Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 12

Chapter 12

Mabaraciya Book 1 Complete Hausa Novel 1,204 words 0 views Progress saved
Download Book

kamar yadda ta saba seda tayi nisa sosai kafin ta samu a caɓa ,ka san cewar safiyace sosai,unguwar da xe kaita ta faɗa masa ,babu ɓata lokaci tahau suka tafi. Koda ta kai sa sashen su Rufaidah a rufe yake alamar bata tashi ba kenan ,tasan ko tayi knocking ba ji xatayi ba saboda haka ta samu wuri daga gefe ta zauna ,takai kusan 30 minutes,kafin taji maganar Larai a kanta ,ɗagowa tayi tana kallonta " Fatima me kikeyi anan baki shiga kin fara aikinki ba?"instead ta amsa mata se tayi murmushi tare da gaisheta, amsawa tayi tana sake maimaita tambayar " wlh Aunty Nazo naga kofar a rufe shine na tsaya nan kafin a buɗe" Kama hannunta Larai tayi tace " to ai tanan baya zaki shigo ,mutafi kina ɓata lokaci ,bakisan halin me gidan bane"Meerah batace komai ba tabi Larai suka shiga ,tsaye tayi tana tunanin inda zata fara gyarawa ,can dai tayanke shawarar fara gyaran falo kafin fitinanniyar can ta tashi ,se ta shiga ta gyara mata ,sunan da ta sakawa Rufee kenan. Seda ta tabbatar da ta gyara ko ina a downstairs,tukuna ta kai dubanta ga agogon da ke manne a bangon falon karfe 8:30 ya nuna mata ,a fili ta furta " ko ma tayi sallah? sedai tunanin batada me amsa matane ya sakata nufar kitchen wurin Larai " sannu da aiki Aunty" murnushi Larai tayi mata " harkin kammala gyaran kenan " ehhh iya kasanne da ɗakunan da ke ciki ,ina tsoron na haura sama ne bansani ba ko bata tashi bacci ba" cab!ai se 10 zata tashi " taɓe baki Meerah tayi tace " to bara na tayaki aiki kafin ta tashi" a'a wlh da kin barshi ai ma na kusa kammalawa,kunun gyaɗarnan ne kawai yayi saura "ehhh ai ko wanke² ne se nayi Miki ,naga kinyi abincin kashi²,hala duka gidan ke kike musu a binci? " Hmmm ko ɗaya Meerah kinsan musu kuɗin nan sam basu san tattali ba duk wannan da kikaga nayi na Hajia Rufaidah ne ,yanzu ma idan ta gadama zata iya cewa duk babu abinda yayi mata ,sedai na canja wani" cike da mamaki Meerah ta kalli Larai tace " kuma se kin sake ɗin? "to yarnan zamanta nikeyi a gidan nan fa dole na canja idan tace beyi mata ba" can!amma wallahi....bata karasa ba sakamakon tsawar da sukayi from no where,cikeda rashin mutunci Rufaidah tace... "Larai badai abincin da zanci bane kika bari wannan me suffar aljanu ta taɓa?" A'a ranki ya daɗe yanzun nan ta shigo ma har na kammala komai" itadai Ameerah tsaye tayi tana binsu da ido musamman Larai da jikinta har shecking yake tsabar tsoron Rufaidah,wani dogon tsaki taja tana maida idonta kan Meerah a wulaƙance tace " shishigin ki babu abinda ze ƙara Miki se tsana a xuciyata,idan ma ba kinraina ni bane har yaushe zakizo baki jira na tashi bacci kin gyara min ɗaki ba ,kishigo nan kina abinda ba'a saka ki ba ,ok nasan saboda kwaɗayi kikayi wannan ko wato agama ki kwasa kikaiwa cima kwance iyayenki ko,su sun zauna sun turoki aikatau wayasani ma ko da shegen kyan nan naki zasuyi anfani kun zata ko akwai maza a gidan nan ,to ahir ɗinku ko munada maza sunfi ƙarfin matsiyata irinku"ta ƙarashe tare da kafe Meerah da ido dan ganin duk wannan maganar da ta faɗa mata murmushi ne kwance a fuskanta kamar ma bata fahimci zagin da takeyi mata ba ,ganin tayi shiru ne Meerah ta raɓa zata wuce ta batare da ta furta komai ba , da sauri Rufee ta fizgota ta dawo baya " Who dere you ina magana zaki wuce ,wato kam ga Mahaukaciya ko?nan ma shiru Meerah tayi tana kallon ta kamar bazatayi magana ba se kuma tace " Ai bansan amsar abinda kika faɗa kike nema ba shi yasa nayi shiru ,amma tunda har kin buƙaci haka inaso kisani ,duk yadda iyaye suke sunan su iyaye, Bara na tambayeki menene ma'anar iyaye? nasan baki sani ba saboda bakisan daɗin su ba ,abinda kika sani kawai ,kinada buƙata abaki kuɗi kiyi ,anfaɗa Miki komai ne kuɗi keyi akwai farin cikin da kuɗi bazasu baki ba ,amma kulawar iyayenki kawai ya wadatar dashi ,kamar yadda kika ce iyayena matsiyata ne to ina so ki gyara kalaminki ,domin mu arziƙin imani kawai da Allah yayi musu ya ishemu alfahari ,kyau da kike magana kuma ,naji daɗi tunda duk rashin sonki gareni ,idonki be rufe ba har seda ya tabbatar miki da Ni ɗin me kyau ce ,Kinga akwai yiyuwar idan gidan da Nazo babu maza to matan ciki su taya ko? Cikin zafin rai Rufee ta ɗaga hannu zata mari Meerah da sauri ta kauce ,tana dariya ta fita daga kitchen ɗin Ba Larai da tayi mutuwar tsaye ba hatta Rufee ta kasa motsi ,babban baƙin cikinta a gaban Larai Meerah tayi mata wannan iskancin , lalai dole ne ta ɗauki mataki akan ta ,amma zata fara kiran Fatima ta sheda mata kafin suyi shawarar irin tozarcin da zasuyi mata ,dan tayi alƙawarin se tayi nadamar zuwanta duniya. Meerah kam xuciyarta wasai taketa gyaran ɗakin duk da wani ɓangare na xuciyarta na cikeda tsoron kar Rufee ta koreta, tun kafin ta fara abun da ya kawota ,gashi ma ko maganar Hajia saudah bataji anayi ba bare ta saka ran ganinta ,haka dai ta samu ta kammala komai har toilet ta wanke mata se kanshi ke tashi a ɗakin ta janyo mata ƙofa ta rufe ,har zata sauka se takai dubanta ga ɗayar ƙofar dake rufe ,tanason ta shiga ɗakin duk da zuciyarta na faɗa mata cewar ɗakin Hajia saudah ne ,jin kamar za'a hauro sama ya sakata saukowa da sauri ,sedai a mamakinta Rufee bata falon. More comments more typing Idan har comments ɗin ku ya burgeni to zakuci gaba da samun Mabaraciya ko yaushe Insha'Allah Vote and follow me Dan Allah Real Bazamfaria❤️ *INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION* ( *On* *word* *together* ) *MABARACIYA* *Story* *and* *writing* *By* *FIDDAUSI* *SANI* (damsel feedorh) 🅿️:1️⃣3️⃣ Fitowa tayi waje dan tsoron ta zauna falon kuma tayi lefi ,wurin wasu flowers ta samu ta zauna ,tunanin halayyar Rufee kawai takeyi ,wai dama haka wasu masu kuɗi ke rayuwa sam basu ɗauki talaka a bakin komai ba ,to me ke sa suna haka gata ko rashin tarbiyya? Kai gaskiya dai rashin tarbiyya ne meyasa mu lokacin ko masu yi mana aiki Ammi bata yiwa tsawa bare har mu muyi musu ,koda haline kowa da irin nasa"tayi nisa sosai a duniyar tunani har batasan da tsayuwar mutum akan ta ba,Mu'aiseen da tun da ta zauna yake wurin yake kallonta ganin kamar tayi nisa a tunani shine ya ƙaraso ,amma duk da haka bata san da tsuyuwarsa,ƙura mata ido yayi yana nazarin ta,be san me yasa zuciyarsa ke zargin yarinyar ba sam be yarda da ita ba ,gyaran murya yayi ,da sauri ta ɗago kanta ta dubeshi ,a jiyar zuciya ta sauke kuma se ta haɗe fuska ta raɓashi zata koma ciki "me kike tunani haka har Nazo baki sani ba? "Batare da ta waigo ba tace masa " Babu kawai taci gaba da tafiyarta,shima tafiyarsa yayi dama fita zeyi se ya hango ya ta fito shine yazo wurin ɗakin Larai ta tafi ,dan bata

Table of Contents

Chapters

34 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34