo dakai tanan gidan". "Mami nida gidan mahaifina kice meya kawo ni dan kawai aure yasa nabar gidan". Bata bashi amsa ba ta kalli Al'ameen tana cewa kaji dai na fada maka ko tana can tana jiranka"?. "Jiwai tana jiran ka kamar wani driven ta wato wannan yar iskar yarinyar hajiya Bintan ce ta dawo". Cikin yanayin tambaya Al'ameen yace wace ne yarinyar wai yar gidan umma kanwar mami dai ina take da yar dahar take fita waje". Daidai sun mike Sadiq yace kai amma Zainab wata yarinya me shegen tsiwa kodan ba a hannun hajiya Bintan ta girma ba tana dangin babanta amma kai da yar uwar ka". Shiru Al'ameen yai suna tafiya yana tunani amma gaskiya ya manta yarinyar saidai yanzu idan ya ganta. Tana tsaye tadau wankan riga da wando wanda sunyi bala'in matseta gashi tasa wani dan mayafi wanda dashi gara babu tana sanye da glass . Sadiq da yake shike driving yace kalli to gata can wani irin kallo Al'ameen ya bita dashi ganin shigar datai arniya sak ba wanda zaiyi tunanin yar musulmai ce. Tsaki yaja yana fita a motar daidai ta karaso ta zare glass din idonta tana kallon su sai kuma tadan murmusa cikin yanga tace Sadeeq ashe zan iya gane ka tsawon lokaci bamu hadu ba". "Eh shigo muje" abinda yace kenan domin shima shigar datai ta bashi haushi". Juyawa tai saitin da Al'ameen yake tsaye tace driver samin kaya a bayan mota kayi sauri nan, da minti biyar na ganni a gida". Zaro ido Sadiq yai ke driver fa kika ce ya miki kama da driver"?. Yatsina fuska Zainab tai mezai hana direbobin aiba kamace dasu ba". Kai Sadiq ya jinjina bai sake magana yace Al'ameen shigo mu wuce". Katseshi Zainab tai wai dan Allah Sadiq nice zansa kayan cikin mota shi meye amfanin sa". Banza Sadiq ya mata jin motar ta tashi tsoron karsu tafi su barta yasa dole tasa kayan da kanta sannan ta shiga motar". Sun danyi tafiya kadan tace gaskiya ne haka nake son driver babu sanya amma Sadiq ina wannan 'kanin naka mejin kannan naji umma na tace yanzu ya zama soja ko"?. Lallai yarinyar nan ba karamar yar iska bace Sadiq ya. Fada a ransa yana kallonta tta mudubin mota yace. "Ga miciji ai ba a neman ja ki tambaye shi da kanki". "Oh shine wannan sorry nace maka driver ya kake". Babu wanda ya kula ta zuwa wani lokaci tace yauwa na tuna shakka babu sunan ka Aminu na manda'ko😂. "Dariya ce ta kama sadiq lalli Zainab taci kai amma bari ya kyale ta Al'ameen na daidai da ita". Cigaba tai ko shekarun baya na tuna ya tsani zuwa kauyen mahaifin ku wata rana zakuje ya fadi a kasa yana burgima shi bazai jeba daddyn ku ya ciro bulala a garden ya zane sh...........' Wani irin taka burki Al'ameen yai wanda saida ta gwaru da kujera a fusace yace "fita a motar nan". Zaro ido tai baka karaso ba ga gidan can dan kawai na fadi gaskiiya na tuna maka da baya"?. Cikin tsawa yace "get lost". Kallon Sadiq tai ko zai

Table of Contents

Chapters

25 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});