Chapter 15
Chapter 15
har da gaske yake yi nikam zanyi murna gaskiya saboda irin mijin da nike roƙa mikine yazo Meerah inaso kisamu rayuwa me ingancin idan kika aure talaka hakan baze samu ba inason kisamu mijin da ze dawo da jin daɗin da kika rasa " haba Aunty kidena ma wannan maganar aishi jin daɗi base ga me kuɗi kawai ake samu ba kedai kiyi fatan samun miji nagari shine jin daɗin mace nawa ke auren masu kuɗin amma basuda kwanciyar hankali,yanzu keɗinnan yaya da Rufin asirin da Allah yayi masa ya riƙeki harma ni ɗinnan kuma saboda son da yake Miki ne kullum cikin soyayya da kulawa kuke ,na tabbata kinfi wasu matan masu kuɗin kwanciyar hankali,saboda haka ni duk wanda zan aura gaskiya se wanda ya iya soyayya sosai dan nikam nafison soyayya da kulawa Fiye da komai" ikon Allah Meerah yau ni kike faɗawa kinfison soyyaya idan kikayi aure? Daria sosai Meerah tayi tace " kai Aunty ai gara na faɗa Miki tunda kece uwar amarya,ƙawarta kuma yayarta so duk kika ga na kawo mijin auren gidan nan ,wanda be iya soyayya ba karma ki amince na aure sa dan ba zama zanyi ba" dariya kawai Aunty tayi tace to buɗe mana ledar muga me mota me ya kawowa ƙanwata" perfumes ne masu kanshi da tsada har kala 3 se wani dan card da alama complementary card dinsa ne " Masha'Allah kam Meerah da gani wannan yasan takan soyayya baki gani ba kyautar turare a zuwan farko nide shawara gaskiya karki wulaƙanta sa bamusan me Allah xeyi nan gaba ba ,Kinga wuce da turaren ɗakin ki kinsamu na shafawa " a'a Aunty kiɗauka dai keda kikeda miji zefi miki anfani" hararanta Aunty tayi tace" banson shirme maza kwashe abunki " Allah aunty ki ɗauka duka na baki ai inada sauran turaren da yaya yakawo mana da yazo " duk da haka dai Meerah kiyi anfani da wannan ɗin " to gaskiya aunty kiɗauki biyu Ni se nayi anfani da ɗaya" haka dai suketa musu daƙyar Aunty ta yarda ta ɗauki ɗaya daga cikin turarukan. Da daddare bayan sun gama sallahr isha'i suna zaune itada aunty take faɗa mata cewar dazu da sukayi waya da yaya yace xe dawo karshen makon nan ,cike da jin daɗi Meerah tace "Allah ya dawo dashi lafiya kwana biyun nan ban samu zama ba mundaɗe bamuyi waya dashi ba ,koda ma aini fushi nikeyi dashi tunda ko tambayata bayayi" Dariya Aunty tayi tace ai kunfi kusa idan yadawo sekuyi Shari'a keda shi. daga tsakar gida suke jin sallama wai ana kiran Aunty Meerah a waye ,kallon juna sukayi itada Aunty kafin tayi ƙarfin halin fitowa ganin yaron tace "Jabir kaine waya aiko ka kirana cikin daren nan? " Wanine dan gaju Aunty bakiji kanshin tutarensa ba kuma ma da ƙatuwar mota yaxo" tunda taji haka ta gane Muhsin ne " jeka kace tayi bacci kaji" har ya juya ze tafi Aunty da fitowar ta daga daki kenan tace Jabir jeka kace tana zuwa ,kallon Aunty tayi tana narke fuska kamar xatayi kuka tace amma Aunty me ze kawo shi cikin daren nan bayan ɗazu yazo ni wlh banson maita daga ganin sa xeyi naci sosai "kitsaya shegen musunki dai karki yi sauri kita fi ,kasan wayar dake hannun Aunty ta karɓa dan tayi anfani da toch light ɗin kasancewar akwai hijabi a jikinta ,ta tafi. A bakin zauren gidan tayi tsaye tana kallonsa daga inda yayi parking marfin motarsa a buɗe ƙafarsa daya a waje saboda akwai hasken farinta wata shiyasa zaka iya ganin komai Muhsin ma tunda tafito yake kallonta a tunaninsa zata karaso wurin da yake ne ,amma Sega ta tsaya hakan ya tabbatar masa da sedai shi ya sameta kenan , murmushi yayi dan garga Allah jan ajinta ya burgesa ,da sallama ya karaso ,itama bata ɓata lokaci ba ta amsa masa dan sanin muhimmanci sallama da tayi ,daganan kuma sukayi shiru ,shidai ƙare mata kallo yake a yayin da ita bata masan yanayi ba dan ta duƙar da kanta kasa tana wasa da wayar hannun ta ,katse shirun yayi da faɗin " ina wuni" harga Allah ita ta manta da bata gaida shi ba ,rufe fuska tayi ta ce " yi hakuri dan Allah na sha'afa ne ,ina wuni ya gida da yara? Cikin jin daɗi ya ce duk suna lafiya yara sunce na gaida musu da Auntyn su kafin su zo da kansu su gaisheta" Kallon mamaki tayi masa se kuma tayi murmushi tace "har sun samu labarina tun banyi accepting ba kenan" dariya yayi " ai nasan zuciyata bazata taɓa son abinda baze so ta ba tunda na ganki ta faɗa min cewar ga abokiyar rayuwa ta sake zaɓa min a karo na biyu idan babu damuwa ko zamu ƙara sa daga cikin mota saboda gaskiya akwai abinda nikeso na faɗa miki ,kuma kema zanzo nasan ke wacece a takaice " a'a karka damu ni yanzu ma zan shiga da ga ciki ne and gaskiya bana tunanin zan shiga motar ka da sunan hira ,kaganni ko kaga kuma gidanmu ,so idan kana ganin bazaka iya tsayuwa anan ba sedai ka hakura ,banada wurin ajiye ka dayafi wannan ,hira a mota yana zubar da mutunci and be kamata ma a matsayin mu na musulmai muriƙa kebe wa a mota mubiyu da suna hira dan munsan illar hakan ,dazu naga sako amma gsky banji daɗin hakan ba nide karka sake kawomin wani abu pls" to shikenan naji Insha'Allah zan kiyaye ,but tunda kince baxaki riƙa shiga moto ba se Nike ganin kamar tsayuwar anan ma ze iya zubar da mutuncin why not kibani tym da zan riƙa zuwa Kinga se muriƙa shiga daga zaure ko kamar hakan zefi " ehhh to amma kabani kwana biyu zanyi tunani akan hakan kuma dan Allah karka sake zuwa a week dinnan dan bazaka samu ganina ba akwai yan ayukka da Nike yi " yadda kike so haka za'ayi duk da nasan zuciyata xatayi ƙunci na rashin ganin ki har kwana biyu zuwa uku,sedai zaki bani contact naki Kinga se na rika kiranki hakan ze rage min kewarki " shiru tayi kamar karta bashi ,sedai ganin ko bata bashi ba tunda har yasan hanyar neman gidansu ,to contacts nata baze masa wuya ba ,saboda haka bata Musa ba ta bashi ,godiya sosai yayi mata har zata shiga gida yace " am bakiji ba" dawo wa tayi tace " mefa? Yace yaranki sun bada sakon gaisuwa nakawo Miki but baki basu nasu sakon ba " murmushi ta saki batare da ta shirya ba" kace ina amsawa sosai ,nima kuma ina gaishe su yaushe zasu zo su gaisheni? to zan faɗa musu se su saka ranar zuwa gaisheki da kansu......... *Am sorry* *nayi anfani da wasu kalmomi uku and ba lallai bane wasu daga cikin ku su gane saboda banbancin Hausa* a *inda *nace (Cibi) ina nufin (cokali.spoon) se kuma zaure ina nufin (soro) se hira ( zance ,ko taɗi)* 08039228702 *Wattpad@damselfeedo* *Comments and share pls* Real Bazamfaria ❤️ *INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION* ( *On* *word* *together* ) *MABARACIYA* *Story* *and* *writing* *By* *FIDDAUSI* *SANI* (damsel feedorh) 🅿️:1️⃣5️⃣ Rufaidah da bata san da zancen dawowar Abban su ba kasan cewar bata shiga sha'anin mutanen gidan bare ta
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34