Chapter 19
Chapter 19
dama na gabatar da kaina a gidanku saboda asan dani ina tsoron wasu suyi min kutse " Haba dai ,idan har da rabo ai babu wanda zeyi kutse ,and Kuma dai gaskiya bazanso ka gabatar da kanka tun yanzu ba saboda inaso ka ɗan bani lokaci kaga kafin nan mun fahimci junan mu ,kuma ma ni nafaɗa maka tun farko ba yanzu zanyi aure ba akwai aikin da nikeyi to se na kammala shi tukuna " nikam wane irin aikine da ze zama shamaki a gareni na mallakar ki a yanzu? "Kaga Manager don't bother ur self ,its off no use ,babu anfanin na faɗa maka ,kaga Yakamata ka kwanta nima baccin zanyi karka manta kayi addu'a" bata jira cewar sa ba kawai ta kashe wayar baki ɗaya ma tayi kwanciyar ta,xuciyarta cike *da saƙe²......... Comments and share pls *Sorry* *nayi* *mistake wurin nace Meerah se nace Zahrah ,bazan iya* *komawa nayi edit ba ,but* *nasan dai zaku* *fahimta luv You all mAh** *pipul* ❤️ Follow me on Wattpad@damselfeedo Real Bazamfaria ❤️ *INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION* ( *On* *word* *together* ) *MABARACIYA* *Story* *and* *writing* *By* *FIDDAUSI* *SANI* (damsel feedorh) 🅿️:1️⃣7️⃣ Washe gari Hayia sauda ta taso daga Niger ,bayan tayi handling gidanta a hannun Binta , bata sanar da kowa zuwanta ba ,dan haka babu wanda ya san zata dawo har Rufee saboda 2 days basuyi waya da ita ba a cewar Rufee tana fushi da ita ne. Misalin ƙarfe 1:20pm ,Hajia saudah ta iso gidan, shigo warta yayi daidai da fitowar Meerah daga cikin gidan hannun ta rike da yar'leda zata tafi kaiwa Nawwara saƙon ta ,da ido take bin motar da ta shigo dan bazata iya ganin wanda ke ciki ba ,saboda haka bata maida hankali kan ta ba tayi wucewar ta inda tayi niyya dan bata taɓa kawo wa ranta cewar Hajia saudah bace da Ammi tafara cin karo ,kwarjinin da matar tayi mata ne yasaka ta saurin xubewa a kasa tana kwasar gaisuwa ,da fari'a Ammi ta amsata tanayi mata wani irin kallo wanda ta rasa na miye mamaki ko rashin sani ,tun da ga waje suka fara jiyo hayaniyar su Nawwara ,da alama yau ma musun sukeyi akan wani abun ,da kuka ta shigo gidan ,tana kwalawa Ammi kira ,turus tayi ganin Meerah a gidan su se kuma ta tafi da sauri ta faɗa jikin ta ,tace " Aunty Nurain mugu ne kin ga yau ma seda ya kwacen abuna a school " ayya yi haƙuri ai kece babba Kinga abunki na kawo miki" ta bata ledar da ke hannun ta ,da murna ta amsa tana dubawa "Ko kece sabuwar Auntyn da aka ishemu da labarin ta jiya? Ammi ta faɗa tana murmushi"wow Ammi kalli abinda ta kawo min "Nawwara ta fitar ta na nunawa Ammi " kai lallai kam kin gode ,to kiyiwa Auntyn ki godiya mana "Ammi ni Aunty bata bani ba"to Nurain ai gatanan a gaban ka ka faɗa mata babu ruwana" dawowa yayi wurin Meerah yace " Aunty ni baki bani ba "ni ai babu ruwana da mecin zali ,so biyu kenan kana zaluntar twins sis naka dan haka idan kana so se kayi alkawarin bazaka sake amshe mata kayan ta ba "nayi alƙawari Aunty ,amma itama kifada mata tadena fadawa abokanaina cewar itace yayata" dariya Meerah tayi tace to shikennan zata dena ,ai baxaki sake ba ko ƙanwata? Kai ta ɗaga mata tace nadena Aunty "dariya Ammi tayi tace " idan kika biyewa rigimar wa'yannan ai bazasu barki ki huta ba ,kullum haka suke kafin atafi school za'ayi faɗa kuma da faɗan za'a dawo min "haba Ammi ai babu komai nikam rigimar nasu yana burgeni sosai ma ,bara na wuce se anjima Ammi" la har zaki tafi ko ruwa baki sha ba ya sunan ki ne " suna na Ameerah "Allah sarki sannu angode fa Allah yayi miki albarka "Amin nagode "har ta juya zata tafi Nawwara tace " Aunty zanje gidanku nima ,amma karki bari yaya Rufaidah ta buge ni "a'a kiyi zamanki kinji ,Kinga ai ba'anan gidan nike ba ,yanzu nan zan wuce gidan mu kuma Ammi bazata barki kije tare dani ba ta faɗa tana satan kallon Ammi " a'a Ameerah ni kam bazan hanata binki ba dan gani ɗaya kinshiga raina kuma har a xuciyata na yarda dake sedai,ƙa'idar Alh ne idan yazo garin nan to baya barin kowa fita ,har se ya koma and kuma inaso kisan wani abu kiyi taka tsantsan kinga wa'yanda kikeyi wa aiki basa son ma'aikatan su suna hulda damu ,bazan ji dadi idan kika rasa aikin ki ta sanadinmu ba ,dan Allah ki kiyaye kinji ,bawai saboda kar kishi go nan bane ,a'a sedan guje miki matsala" "To Ammi nagode sosai ni zan tafi "ok to ki gaida mutanen gidanku kinji . Koma wa bangaren su Rufee tayi dan tayiwa Larai sallama zata wuce gida ,tana shiga kitchen ta sameta tayi haje-haje dora wanan sauke wannan da mamaki Meerah tace " Aunty ba kin gama girkin tun ɗazu ba? Larai da batasan da shigowar ta ba ta jiyo da sauri ,tana zare ido tace " nikam Ameerah ina kika shiga tun ɗazu Hajiya Rufaidah ke neman ki "nema na kuma to me zanyi mata bayan seda na kammala duka aikina kafin nafita " cab! Hajia ce fa ta dawo ,shine take nemanki zaki gyara mata ɗaki, saboda yayi kura " Wai da gaske kikeyi Hajia ta dawo" ehhh mana menene ai nayi mamaki ma wannan karon ta daɗe dan gaskiya bata bari Alh ya kwana a garin nan bata dawo wa kinsan shegen kishi ne da 'ita. Meerah kam bata ma tsaya sauraren Larai ba ,da sauri ta kutsa falon ,raba ido kawai take yi a falon saboda matane har su biyar a zaune sun baje kayan ciye-ciye a gabansu ,se nishaɗi sukeyi " ubanme kikeyi akan su shegiya mayya kuryar su tafi ƙarfin ki "ko ba'a faɗa mata ba tasan cewar Rufaidah ce , sedai ba wanne ne a gabanta ba ,so takeyi ta tantance wacece Hajia Saudah a cikin matan nan ,kamar yadda suke binta da ido haka itama take kallon su ,bata gaishe su ba bakuma tayi magana ba ,sukar marin da taji a fusakanta ne yasaka ta dawo wa hayyacin ta da sauri ta zube a wurin. "a'a Rufaidah keda waye nikejin hayaniyar ki tun daga sama"Hajia saudah ta faɗa tana saukowa falon " Mama nida wata shegiyar Mabaraciya ce da na temaka na ɗauke ta aiki amma sam batasan me take yi ba ,ina tun ɗazu nike nemanta ta zo ta gyara ɗakin ki amma gana can wurin gantalin ta ,kinsan ,ƴaƴan talakawan nan kwaɗayi ne dasu ,salon taje can ma'aikatan gidan nan suyi mata ciki ayi kuka damu "tun da Meerah taji ta ambaci Mama se ta nemi zafin marin ta rasa ,sema kafe matar tayi da ido ,tabbas itama Hajia saudah kam cikakkiyar mace ce me ji da gayu gata babu lefi kyakkawa da ita ,a iya fuska kam bazaka taba tunanin tana da wani hali na daban ba " seda Hajiya Sauda tagama saukowa tukuna takai kallonta wurin wacce Rufee keyiwa wannan hargowar ,da sauri ta ja baya tana nuna Ameerah da hannu ,cikin rawar murya tace "Mar..y.am" jin sunan da ta
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34