Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 29

Chapter 29

Mabaraciya Book 1 Complete Hausa Novel 1,194 words 0 views Progress saved
Download Book

tayi " kai Alh to ka yarda ƴarka ce ,yama za'ayi ace ciki babu wanda ya san dashi se kawai su samo ya sukawo kuma kai kayarda dasu? Saudah ashe baki da hankali ban sani ba ,kina tunanin Zainabu zataci amanata ne kome? Nifa ba haka nike nufi ba ina nufin ɗai ba itace ta haife yar ba samota sukayi ,dan kawai idan ka mutu su ci dukiya " dakata dan Allah,zan iya shedar Zainabu a ko ina ita ɗin mace ta gari ce ,wacce bata damu da kuɗina ba niɗin dai ni take so ,kuma kar ki manta ba ita kaɗai ce ta haihu ba tare da yar uwata itace ma ta kaita asibiti ,kuma kece dai bakisan da cikin ba saboda baƙin hali yahanaki ganewa,amma tun samuwar shi ƙanwata ta sani ta zaɓi ta ɓoye abunta ne saboda gorin da kikeyi mata to gashi dai itama ta haihu ,saboda haka ki natsu kar ma Bilikisu taji kin fadi wannan maganar kinsani sarai ba shiru xatayi ba dan seki faɗa Zainabu ta shareki amma ita se ta tanka " kawai Alh kafito fili kace min kafison matar ka akaina ,har kake wani zancen ba dan kuɗi take zaune dakai ba ,ni ma ban aure ka saboda kudin ka ba ai ,haihuwa ce dai kafin tayi nice na fara yi ba ɗaya ba ma ,kuma zanci gaba dayi se naga tsiya "haka tayita borin kunyarta ganin ya juya mata baya yasaka ta fita daga ɗakin tana bambami Washe gari kam sega mutanen Ɗakin gari sun iso harda matar kaninsa Yahuza da bata taɓa zuwa Kaduna ba duk haihuwar nan da Saudah tayi ,segashi wannan karon sune sahun gaba a yan zuwa barka ,wanann abun yayiwa Ammi daɗi dan itama dangin Babanta su 3 sun zo sauran dai kam duk dangin Yusuf ne ,dan shine ya tura diver da babbar mota yace duk ne zuwa ya ɗaukosa. Sosai abun ya taɓa xuciyar Saudah dan bata taɓa tunanin Alh zeyi wani dokin wannan haihuwar ba tunda dai itace tafara yi har guda biyu kuma mata ne ,bare tace ,ita kanta Ammi tayi murna sosai da ganin yadda Alh yake nuna musu soyayya da kulawa itada ƴarta ,da taci suna Rumaisa Haka Kullum gidan yake wuni cike da mutane ,saboda mutanen ɗakin gari Alh ya hanasu komawa yace sujira kawai idan anyi suna se amaidasu baki ɗaya ,matar Yahuza ce kawai ta koma itama zata dawo idan ana gobe suna ,Umma kanta kwana ne kawai batayi a gidan amma da ta shirya yara sun tafi school take zuwa idan sun tashi anan ake tura driver ya ɗauko su ,se dare take komawa gida saboda mijinta beda matsala. Ranar Suna kam anyi bidiri wanda daga ƙarshe Saudah rufe party ɗin ta tayi ,dan taso barin gidan ne seda Alh Yusuf ya tabbatar mata da matuƙar tafita to kar ta dawo masa gida kuma duk inda zataje karta fitar masa da yaran shi ,dan haka ma da kanshi yayiwa Nanny magana tayi musu wanka aka shirya su ,ya tafi dasu sashen Ammi ,ya kaisu ga dangi dan suma a san su ,dan yanajin tsegumin da sukeyi akan Saudah. Macen kirki ce za'a ce iyaye da ƴan uwan mijinta sun zo amma ta kasa zuwa ta gaishesu tsawon sati ɗaya,ga ko da wasa basuga ta shigo yiwa abokiyar zamanta Barka ba ,lallai kam sun tabbatar da Yusuf yayi auren bariki dama kaɗawa ba kunyane da su ba ,da yasan yana son ƙarin aure ai da se ya koma gida ya auro kamar dai yanda yayi auren fari "ire-iren maganganun da sukeyi kenan ,wanda shi kansa yasan Saudah bata kyauta ba sedai shi mutum ne da baya damuwa da abinda be ahafeshi ba a ganinsa ba dole se tayi mu'amala da dangin sa ba tunda shi take aure ba su ba , sedai baƙinciki da ta nuna akan samun Rumaisa ne abun ya tsaya masa arai. Kwana biyu da gana suna ,kowa yakama gaban sa ,gidan ya dawo kamar ba'a taɓa taro ba ,da Abba ze koma aiki yace ze nemowa Ammi Yar'aikin da zata riƙa tayata saboda yanzu abubuwan ze yi mata yawa ga raino ga kula da gida ,sedai fir taƙi yarda saboda ita sam bata da ra'ayin masu aiki a gidan ta ,tafiso takula da yaranta dan samun shaƙuwa da soyayya ,abinci kuma bazata ci na masu aiki ba , sharane se mofin dama Mu'aisam keyi mata ,to saboda haka bataga dalilin tara mata a gidan ta ba ,da wanna taci gaba da kula da yaranta kwanan ta 40 da haihuwa itama Ummah ta haihu ta sake haifar mace ta ci suna Amrah , bayan tayi 40 suka shirya itada Ammi da yaransu suka tafi ɗakin gari ,wanda shine zuwan Ammi na farko tun bayan barin ta garin. Haka rayuwar sa taci gaba ,tsakanin ta da Saudah se ido ,idan kuwa magana ta haɗa su to Khadijah ce ta shigo sashen Ammi shine fa Saudah zata biyota tayita zaginta, kuma baze hana anjima yarinyar ta sake shigowa ba ,saboda tana son Rumaisa idan ta shigo haka take zama tace Ammi ta goya mata ƙanwarta ,ita kuma Ammi ta goya mata ,kuma duk jarabar da Saudah xatayi baze hanata kula Khadijah idan ta shigo ba ,a cewar ta ita takawo kanta ba itace ta kira ta ba . shekarar Rumaisa 7 ,lokacin ita Rufaidah tana cikin na 9 amma cikinsu babu wacce ta sake yin ko ɓarin ciki ,kuma hakan yayiwa Saudah daɗi dan tana tsoron ace Ammi ce zata haifi na miji ba ita ba ,gashi itakuma ba son haihuwar takeyi ba ,dan yanzu ma rabonta da wani muaamalar aure ya haɗa ta da Alh har ta manta dan kuwa baya gabanta a cewar ta ,tana samun fiye da abinda zata samu a wurin sa ga kuma kudi da suke shigo ta ,to miye matsalar ta bayan wanann ? Sedai abinda bata sani ba ita kam Ammi tana ɗauke da ciki har na tsawon 3 months ,wannan karon kam da wuri Saudah ta falga dan babu lefi cikin yazo mata da laulayi ba kamar na Rumaisa ba ,iya tashin hankali ta shige shi ,tana shirye shiryen yadda zata barar da cikin ,wata ƙawarta ta gayyace ta biki Niger , wanda zuwan ta Niger ya kara sauya mata rayuwa dan ta haɗu da manyan mata masu ji da kuɗi ,anan take koka musu halin da take ciki na kishiyar ta tana da ciki kuma tana tsoron ta haife namiji " ke miye naki idan ta haife namijin? Yanzu fa andena dogoro da dukiyar namiji dan ba ƙaramin raini hakan yake janyo wa ba ,tashi zakiyi kinemi naki, idan kinso ma har shi mijin se kin fishi kuɗi" anan suka dorata a seti ,se ta watsar da zancen cikin Bayan wata 7 Ammi ta haihu wannan karon ma macecen ce ,taci sunan Mahaifiyar Abba Mariya suke kiranta Mimi. Wannan karon Ammi bata wani daɗe ba dan Mimi tanada shekara 2 ta samu ciki ,ta haife twins Mace da Namiji ,wanann karon kam Alh Yusuf yayi bikin da be taɓa yi ba ,hakika jahar Kaduna sun sanda samun magaji da yayi anyi shagali an kashe kuɗi Saudah ta kasa ɓoye bakin cikinta, wanda har se da tayi

Table of Contents

Chapters

34 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34