Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 32

Chapter 32

Mabaraciya Book 1 Complete Hausa Novel 1,179 words 0 views Progress saved
Download Book

kamar xatayi kuka haka ta shiga ɗaki ta canzo hijab sedai powdern ne kawai bata shafawa turare ta ɗan fesa kaɗan kafin ta fito " kallon ta Aunty tayi tana girgiza kai " Allah dai ya kyauta miki Ameerah ke sam idan bakiyi niyyar abu ba to babu wanda ya isa ya saki kiyi "narai² tayi da ido kamar xatayi kuka" Kinga jeki ni karkimin kuka bawan Allah nacan kin shanya sa ,dan dai kawai so na so amma taya mutum ze jure duk irin wannan. Meerah tana fitowa ta ga motarsa ,dan haka ta dawo daga cikin zauren gidan ta tura masa text cewar ya shigo daga ciki ,koma tayi gida ta dauko ta barma tazo ta shimfiɗa masa ,itama se ta zauna daga ƙarshen shimfiɗar zamanta babu wuya se gashi ya shigo hannun sa riƙe da na yarinyar sa zauna wa yayi yana faɗin " anya jan ajinnan beyimun yawa ba Hajia kinsan tsawon lokacin da kika barni a zaune ina jiranki ,ni har nayi tunanin ma baxaki fito ba ,da se dai kiganni cikin gidanku" kawar da zancen tayi da faɗin " ina wuni" lafiya lau yakike nace dai bara naxo tunda na fahimci ko shekara zanyi bankira ki ba to ke baxaki taɓa nemana ba " murmushi kawai tayi tana janyo yarinyar zuwa jikin ta kusan dai yadda Meerah take da son yara ,to hakan ce ma ta faru tsakanin ta da wannan" ya sunan ki? Kallon Muhsin yarinyar tayi ,ya gyaɗa mata kai " ki faɗa mata mana itace fa Auntyn ki ina kece kk ce zakizo kigaishe ta" gaishe da Meerah tayi ,ta amsata tare da tambayar ina yayunta " Aunty Dadyn mu ne yace baze zo dasu wurin ki ba basajin magana" ayya dadynku be kyauta ba gaskiya idan kika koma kice nace suyi kuka harse yakawosu na gansu kinji? Dariya kawai Hanifa tayi haka tayita yiwa Meerah surutu ita kuma tana biye ta ,ganin haka Muhsin yace " yaudai nazama ɗan rakiya kenan ,naga anmanta dani ma a wurin se biyewa Hanifah kikeyi "dariya Meerah tayi tace " Allah kamar kabarmun ita Momyn ta zatabani? Taɓe baki yayi yace bansani ba sedai ko idan zaki tambayeta ,bara na kira miki ita se kiji daga bakinta "da sauri ta dakatar dashi " a'a Abban Hanifah ,to idan ta tambaya wace ce se na faɗa mata me? Au har an canja mun suna kenan ,aikam dai naji daɗin wnnan,karki damu ai tasan komai akan ki ,dan babu ɓoye ² a tsakanin mu tun ranar da na fara zuwa wurinki se da na sanar da ita ,kuma fatan Alkhairi kawai tayi mana ,Kinga yau ma cewa nayi ta shirya Hanifah zan zo da ita wurin ki, kuma ta shirya ta ɗin na faɗa miki mata ta bata da matsalar komai zakiji dadin zama da ita " taɓe baki Meerah tayi tace" nikam ai banda damuwa da hakan ,yanzu yaushe zaka kawo sauran yaran suma na gansu " uhmm to wani lokacin dai ,zasu zo su wunan miki ma " aikuwa da naji daɗi wlh " wai haka kike da son yara? Kinga kawai ki amince muyi auren mu da wuri Kinga next year i war haka kinsamu naki yaran maybe ma twins" rufe ido tayi tana dariya ,shima dariyar yayi ,dan ze iya cewa yaune rana ta farko da yake ganin dariyar ta irin haka har take bayyana haƙoranta , sedai ko yaushe tayi murmushi. duk wani tunani da Yakamata Hajia saudah tayi na neman hanyar rusa auren tayi amma ta kasa samun solution , shiyasa damuwa tayi mata yawa duk da tasan tunda Hajia Laura tace xatayi wani abu akai to xatayin sedai tunanin ta me Hajiya Laura zatayi wanda zesa Alh yace ya janye maganar auren kamar yadda ta faɗa ,tunda wannan abun ya faru ta kauracewa Alh ,sam bata bari ma su haɗu ,gefe ɗaya kuma ga tunanin da takeyi akan Meerah ,ita da tazo Kaduna ta ɗan kwana biyu kafin ta koma ,Sega wannan matsalar ta taso mata yazama dole tayi tabar garin ko dan saboda Ameerah ma da take wani tunani akan yarinyar ,tana cikin wannan tunanin ne sega Binta ta kira wayarta ,ɗagawa tayi jin yanayin Muryar Binta ne yasakata faɗin " lafiya? Hajiya wlh Alh Tanko ne yazo jiya to be sameki ba rabon ayi se na tura ɗaya daga cikin yaran nan takai masa ruwa ,shikennan fa kamar wani tsohon maye ya hakewa yarinyar mutane ,kuma na faɗa masa cewar naki ne kar ya taɓata amma bakiga illar da yayi mata ba seda yaga ta dena mosti daƙyar doctor Ali ya ceto rayuwar ta amma shikansa seda yayi faɗa" dogon nunfashi Hajia Sauda ta sauke tace "wacce daga cikin yaran yar farar ko baƙar? Ehhh Hajia Bakar ce "to yanzu dai ta farfaɗo ko? Ehhh har ma nasamu tasha tea yar uwarta se kuka takeyi " karki damu Binta ,zan kirashi muyi magana ,yasan dole ze biya duk abinda nace ya biya tunda be nemi izini na ba ,ina fatan anyi recording komai? Ehhh komai yana nan Hajia " To karki damu ,nima nan ɗin akwai yarinyar da nake harar mana duk da nasan bazan sha wahala ba dan na fahimci tanada son kudi ,ki kula da komai Binta ,kuma kitabbatar tana shan magani yadda ya kamata, abata kulawa ta Musamman dan nasan taji jiki ,ko wannan Tumbi na Alh Tanko kawai ai kayane ko ga mu manya bare ma wannan yar cikinsa ,ya gidan komai dai yana tafiya lafiya ko? Ehhh Hajia yawwa to ki kula sosai zan sake kiranki. tana kashe wayar ta saki murmushi tuna irin kuɗin da zata samu a hannun Alh Tanko ,shigowar Rufee ne yasakata haɗe fuska Tun kafin tayi magana tace " menene? Um.um Mama dama nazo ne na faɗa miki inaso zan fita ,akwai gidan ƙawata da zan tafi " to Rufaidah kinajin magana ta ne da zaki zo tambaya na ,ina ko cewa nayi bazakije ba ,zakijen tunda yanzu sam banda wani girma a idon ki ,ƙan kanuwa dake wai harkisan kizaɓi namiji akan uwarki " Haba Mama kidena faɗar hakan nifa bawai na zabeshi akanki bane Mama inaso kifahimci wani abu , keda Ammi matsayi daya kuke dashi a wurin Mu'aisam,amma saboda kilibibi irin nata ta kakance komai ,nasa sekace itace uwarsa ,nace ina son sane saboda na tarwatsa burinta ,dan nasan batada wani buri da ya wuce ganin Mu'aisam ya auri Rumaisa ,shiyasa nakeso muyi anfani da damar ,Kinga yanzu idan na auresa dole zan rabashi da ita ai kuma nasan zakiyi farinciki da hakan ,kinsani Mama ina kishin duk wanda be kaunarki ya kike tunanin wai saboda ra'ayin kaina zan aure shi ,duk wannan saboda ke ne " ganin irin kallon da Hajia saudah keyi mata ne yasakata yin shiru " ai bantaɓa sanin ke sakarya bace se yau ,anfaɗami ki ta wannan hanyar zan gurgurta Saudah to dalilin da yasa bazan bari ki auri Mu'aisam ba ni nabarwa kaina sani ,kuma kar kiyi tunanin mallakar sa ,dan wlh bazan bar hakan ta faru ba ,bakisan wanene shi ba baki kuma san abinda ke tsakanina dashi ,ba auren da zakiyi masa ne ze illlata rayuwata Rufaida,baze yiyu na zauna dashi a matsayin suruki ba ,dan

Table of Contents

Chapters

34 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34