Chapter 22
Chapter 22
cike da farin ciki tace " Aunty Nagode miki sosai wlh naji daɗi , Insha'Allah babu abinda ze faru yanzu Bara naje nayi masa godiya ko ,dama tun ɗazu na shirya ke nake jira" a dawo lafiya Aunty tayi mata ta fita. Amamakin Meerah tana fita daga gidan ta samu motar Manager a kofar gida ,tabbas ta gane motar amma se tayi kamar bata gansa ba taci gaba da tafiyar ta , seda takai bakin titi tana shirin tsaida mashin se taga yayi parking a gabanta ,ɗauke kai tayi taci gaba da tafiya ,da sauri ya fito daga motar yasha gabanta " haba Ameerah wai ya kikeso nayi da kaina ne sam kin ƙi bani damar da zan samu kusanci dake ,ki yi haquri idan na takura miki amma wlh lefin xuciyata ne ina sonki ,dan Allah kixo kishiga na ajiye ki inda zakije se mu karasa maganar a mota" ganin idan bata shiga ba zeci gaba da binta se kawai ta bi bayanshi da kansa ya buɗe mata motar ta shiga sannan shima ya zagaya ya shiga ,seda suka ɗauki hanya yace " ina muka nufa? dama bakasan inda zanje ba amma shine ka dage seka ɗaukoni " Murmushi yayi yace " to ayi hakuri ni ai banki mu zagaye garin nan a haka ba saboda haka idan ma baxaki faɗa ba zanci gaba da zagaye dake " aikin naka fa? Uhmmm zan kira nace yau Madam ta hanani fitowa" bata lakacin da murmushi ya suɓuce mata ba ,harseda haƙoranta suka bayyana " haba koke fa ,kina da kyau idan kika haɗe fuska to ya kike tunani a lokacin da kikayi dariya? Cike da son kauda zancen tace " unguwar da ka ganni ranar can zaka kaini" kallon ta yayi cike da son karin bayani ,se dai ta kauda fuskarta gefe saboda Allah yagani bata son yawan shige matan nan da yake yi ,dan ita fa babu tsarin auren me mata a rayuwarta ,sedai abinda Allah ya rubuta a gareta. Har bakin get ɗin gidan yakaita,duk da ya dage akan se ya shiga da ita ,daƙyar ta samu yayi parking a wajen ,a xuciyar ta take ayyana dan besan matsayinta a gidan bane ,kafin tagama tunani taji ya sakomata tamabaya " me kike zuwa yi a gidan nan ? Da sauri ta kalleshi ,seda ta buɗe murfin motar kafin tace " Aikatau" daga haka ta rufo masa kofar ko waigowa batayi ba tayi knocking me gadi na buɗe mata ta shige da sauri kamar zata kife , A harabar gidan ta samu Mu'aisam yana karanta jarida ,sauri ta kara dan bata so ya ganta ,seda takusa shigewa taji saukar muryasa akanta " ke zo nan.......... Comments and share pls Real Bazamfaria ❤️ *INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION* ( *On* *word* *together* ) *MABARACIYA* *Story* *and* *writing* *By* *FIDDAUSI* *SANI* (damsel feedorh) 🅿️:1️⃣9️⃣ jiyowa tayi cike da addu'ar Allah yasa ba da ita yake ba ,kusan hakanne dan hankalin sa na kan jaridar da yake karatu ,bama zaka taɓa tunanin shine yayi magana ba "wata ƙil nice banji da kyau ba ,dagani ma beyi magana ba" abinda zuciyarsa ta gaya mata kenan aiko se taci gaba da tafiyarta ,har ta shige party ɗin da take aiki, hakan da tayi ba ƙaramin ɓacin rai ya saka shi ba ,idan akwai abun da ya tsana befi yayi wa mutum magana yajishi kuma ya share shi ba ,wanda ya kula ɗabi'ar yarinyar kenan duk lokacin da zakayi mata magana ko tambayarta kayi se tayi kamar ma bata ji ka ba "amma zan koya mata hankaki ai " daga haka yaci da abinda yake yi da sallama ta shiga falon ,sedai kamar kullum bata isko kowa a ciki ba ,dan haka kawai ta fara aikin ta ,tana cikin aikin ne Hajia saudah ta fito daga ɗakin Abba turus tayi tana kallon ta ,maganar da Abba yayi ne yasaka ta saurin amsahi cikin rawar murya " Saudah kema Kinga abinda nagani ko? cikin rawar Murya tace " me kenan? Nuna mata Meerah yayi yace nasan kema Kinga kamar "a'a ni banga komai ba ,kamar wa kuma kagani gareta " wlh Hajia ina ganin ta na tuna da Birrester,badan nasan da ya mutu be bar kowa ba kuma ba dangine da shi ba to da se nace tabbas wannan ɗin jinin su ce "kai Alh idon ka ne kawai yagane maka haka ,to taya ma wannan zata zama jinin su bayan Rufaidah ta faɗa min a titi take yawon bara shiyasa ma ta temake ta ,kaima kasan wannan batayi kama da masu arxiƙi ba " hakane kuma ,amma dai ni kam gaskiya naga kamar su ,ke bani ba ma nasan ko Hajia Ammi ta ga wannan zatace suna kama" Cikin fushi tace " to ko suna kama dai bance wata can ta rika shiga lamarin gidana ba ai koda basuyi kama ba zata iya cewa sunyi tunda har kai kace ,kasan ta da muna furci ,nikuma bazan faɗi karya kawai saboda na faranta ran wani ba ,kuma wlh wannan ƴar aikin dai tawa ce babu wanda ya isa yayi min shishigi a kanta" Shiru yayi yana sauraren ta ,mace kamar me aljanu to menene abun faɗa anan ,tun da ba wani yace xe ɗauke yarinyar yakai wani gu ba ,sanin idan yayi Magana zasu iya seda hali a gaban Meerah se kawai yace " to nide asamu a shiryamin abun kari da wuri na faɗa miki zuwa 10 fita zanyi bara naje mugaisa da su Ammi ko ? Taɓe baki tayi tace" banda damuwa da wanan kuma salon nayi magana kace na cika kishi kaidai wlh Alh kaji tsoron Allah ,mutum ya girma amma besan ya girma ba ko yaushe se rawar ƙafa akan mace mtsswww" ta barshi tsaye a wurin ,ita dai Meerah al'ajabi ne ya kamata ,a zuciyar ta take ayyana wane irin mutum ne Abba ,shikennan shi beda kataɓus a lamarin iyalin sa ,a fuska dai kaga cikakken mutum amma a zuci ba haka bane" ganin Hajia Sauda ta shige cikine ya saka Meerah saurin duƙawa tana gaishe shi " yauma dai babu lefi ya amsa mata fuska a sake "duk da yanayin da yaɗan sauya ,da alama abun da Saudah tayi ne ya taba zuciyarsa sedai yakasa nuna hakan a gabanta. Koda Hajia saudah ta shiga ɗaki se ta kasa zama ,xuciyar ta se saƙe² take ,wani tunani ne yazo mata ,se ta saki murmushi tana dauko wayarta ,lambar Hajia Laura ta kira ,bayan sun gaisa tace " Hajia Albushirin ki ,Kinkuwa san naci karo da wani zinari mai matuƙar kyau a gidan sedai da alama xeyi wuyar ɗauka ,dan na fahimci da zafin wuta a jikin sa ,ina tunanin ban taɓa samun zinari irin na wannan lokacin ba gaskiya "daga can Hajia Laura tace " ke uwar daba ,fayyacemun ingane me ze hanaki ɗauka idan ke kinajin tsoro ne ,ba gani ba kinsani bana tsoron komai yanzu ya za'ayi naga kalar design ɗin nasa kafin nasan hanyar da zamubi dan damƙeshi batare da wani matsala ba? " Uhmmm to bara ayi yadda aka saba bani some minutes ,zan turo Miki" kashe wayar tayi ta shiga wanka a gurguje ta fito ta shirya cikin wani doguwar rigar lace ,kayan ya amshi jikin ta dan
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34