Chapter 28
Chapter 28
tana tambayar lafiya? Se kawai tafaɗa jikinta tana fashe wa da kuka, anan ta sanar da ita kyautar da Allah ya bata , aiko sosai Umma tayi murna ,a nan gidan ta wuni ,seda ta kwatanci Mu'aisam yakusa dawowa daga school kafin tayi wa Umma sallama ,bayan ta gargadeta akan dan Allah ko Alh bataso ta gaya wa ,tanaso ne idan cikin ya bayyana kansa se su gani ......... Comments and share Dan Allah Real Bazamfaria ce ❤️ *INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION* ( *On* *word* *together* ) *MABARACIYA* *Story* *and* *writing* *By* *FIDDAUSI* *SANI* (damsel feedorh) 🅿️:2️⃣2️⃣ cikin farin ciki Ammi ta dawo gida ,xuciyarta wasai lokacin da ta sanar da Mu'aisam cewar zata haifa masa ƙanwa shima ba ƙaramin murna yayi ba dan kusan yafi kowa jin haushin gorin da Sauda keyiwa Ammin sa ,sam babu wanda yasan da zancen cikin a gidan saboda dama shi Alh Yusuf a satin yayi tafiya kuma xe ɗauki lokaci kafin ya dawo ,ita kuma Saudah ba shig sabgar Ammi takeyi ba ,hakanne yabata damar rainon cikin ta cikin kwanciyar hankali A kwana a tashi babu wuya sega cikin Ammi har ya shiga watan haihuwar sa ,a kuma lokacin ne Hajia Sauda ta yaye Rufaidah,saboda ƙawayen ta da suka dameta akan yakamata ta cire yarinyar a nono ,dan bazataji daɗin kasuwanci da ita ba ,ta amincewa shawarar su kuwa tunda itama bazata so ta fara yawon garuruwa tare da ita ba ,saboda haka se ta ɗauko nernny da zata riƙa kulan mata da ita A ranar da Alh Yusuf ze dawo a ranar Ammi ta tashi da naƙuda ,dan haka bata faɗa wa kowa ba se ta saka Mu'aisam ya haɗa mata kayanta a jaka ,tace yayiwa driver magana zasuje asibiti ,babu ɓata lokaci kuwa suka isa a sibiti dan lokacin haihuwar bata kankama ba koda likita ya duba se yace tana 2cm dan haka zata iya koma gida ko zuwa ƙarfe huɗu ne se su dawo ,ƙin yarda da hakan tayi dan gani take kamar wani abu ze iya faruwa da babyn ta idan ta koma gida , Mu'aisam kam driver yasa ya kaishi gidan Umma dan ya manta be ɗauko wayarsa ba ,lokacin da ya sanar da Umma cewar Haihuwa Ammin sa xatayi har ma sun kaita asibiti ,babu ɓata lokaci ta shirya itama ,dama drivern yana jiransu shine ya maidasu asibitin. Kafin wani lokaci kam Ammi ta fara fita hayyacin ta , addu'a kawai takeyi dan a tunanin ta mutuwa xatayi iya tashin hankali Umma da Mu'aisam sun shiga ganin har 8pm bata haihuba kamar ma ƙarfin ta ya fara ƙare wa se kawai ya fara Kuka " Haba Mu'aisam ba kuka zakayi ba kaji anfara kiran sallar jeka kayi ,daganan se kayiwa Ammin ka addu'a Allah ya sauketa lafiya kaji? Umma ta faɗa tana shafa kansa ,jiki a mace ya tafi masallacin ko bayan angama Sallahr shi be fito ba se nafila yakeyi idan yazo sujada se yayitawa Ammi addu'a Allah yabata lafiya yasa ta haifa masa kanwar sa ,bashi ya baro masallacin ba se 9pm ,zuwan sa yayi daidai da lokacin da wata nurse ke cewa Umma ta kawo kayan babyn Allah ya sauketa lafiya ta samu baby baby girl. Alhmdulilah kawai suke furta wa shida Umma ,cikin dan lokaci aka gyara Umma da kyakkyawar babyn ta wacce ta ɗauko hasken fatar mahaifiyar ta,aikam Mu'aisam se murna yake yakama babyn ya ƙankameta se sannu yake jerawa Ammi da ke sakar masa murmushi,kallon Umma tayi tace " Alh kuwa ya sani? " se Alokacin ma ta tuna da basu sanar da kowa ba ,da sauri ta ɗauko wayarta. Tun misalin ƙarfe 4pm Alh Yusuf ya sauka gida ,ganin part ɗin Ammi a rufe ne yasaka shi sauka wurin Saudah wanda hakan yayi mata daɗi ,bayan ya huta ya kira wayar Ammi dan yaji ina ta tafi,amma wayar tana ringing sedai ba'a ɗagawa ,sosai hakan ya bashi mamaki saboda haka ya tambayi Saudah ko ta san inda Ammi take" hmmm Alh ni ina zan sani tunda kaine ka ɗaure mata matukar baka garinnan to itama bata zama ,tun safe take fita bata dawo wa gidan nan se dare ni tsoro na ma su waye ke kawo ta a motor ,karta bata maka sunan gida kuma idan hakan ta faru nice zan kwana a ciki dan ni nake da ya'ya mata ,hakan ze taba mutunci su " Da ido kawai Abba yake binta dan ya rasa inda kalaman ta suka dosa ,shide yasan Ammi baza taɓa cin amanar sa ba ,sedai kuma ba'a shedar mutum ,dan haka ya sake ɗaga waya dan ya kirata ,Sega kiran Umma ya shigo ,da sauri ya ɗaga ,yana tambayar ta ko Zainabu tazo gidan ta "Ehhh muna tare sedai ba'a gidana ba muna asibiti" asibiti? Ya faɗa da yana tashi tsaye " waye beda lafiya ita ko Mu'aisam?kwantar da hankalin ka kowa lafiya lau ,idan da dama ko zaka iya zuwa ka ɗauko mu dan anbamu sallama "to to kujirani gani nan zuwa ,yana kashe wayar yafara laluben keys ɗin sa "wai Alh ina zakaje ne naga duk ka firgice , lafiya? da sauƙi dai Saudah duk da Bilkisu bata faɗa min me yake faruwa ba ,amma dai suna asibiti ,nasan dai Zainabu ce babu lafiya ,amma tace har anabasu sallama ,to kijiramu yanzu zamu dawo tare da su " da sauri yafita Tsaki tayi tana faɗin " aikin banza ,Allah yasa kafin ma yaje ace ta matu, duk kowa ya huta ,a ce mace baya karuwa da ita amma matuƙar akayi maganarta to yanzu zakaga yana rawar ƙafa,ko da yake wayafi fulani bin bokaye ,shegiya me kama da bararo. daskarewa Alh Yusuf yayi lokacin da Umma ta ɗora masa jaririyar da Ammi ta haifa wai da sunan yarsa ,yakasa gasgata hakan to yaushe ma ta samu cikin be sani ba " kayi mata addu'a mana Alh"maganar Ammi ta dawo dashi duniyar Mamaki ,hawaye ya goge yace " Allah ya albarkaci rayuwarta Zainabu ,haƙika nayi matukar murna da samun iri daga tsatsonki ina fatan zaki bata tarbiya irin taki ,ina kuma roƙon Allah yasa buɗewar haihuwar kenan a wurinki ,nayi murna sosai ,dan haka kifaɗi duk abinda kike so ni Kuma nayi miki alƙawarin zan mallaka miki "haba Alh ni bana son komai ,dan kuwa duk wani abu da mace zata bukata a wurin mijinta to na samu abu ɗaya ne ,nake roƙo ka daure kayi adalci a tsakanin ya'yan ka inajin tsoron banbancin da kake nunawa a tsakanin na da Saudah ,matuƙar ka nuna shi akan yata, zuciyata bazata iya ɗauka ba ,dan kuwa a duniyar nan banda kowa se su biyun nan Mu'aisam da ita ,dan Allah Alh ka kulamin sa su koda bana raye " ta faɗa na share hawaye ,da alama ta taɓo abinda keyimata ciwo ne a zuciya " A'a Zainabu kina raye ma tare zamu kula da yaran mu da wa'yanda zaki sake haifa mana nan gaba ,Kinga yanzu dai ku tashi mu isa gida ,naji dalilin ɓoyemin wannan abun farin cikin da akayi tun farko "dariya sukayi dukan su suka rankaya zuwa gida. tashin hankali wanda ba'a sa masa rana ,wannan daren daƙyar Hajia Sauda ta runtsa ,tsabar baƙin ciki ,bayan tayiwa Alh tijara son ranta ,da farko cewa
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34