Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 24

Chapter 24

Mabaraciya Book 1 Complete Hausa Novel 1,176 words 0 views Progress saved
Download Book

neman ƴar aiki,dan tawa tayi aure ,se na faɗi kaso me yawa da zan riƙa biyanta duk ƙarshen wata ,nasan iyayen ta ma zasu amince ,Kinga se na taho da ita ,Kinga kema zaki fita zargi" kai ƙwarai kuwa Hajia kinzo da shawara amma dai zanyi tunani akan hakan " Sallama sukayi Hajia Laura ta aje wayar tana bushewa da dariya " tabbas wani lokacin kwakwalwar Sauda bata aiki ,tsawon lokaci taki basu damar sanin ahalinta gashi cikin sauki zata je ga abun kaunarta , dan wlh komai ze faru bazata bar gidan ba se ta lasa zumar Rufaidah dan kuwa tun lokacin da ta ga hoton ta abun yakasa barin kwakwalwar ta ,kiran sauran kawayen cin mushen su tayi ta haɗa compress ,anan ta labarta musu ,kowa daga cikinsu shawarar yadda zata mallaki Rufaidah cikin sauki suka bata ,tare da bata ƙwarin gwiwar tafiya ,ko dan ta gano musu kalar mijin Hajia Sauda da takeyi musu tunkaho. Meerah# Da sauri ta kammala gyaran ɗakin ,tana gama yau bata jira lokacin tafiyarta yayi ba ,kawai ta tafita ,a daidai lokacin da tafito shiku Mu'aisam,ya fito hannusa rike da twins da alama fita zasuyi ,sam bata kula dasu ba se da Nawwara ta kwace hannun ta daga Mu'aisam,ta taho da gugu tana faɗin " Aunty" da sauri meerah ta jiyo ,ganin Nawwara se ta sake mata smile "iyye Auta ina zakije haka ,kikaci gayu "fita zamuyi Aunty zamuje gidan Umma ne " ba tare da Meerah ta san wace Umma take nufi ba tayi murmushi tace " lallai kam to ki gaisheta sosai kinji " lah Aunty ai bata sanki ba" Ehhh duda haka dai ki gaishe ta "karar horn da sukaji ne yasa da sauri Meerah ta sake hannun ta tace jeki ana jiranki " Aunty kixo mutafi mana "a'a ni Kinga gida zanje ,jeki karki ɓata lokaci" make kafaɗa tayi tace "Allah kizo zamu sauke ki a hanya ai haka Ya Rumaisa ma idan zamu fita se tace Yaya ya ajeta gidan ƙawayen ta kuma baya faɗa ,oya let's drop you" ta faɗa tana jan jannun ta "kamar wata sauna haka Meerah ta zama ita batabi Nawwara ba ,ba ta kuma hanata jan hannun taba" kishigo mutafi mana " taji maganar Rumaisa ,murmushi tayi tace" a'a ba hanyar mu daya ba ,kutafi kawai na gode " tsawar da Mu'aisam yayiwa Rumaisa ne yasakata ɗago idon ta ta kalleshi " zaki shiga mutafi ne ko natafi na barki nan idan Mazan da suke zuwa daukarta sun zo se ki shiga su rage miki hanya?sosai kalmar mazan ya bugi zuciyar Meerah sedai bata da halin maida magana a wannan muhallin ,da sauri Rumaisa ta ja hannun ta ta tura ta a motar ,babu yadda ta iya dole ta zauna ,sedai ta haɗe fuska dan ta kula kamar Mu'aisam irin mutanen da basu iya magana ba ,su kan faɗi duk abinda yazo bakin su ,idan ba haka ba wane namiji ne ya taba zuwa ɗaukar ta da ze faɗi haka Babu wanda yayi magana a motar se su twins da suke ta buga game a wayar Mu'aisam, basu tambayi ina zasu ajeta ba haka itama batayi magana ba ,tsayawar da taga motar tayi a gaban wani gida dake bakin titi ya sakata saurin buɗe motar tafita ,dan a tunanin ta ita suka tsaya ta sauka ,tun sun zo bakin hanya , sedai a mamakin ta dukan su suka fita ,Rumaisa ce ta rike hannunta kamar me tsoron karta gudu ,har suka isa bakin get ɗin gidan , knocking sukayi daga ciki aka amsa da ana zuwa ,da alama irin madaidaicin gidan nan ne da zaka ga get ɗin kusa da falon gida Wata yar budurwa ta buɗe kofar fuskarta dauke da farin ciki take musu sannu da zuwa se kuma ta basu hanya suka shiga har falon gidan dukan su anan suka zauna ,babu daɗewa wata ƴar matashiyar dattijuwa ta fito akalla zata kai shekaru 55 ,dan sosai dan zata girmi Ammi ,kuma dai yanayin jin daɗin ba ɗaya ba ,duk da suma ɗin da gani suna da nasu rufin asiri sedai Bama zaka haɗa da nasu Ammi ba. "Lale marhaban yan biyu kyautar Allah, yau kune a gidan mu sannun ku" abun da take faɗa kenan har ta zauna ,dukansu rusunawa sukayi suna gaishe ta ,cike da jin daɗi ta ke amsasu " Amra kije ki kawo musu ruwa mana "tashi tayi babu bata lokaci kuwa ta kawo musu Ruwan ,ita dai Meerah ,kusa a makure take zaune ,dan duk se takejin wani iri A kunne Amrah tayiwa Rumaisa rada tana tambayar ta " wannan ko ita ce Yayan mu ze aura,na ganta kyakkawa da ita "tayi maganar so whisper ,kama baki Rumaisa tayi tana dariya se kuma ta kalli Mu'aisam ,harara ya jefa mata ,kamar yaji abinda sukace, tashi yayi yace " Umma bara na ajiye yarinyar nan se na dawo " adawo lafiya sukayi masa ,ganin yafice beyi mata magana ba ,se ta mike itama tayi musu sallama ta fita ,aiko suna fita Amrah da Rumaisa suka samu damar yin dariyar da suka kumshe ,kallon su Umma tayi cikeda mamaki tace " kuma lafiyar ku ,ko shegen gulmankun da kuka saba ne? Wlh Umma da rabon autar yarnan taki ta daku a gidan nan yau " Rumaisa ta faɗa tana sakeyin dariya " Haba waya isa yazo har gida yadaki yata me tayi ma da wani ze daketa ? " Hmmm Umma bakiji me tace ba wai wannan ce yaya ze aura? tasan dai halinsa ai" se kuma tayi kasa da murya "Allah kuma Umma da ta faɗa se nake ganin dacewar su ,dan kam Allah yayi mata baiwar kyau ,a haka ma dan basu da shi ,da ace sunada kudi wannan ta shafa mai me tsada ai wlh ba matar kanana bace " ita dai Ummah murmushi kawai tayi tace " to menene nikaina ai nazata surikar Ammi ce aka kawo ta gausheni ,kuma Kinga saura kaɗan na tambaya ganin dai kamar tanajin kunya ne yasa nayi shiru,ashe da se ya haɗamu duka ya daka ko?". " cab Umma ko kin manta sis Rufaidah ce yake so ,kuma tana matuƙar son sa ,dan Allah kudena zancen nan kar kujawa yar mutane wulaƙanci dan kuwa Ƴar aikin ta ce " zaro ido Amrah tayi tace "wai da gaske kikeyi wanann fine girl ɗin aiki takeyi wa Rufaidah ? Cab dama Yayanmu zece yana sonta ,naga yadda shegiya xatayi ,wlh nikam bana fatan ya aure ta ,nifa bana ma tunanin soyayya sukeyi kamar dai itace take wani iyayi ,musamman idan ta ganmu ,shegiya tana fama da dogon wuya kamar wata umbrella" kai Amrah bana son wulakanci a gabana kikeyiwa yar' uwara rashin kirki ,Kinga nikam inaso ya aure ta ,dan tana son sa a yadda na fahimta ze iya canza ta " taɓe baki Amrah tayi tace " hali ai zanen dutse ne ,bana tunanin zata canja ,any way Allah ya tabbatar mana da mafi alkhairi " yawwa ko kefa abinda Yakamata kice kenan tun farko". Koda Meerah ta fita har Mu'aisam yakai motor ,dan haka itama kai tsaye ta isa back seat ta buɗe ,har xeyi mata magana kuma se ya fasa ,tana shiga ya tayar da motar ,ganin

Table of Contents

Chapters

34 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34