Chapter 26
Chapter 26
wani muna funcine akayi ,tun wuri a warware maka dan narigada nayiwa ƴata miji " cikin tsawa Abba yace " ya ishe ki haka Saudah ,waike se yaushe ne zakiyi hankali ,ace a gaban yaranki ma bakisan ki kama kanki ba yanzu wannan abun da kikayi shine me? Haka kike so itama ƴar taki taje tanayiwa mijinta kome ,wlh kar ki kaini bango shirun da kika ga inayi miki bawai tsoron ki Nike ba kuma wlh idan kika sake furta kalma ɗaya a wurin nan to a yau ɗinnan zan ɗaura musu auren ba se gobe ba kuma kinji na rantse idan kuma kina wasa to ki tanka " duda Abba mutum ne wanda bayada damuwa amma fa idan ransa yabaci to yakanyi abinda yafi abinda ya faɗa ,kuma tasan idan ya ɗaura auren shikennan anshiga gabanta dan haka ta ja hannun Rufaidah da karfi suka bar falon. Mu'aisam ma jiki a mace yatashi ya fita ganin haka Rumaisa da Mimi harda su Nawwara ma suka fita duda itama zuciyarta babu daɗi. Yayi saura daga Ammi se Abba ,kallon yadda ranta yake a ɓace yayi ,se yanzu ne ya fahimci cewar be kyauta mata ba ,dan ya hango tsan tsar rashin jin dadi a idon ta ,cikin sanyi murya yace "Hajia" ɗaga masa hannu tayi alamar dakatar wa ,cikin sanyi murya batare da hargitsi ba tace " me zakace Alh hukunce ka zartar akan ɗanka ko to miye na wa se fatan alkhairi Allah yabasu zaman lafiya ,bazan damu ba kuma bazanji haushi ba ,tunda ba Mu'aisam bane yanunamin wariya ba ,na yau kawai an nunamin cewar banice na haifeshi ba ,bayan tsawon shekarun da wanann ya shafe a lissafina sedai inaso na tuna maka ,bakaine ka bani Mu'aisam ba bare kayimun katsalandan a rayuwar sa, sam ban amince da wannan haɗin ba sedai idan har shine yacemin yana sonta da bakin sa ,kamar yadda tayiwa ƴarta miji haka nima ɗana yanada wacce yake so" tana gama faɗar hakan ita ma ta bar falon Lallai kam be kyauta ba ya sani tunda har Ammi ta nuna fushin ta ,macen da xeyiwa rashin adalci kai tsaye amma bazata taɓa nuna fushi ba,dafe kai yayi yana jan tsaki. a ɓangaren Ammi ma tana barin ɗakin ,kai tsaye ɗakinta ta shiga ,zama tayi bakin gado ta fara tunanin rayuwar su ta baya Asalin labarin Alh Yusuf tsoho haifaffen garin Kebbi state ne a wani ƙauye da ake kira ɗakin gari ,mutanen garin dukansu fulani ne sedai irin baƙaƙen fulanin ne ,mafi yawanci mutanen garin ƴan boko ne kuma babu lefi sunada kudi sedai akasarin masu kuɗin basa zama a garin wasun su suna dawowa cikin Kebbi ne da zama wasu kuma Sokoto wasu Abuja ,kaduna da dai sauran su ,sedai sukan haɗu bikin sallah kowa yakanyi kokarin ɗaukar iyalinsa yaje sallah saboda basa son yaransu su tashi da rashin jin Yaren fulatancin ,duk da nasu Yaren yasha banban da na sauran Fulani ,kamar dai yadda kuka sani ko a fulanin akwai banbancin yare Alh Yusuf su 3 ne a wurin iyayen duda matan Babansa biyu amma ita ɗayar Allah be bata haihuwa ba ,shine Babba se kaninsa Yahuza da yake zaune a nan cikin Kebbi se kanwar su Bilikisu ,wacce take aure a Kaduna Anan cikin garin su yayi auren fari wacce ta kasance itace uwar gidan sa wato Zainab (Ammi) ita ta kasance farar macece kyakkawa ,sam bata kama da mutanen garin wanann ya samo asali ne kasancewar babanta ne ɗan ɗakin gari amma Mahaifiyarta fulanin Gombe ne ,kuma ita ɗin kamannin mahaifiyarta ta kwaso. Kasancewar ta fara yasaka hankalin samarin ƙauyen dawowa kanta ,da yake mace bata auren mijin da ba nata ba ,se gashi ta tsayar da Yusuf a matsayin wanda take so ,bayan anyi bikin su ne ya ɗauki matar sa ya wuce da ita a buja lokacin a can yake zama suna zaune cikin lfy da soyayya sedai matsalar da suka fara fuskanta shine ra shin haihuwa ,dan kuwa yanzu shekarar auren su 7 kenan amma ko batan wata bata taɓa yi ba ,kusan ma itace me damuwar dan shi Alh Yusuf sabgogin gabansa ma sun hanashi zama ya natsu bare har ya fahimci cewar yakamata ya samu yara ,gashi yaki yaje asibiti bare agane matsalar daga ina ne duda ita tasha zuwa ana faɗa mata lafiya lau take lokaci ne de beyi ba ,ana haka kwatsam ,yace zasu baro Abuja su dawo Kaduna da zama ,hakan yayi mata daɗi dan a Kaduna kanwar sa take zaune da nata mijin ,harda yaransu guda uku, ko ba komai ta samu ƴar uwa ,tunda dama ita kaɗai iyayen ta suka haifa kuma Dukansu sun rasu tun bayan auren ta da shekara 3 babanta ne yafara rasuwa kafin mamanta ,se ta zama kamar batada kowa a ɗakin gari tunda dama babanta ne anan kuma dangin uba ba kowanne suke damuwa da lamarin ƴaƴan yan uwan su ba idan basa raye. yau da gobe bata bar komai ba segashi kwatsam Alh Yusuf yazo mata da zancen karin aure ,sosai ta ɗaga hankalin ta saboda tana tunanin xeyi aure ne saboda yaga ita bata haihuwa ,kanwar sa ce Bilkisu (Umma) take kwantar mata da hankali ,daga ƙarshe ta fawwala wa Allah komai ta saki ranta. Alh Yusuf ya haɗu da Sauda ne a wani kamfanin suminti lokacin yakaiwa abokin sa ziyara ,ita kuma tana kai musu tallan kaya irin su atamfa da lace da dai sauran su ,babu lefi itama tana da kyau duda ba fara bace kai tsaye baza'a kirata baƙa ba ,tana dakyau dai² gwargwado,yanayin wayewar ta yasaka shi tashin farko yaji yana sonta dan haka beyi kasa a gwiwa ba yasanar da abokin sa ,shine yashige masa gaba har komai ya daidaita. Kasan cewar irin mijin da take fatan samu ne dan zahirin gaskiya da abokin da take hari ,wato jogai shima ɗan asalin ɗakin garin ne ,amma ganin Yusuf ,se taji ta amince da auren sa musamman ma da taji labarin matar sa bata haihuwa ,haka take ta addu'ar Allah yabata ɗa namiji tana shiga gidan ,an ɗaura aure lafiya amarya ta tare daƙin mijin ta ,da farko dai zaman su lafiya lau ne kasancewar Ammi ta kama girman ta ,duk da irin rawar ƙafan da mijin nasu yake yi akan Saudah haka take kauda kanta dan tasan komai na ɗan lokaci ne ,babu abinda beda iyaka a rayuwa matuƙar zakayi haƙuri to zakacin riba , Watan Saudah 3 a gidan Allah yabata ciki ,zo kaga murna wurin su su biyun ,a wannan lokacin kam Ammi ta kasa daure wa se da tasha kuka sosai dan a da tana tunanin ko Alh baya son haihuwa ne amma ganin irin ɗokin da yake yi akan Sauda se abun ya taba xuciyarta , ga wani tsirfa da ta tsiro wai ita yanzu tsoron part ɗinta take bata iya kwana ita kaɗai sedai ya rika kwana da ita ,haka ya ajiye kasuwancin sa ,ya dawo gidan kaco kam ,ya roki Saudah akan tayi hakuri ta yafe masa kwanan ta saboda Saudah tana bukatar kulawa ,Allah ya raba lafiya kawai tace masa ,daganan ta fita sabgar su da safe dai xe shigo ya dubata ,daganan kuma se wata safiyar , wannan damuwar da
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34