Chapter 9
Chapter 9
akwai dan tazara tsakanin su da kasuwa ,cikin natsuwa tagama siyan duka abunda Aunty tace ,haka ta riko kayan ta nufi titi don samun abun hawa 'a can tsallaken titi ta hango wani mutum yawuce yama tallan a agwalima ,hannu tafara daga mishi alamar yatsaya sedai da alamu sam be kula da itaba ,ganin da tayi kamar babu motorn da ze wuce kusa yasakata saurin tsallakawa ,sedai tun kafin takai tsakiyar titi ta sake duka kayan hannunta sakamakon wani uban horn da yacika kunnen ta duk tabi ta rude ta kasa yin gaba ta kasa yin baya ,sedai tayi tsaye tare da saka duka hannunta biyu ta toshe kunnen ta ,fitowa mutumin da ke cikin motorn yayi ,fuskar shi a hade da alama tabashi haushi sedai kai tsaye bazaka fahimci hakan ba ,tana nan toshe da kunne sedai taji anja hannunta ,anyi gefe da ita cikeda mamaki ta dago dan ganin waye ,sedai har yayi gaba abunshi yana kokarin shiga motorn shi "am sorry ya tsinkayi siririyar muryarta wacce ke nuna har yanzu acikin tsoro take ,dan waigowa yayi sedai karaf idonsu yahade cikin na juna ,bin junan su da kallon sanin suke sedai sun kasa tuna a ina sukasan juna " she damn cute ya furta can kasan makoshi ,saurin janye idonta kanshi Meerah tayi tafara tattara kayan ta da suka watse.... ,,,,,,Harhada kayanta tayi batare da ta sake kallon inda yakeba ta tsayarda napep ta shiga, bin Napep din yayi da kallo harse da ta bace wa ganinsa tukuna yatayarda motorn shi ya wuce. Cikin Napep ma Meerah se tsaki takeyi se yanzu ne takejin haushin rashin siyan agwaluma da batayi ba Washe gari tunda Meerah tagama sallah takasa komawa barci,saboda ta matsu gari ya waye Fatima ta zo su wuce ,tanan zaune har 8:00am bataga Fatima ba hakan ne yasakata daukar wayarta ta kirata ,cikin bacci Fatima taji karar wayarta ,dan tsaki tayi ganin an katse mata baccinta ,idonta a rufe ta kai wayar a kunne "Hello tafada cikin murya irin na masu baci " kut ,Meerah tafada cike da jin haushi " amma wlh Fatima ke yar wulakanci ce amma dai kinsan jiranki nake ko ,da sauri Fatima ta tashi tana duba agogo ,waro ido tayi tare da Fadin " am sorry our head girl,wlh bansan lokaci yatafi hakan ba ,tsaki Meerah tayi batace komai ba ta kashe wayar sa sauri Fatima tashiga toilet wanka tayi tukuna ta fito ta shirya ,zuwa tayi ta samu Momynta tayi mata sallama akan zata tafi gidansu Meerah ,fatan dawowa lafiya kawai tayimata ,saboda tasan wacece Meerah da kuma shakuwar da ke tsakanin ta da Fatima ,saboda ma nemanta da Fatima taitayi ne bata sameta ba yasakata hakura ,ranar nan da Meerah tazo kuwa ,har dare labarinta Fatima kebaiwa Momy sedai tace "yanzu Meerah ta sauya ba kamar da ba ,a da Meerah irin yaran nan ne masu kiriniya shiyasa kaf a school dinsu babu wanda be santa ba gashi tanada kokari ,kuma ta iya zama da mutane hakan ne yasa kowa yake kaunarta. duk da kwatancen da Meerah tayiwa Fatima,amma seda ta sha tambaya kafin tagane gidan su kasancewar a lungu yake ,kuma unguwar ba wurin zuwanta bane ,da sallama dauke a bakinta ta shiga Aunty da ke kitchen ne taji ana sallama lekowa tayi don ganin waye ,kallon rashin Sani tabi Fatima da shi , murmushi tayi tace " ina kwana? Itama anuty amsa ta tayi cikin sakin fuska,zata tambayarta sega Meerah ta fito , da sauri Fatima ta rungumeta tana fadin "on my kneel head girl,dariya sukayi dukansu ,aunty naganin haka ta gane Fatima kawar Meerah ce ,saboda haka takomawarta kitchen dan karasa abunda takeyi. Kama hannun Fatima Meerah tayi ,suka shiga daki ,sedai sosai take ganin mamaki hadi da ayar tambaya a idon Fatima ,sharewa tayi tace " ko so kike tace tafasa son ' yar aikin ,dariya Fatima tayi tace " a yanda xuciyarta take cikeda son wulakanta ki ,banajin zata hakura ,amma nikam Meerah meyasa kika zabi to zarta kanki a matsayin yar aiki? Wai ina ya Maryam wai? Dan danan yanayin Meerah ya sauya ,idon ta na kawo kwallah " am sorry Meerah bansan zakiji haushin tambayar ba ,girgiza mata kai Meerah tayi tace" Fatima shin ganin yanda rayuwa ta mayar dani ma bazaki gane cewa komai ya sauya ba ,banda kowa a duniyar nan yanzu ,se wannan matar itace ta mayemin gurbin dangina ,Fatima idan kana duba rayuwa zaka gane kaidin ba kowa bane ,yanzu dai gani Ameerah Farook Head girl da ake alfahari da ita a school 'yargatar da kowa ke burin sakata farinciki Ummina ,Abbanah, yayata mafi soyuwa ,amma gashi yau na wayi gari banda kowa ,burin yayata ya rushe na son ganin nazama cikakkiyar Birrester,ta karashe tana zubar da kwallah ,sosai tausayinta yakama Fatima , hakuri kawai ta bata ,duk da tanason tambayarta dalilin mutuwar Maryam sedai bata so tasake sakata kuka ,kiran aunty ne yasakata,tashi ta fita , kallo daya aunty tayi mata ta gane kuka tayi " ki dauki breakfast dinki ,tafada tana daukar nata tayi ficewa ,cikin mutuwar jiki taaniye jug din kunun agaban Fatima sake fita tayi segata ta dawo da plate din alale,tunkafin ta karasa ajiyewa Fatima ,ta janyo cup ta zuba kunu cikin jin dadi tace " kamar kinsan wlh banci komai ba ,ashe da rabon nazo nasha favorite dina kunun tsamiya ,sosai kuwa tasha kunun hakan ba karamin dadi yayiwa Meerah ba ,don batayi tunanin zatasha ba ,seda suka koshi ,tukuna Meerah ta tashi ,tube kayan jikinta tayi ,ta fiddo wata kodaddiyar atamfa ,duk ta cimuimuye da alama ta dade cikin tsomakara Kallon mamaki Fatima kebinta da shi ,cikin lokaci takoma kamar irin mutanen nan ,da talauci yayiwa kanta 'bata sha mamaki ba seda taga ta yafa wani gyale kodadde irin pashminar dinnan da akayi yayi can da " mutafi tacewa Fatima " Haba Meerah me kikeyi haka kinkuwa sam wane irin gida zamu tafi ,ai seki saka Rufaida korarmu " kar ki manta ,fa Mabaraciya ce ke gabanki,zamu tafi ne amatsayin yar aiki bawai kawarta ba ,kuma kora bana tunanin haka daga wurinta domin bawai saboda nayimata aiki ta daukeni ba ,sedan ta wulakantani,so na fison taganni a wulakancen ,jinjina kai Fatima tayi alamar gamsuwa . Seda ta shiga dakin aunty tace" aunty kimun fatan nasara zamutafi " to Ameerah rabbi ya dafa miki ,da amen ta amsa tana jin dadi har cikin ranta ,sun dade sosai abakin titi kafin suka samu Napep din da zata kaisu unguwar Knocking sukayi me gadi ya leko ,binsu da kallo yake ,yagane Fatima ,itace wacce ke zuwa wurin Rufaida, sedai mamakin ganin ta yake tare da wannan da batada banbanci da mahaukaciya ,gaisheda Fatima yayi yana bude mata kofa ,shiga tayi Meerah nabinta da a baya " ikon Allah yafada cikin xuciyar shi ,ga yarinya kyakkyawa ,ta bugu da jarida,amma da ganinta ta hadu da jarabtar ciwon haka ,ga kuma talauci domin da gani wannan tana cikin ciwon rashi Tunda suka shiga gidan Meerah takebin harabar gidan da kallo yananan yanda ta sanshi,sedai sabon fenti da akayi " dallah malama zaki fara kauyanci tun bamu shiga ciki ba ,Fatima tafada cikin sigar xolaya ,murmushi kawai tayi wanda da alama na yake ne ,cigaba da
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34