Chapter 34
Chapter 34
fito fici-fici tayi sallar saboda batason su tafi su barta ,koda ta gama Rumaisa ta fito mata da kayan da zata saka dan haka ta sanya mata ,suka tsaya jiran Ammi tagama addu'a suyi mata sallama ,bayan ta idar Rumaisa tafaɗa mata zasu fita ,adawo lafiya tayi musu ,cikin wasa tace " wato kun faki idon Mimi da Nurain shine zaku fita ko aiko idan yadawo gidan nan ya samu kun fita da Auta kunsan za'ayi darga da shi " Ammi karki damu xan siyo masa Icecreem ,ko Yaya? ta kalli Rumaisa ,dariya tayi mata a haka suka fita Fitowar su yayi daidai da fitowar Mu'aisam daga cikin ɗaki da alama ya daɗe da dawo daga masallaci dan kuwa har ya sauya kayan jikinsa yayi kyau sosai wanda har Rufee ta kasa ɓoyewa seda ta maganta " gaskiya Yaya kayi kyau ko har ka fara hasken amarci ne? Haɗe fuska yayi bece komai ba ,ita kuma Rumaisa se tace" yaya smile mana ,Allah baka ganka ba kamar zakaje wurin babyn ka anya kodai ,zance zamu raka ka? murmushin gefen baki ya sakar mata tare da faɗin " wlh za'a fasa fitar nan ,naga kuna neman maidani wani abokin wasan ku" Rufaida da takaicin maganar Rumaisa ya cikata se taja tsaki tace " wahalar tambaya name kikeyi bayan kinsan tare dani ze fita wannan duk wani yayiwa" fahimtar inda zancen ta ya dosa se Rumaisa tace " haba ke kam ai uwar gida ce sis Rufee ,kika sani ko har ya fara kyarkyarar amarya waƙil ma ku biyu za'a kai masa kinsan masu iya magana sun ce me mata ɗaya abokin gauro ,so yayana ze fita daga cikin su "cikin tsawa Rufee tace " aniyar ki tabiki Rumaisa sedai idan kece kike son sa wannan zamu iya zaman kishi dake amma babu wata mace da ta iso ya so ta ni nasan wanann ,hassada ne da baƙin ciki koda yake na daɗe da gane cewar kema kina son sa " riƙe baki Rumaisa tayi tace" ikon Allah kin taɓa ganin yaya ya auri ƙanwarsa ko kin manta alaƙana dashi ne ni matsayin ɗan uwan da aure ya haramta a tsananin mu nake masa ,da ace ina son sa kamar yadda kika faɗa kema kinsan da baxaki sameshi ba"Rufee xatayi magana ta tare nunfashin ta da faɗin " ki ajiye kalamanki zuwa gaba wata ƙil zeyi miki amfani a lokacin da kika gane cewar akwai wacce yakeso ba keba "da sauri ta wuce ta bar Rufee na sababi ,koda suka iso motar har ya gyara parking Rufee har ta buɗe gaban mota zata shiga se ta ga Nawwara zaune ,cikin haɗe fuska tace " ke fito ki koma baya " ɗago kai Mu'aisam yayi ya kalleta sedai bece komai ba ,har ta fita ta shiga baya ita kuma ta zauna gaban. tana shiga ya tada motar suka fita Babban shopping mall ya kaisu yace kowa ya zaɓi abinda yake so ,sosai suka zaɓi manyan tarare irin desingners dinnann masu matuƙar tsada ,daganan suka tagi gefen kayan yara teddies masu kyau Auta ta zaɓa ,daganan ne suka tafi gefen su chocolate,wannan kam Rufee da Nawwara ne kawai su diba dan ita Rumaisa bata shan kayan zaƙi ,Atm yabada a cire kuɗi ,har anyi debited se Nawwa ta hango wani babban boll cikin net ɗinsa irin elastic dinnann da ake hurawa da sauri ta je ta ɗauko tace " yaya musiyawa Nurain wannan " kai kawai ya ɗaga mata yasake bada Atm ɗin suka cire kudin suka tafi ,har zasu fita daga wurin idon sa ya hango mishi bangaren da ake seda irin jalabiyoyin nan ,dan haka kawai yabasu key yace su jirashi a mota yana zuwa , haka ya tafi ya zaɓo jalabiya har kala 3 masu shegen kyau da tsada , sannan ya dawo suka bar wurin. ganin kamar ba hanyar gida ya ɗauka ba yasaka Rufee kallon sa " Yaya ina kuma zamuje nifa nagaji gida nikeso na koma "to ko mu ajiyeki se ki shiga Napep dan zankai su wani wurin ne " haba yaya yanzu saboda Allah kamar ni dinnann se na tsaya a titi neman Napep? " ke ba mutum bace ko kinfi sauran muta ne ne " to Yaya abun ai a bayyane ne kaiman kasan ta zara me yawa da Allah yayi tsakanin talaka da me kuɗi ,saboda haka ni gaskiya bazan shiga Napep ba " to ko se kijira har mugama abinda mukeyi se ki koma a mota ,daidai lungun su Meerah ya shiga da motar sa , parking yayi daga nesa kaɗan da gidan dan ganin wata motar da ke a jiye kusa da gidan ,wannan karon kam hatta Rumaisa se da tayi magana dan mamakin inda ya kawo su tace " Yaya ina ne nan ɗin ? wlh kamar ba'a kd ba " hararan ta yayi ta madubin motar yace " idan kin fita kya tantance ,fitowa yayi ya ce dukan su su fito ,babu musu suka fito ,kiran Auta yayi yaimata raɗa a kunne ,a mamakin su se sukaga ta daga tsalle tana faɗin " da gaske yaya ? Kai ya ɗaga mata alamar tabbatar wa tare da mata nuni da ƙofar gidan su Meerah. kallon su Rumaisa tayi tace" yaya yace nan ne gidan Aunty Ameerah mushiga mugani ,kallon mamaki sukayi masa sedai be basu damar magana ba ,sema cewa da yayi "Rumaisa kishiga kudubata sauri nakeyi " bin banyan Meerah tayi ,ita dai Rufee kamar wacce aka kafe a wurin tama kas motsi ,lokacin da suka kai kofar gidan yayi dai² da fitowar Meerah tare da Muhsin ,alamar rakiya tayo masa ,sam bata kula dasu ba se da Nawwara ta rungume ta tana murnar ganin ,da mamaki ta cire hannayen ta da ta zagaye cikin ta dasu itama cikin jin daɗin ganin su tace " Auta waya nuna muku gidan mu? munxo ne muduba ki kwana biyu shiru ko bakida lafiya ne ,ashe ke kina nan soyayya ta ɓoyeki "ta faɗa cikin sigar zolaya "rufe ido Meerah tayi tana daria tace " Aunty ai wannan yaya ne ko? Tayi maganar tana kallon Muhsin ,se a lokacin Rumaisa ta gaidashi ,amsawa yayi yana shiga Mota tare da faɗin " bara na wuce tunda kinyi baƙi xamuyi waya dai Allah yaƙara lafiya"bata amsa shiba sedai ta ɗaga masa kai kawai tare dayimasa waving ,seda ya tada motar tukuna ta ja hannun Rumaisa tace" mushiga ciki Aunty " bin bayanta Rumaisa tayi....... Comments and share pls Real Bazamfaria ce ❤️
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34