Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 8

Chapter 8

Mabaraciya Book 1 Complete Hausa Novel 1,197 words 0 views Progress saved
Download Book

nafara imagination,yanda zasusha tsutsa gun......"dakata Asabe Hajia Saudah ta katseta cike da fushi taci gaba da magana"me yasa wai ke Sam bakida tunani ko kinsan wacece wannan din to 'yatace Rufaidah wacce kaf itace duniyata ,lalacewa ta bazesa itama ta lalace ba ,saboda haka ,zanmuku alfarma daya ,akwai yaran da nayiwa kaina tanadi ,amma zan barmuku kuji dadinsu banaso wata ta sake yabon surar'yata ,tafada babu alamar wasa a fuskanta Sage sukayi suna kallon ta cikeda mamaki ,shin ko ta mance a tafiyarsu Babu nuna wariya kuma itama ai lokacin da taga 'yar Hajia Larai haka ta kunace seda ta lalata rayuwar yarinyar wanda shine sanadin yanzu yarinyar ma bata 9ja , domin da ta gwane a harkar tace sedai tayi da Jan fata domin sun fi iya luv ,babu kukan da Hajia Larai batayi ba ,amma tanaji tana gani tayi nesa da 'yarta domin tunda ta fahimci mahaifiyarta ma batada tarbiya se ta dena jin maganar ta baki daya kasancewar dama mahaifinta baya raye Hajia Asabe zatayi magana ,Larai ta girgiza mata kai alamar kartace komai ,shiru tayi tare da kitsima abubuwa da yawa ta yanda zata mallaki Rufaida, domin tariga ta kwadaita wa kanta ita kuma tayi alkawari ko ta halin ya se ta samota matsalar dayace sam Saudah bata basu damar sanin familin ta ba ,saboda tana da matukar wayo shiyasa ko yaushe sedai ta nuna musu ai business ne yahada su saboda haka no need ace se sun san komai nata ,duk tunaninsu itadin bazawara ce ,domin duk lokacin da mijjnta ze zo wurinta to bata yarda kowa yazo mata gida ,takanyiwa mai gadi warning akan kowa yazo yace bata garin Sosai Meerah tayi murna dajin Rufaida ta yarda zata dauke ta aiki ,bata damu da komai zata fuskanta ba ,kawai dai burinta ,Hajia Saudah ne ta dauki fansa ,sedai jikinta yayi sanyi tunawa da aunty da tayi ko ya zata dauki al'amarin ,cikeda sanyin jiki ta nufi dakin ta da sallama ta shiga ,se kuma tasamu wuri ta zauna cikeda mutuwar jiki ,dan dagowa aunty tayi ta dubeta ,cike da kulawa tace "ke kam lafaiyarki ,shiru tayi kamar bazatayi magana ba ,se kuma tace " Aunty a musulunci ma an yarda idan mutum ya cutar dakai ,kuma bazaka iya hakura ba to karama dai dai da abunda yayi maka amma yafiyar ita tafi domin Allah ya tanadi wata kofa a cikin aljannah wanda yayi alkawarinta ga wanda yayi hakuri a inda yakeda ikon ramawa ,sedai duk ba wannan bane dalilin,daukar fansa na ba ,sedan na kubutar da 'wayanda zasu shiga komar Hajia Saudah nan gaba ,wayanda take anfani da 'dayar fuskarta na mutunci,tana keta haddin yaransu ,kimun fatan nasara ,domin cikin kwanan nan zan fara shiga gidan Saudah a matsayin 'yar aiki ,banaso na dauki lokaci a gidan ,ajiyar zuciya aunty tayi tace " Allah ya zama gatanki ya kuma tsare miki mutum cinki daga haka bata sake cewa komai ba .sosai Meerah taji dadin goyon bayan aunty da ta samu cikin sauki ,saboda haka ta turawa Fatima text din zata iya fara zuwa ko yaushe ta tambayi Rufaida...... *Comments nd share pls* #follow me on wattpad@damselfeedo #Real@Bazamfaria💘 *INTELLIGENT* *WRITERS* *ASSOCIATION* (On ward together) *MABARACIYA* *Story* *and* *writing* By *FIDDAUSI* *SANI* (damselfeedorh) 🅿️:1️⃣0️⃣ ,,,,,,,,Washe gari Rufaida da kanta ta kira Fatima a waya sosai tashiga mamakin ganin kiranta sedai ba ta nuna fa ,daga can Rufaida tace "Fatima ya naji shiru? Murmushi ya subucewa Fatima ba tare da ta shirya wa hakan ba har seda Rufaida taji sautin shi ,cike da mamaki tace" yadai kike dariya ? Dole ne nayi dariya Fatima wai kinsan yarinyar nan taso ta ganeni"wace yarinya ta tambaya ,don ita har ga Allah batasan akan wacce take magana ba "Mabaraciya ,Fatima tabata amsa a takaice " ok to yanzu ya kukayi da ita " ehhh to kinsan ko cikin talakawan wasu basuda kwadayi da fari yarinyar da mahaifiyar ta kin amincewa sukayi wai ita bazata seda mutunci 'yarta saboda kwadayin abun duniya ba ,shinefa na samu mahaifinta ,na nuna masa irin Alkhairan da zasu samu a cikin aikin nan ,tukuna yayi tsayin daka akan dole se tayi aikatau ,cikeda jin haushi Rufaida tace " wai me suke takama da shi nikaina idan badan saboda na dauki fansa bane me zanyi da aikin ta yanzu ma kawai inaso na koya mata darasine ,idan na fahimta halin uwarta ne ta gado na ganin dede suke da kowanne'dan adam , murmushi tayi mai sauti cikeda jin ita din watace tace " point of correction cox totally akwai distance sosai a tsakanin mu , mabaraciya wacce abunda zataci ma se tayi yawo ta nemo kuma hakan wai iyayenta da ita suka dogara ta zame musu bango ,dole zan nuna mata wacece ni 'yace wacce ko kiran sunan mahaifiyata akayi dole mutum ya natsu domin yasan ta Tara abun duniya despite my father Shiru itadai Fatima tayi tana sauraren ikon Allah ,a ranta take tunanin wane irin girman kai da takama ne ke damun Rufaida,tabbas rayuwar wasu a kwai gyara ,duk da ta ta'allaka hakan da rashin samun rarbiyar uwa da batayi ba ,kowa yasan Hajia Saudah yakuma san irin Alkhairan ta ,da yanda take taimako da son jama'a ko kadan Rufaida bata gaji halinta ba Farar tukunya kenan mai fidda ba'kin tuwo ,Fatima na cikin wannan tunanin ne tani 'kit alamun ta yankee kiran ,bin wayar tayi da kallo tana tunanin shin wace kaddara ce ke kiran Meerah aiki a karkashin wannan da bata gaji mutum ci ba ,tana cikin tunanin ne wayarta ta sake ringing ganin sunan Meerah ya sakata dagawa ,da sauri ,tambayarta Meerah tayi akan yaushe zata fara zuwa " even tomorrow,tabata amsa jiki a sanyaye ,wani irin dadi Meerah taji ,sosai tayiwa Fatima godiya sanann ta yanke kiran Meerah na zaune dakinta tayi tagumi ,da alama tunani takeyi ,shigowar aunty ne yasakata dawowa daga duniyar tunanin ,kallonta tayi tasakar mata murmushi tare da matsawa daga gefe saboda ta samu wurin zama " kinga ba zama ne ya kawoni ba ,aikenki nakeso nayi kasuwa,sedai naga yamma tayi ina tsoron kitafi kiyi zamanki nasan halinki " kai aunty se kace wata yarinya ,da zan tafi na zauna a titi ,kedai kikawo sakon kawai yanzunnan zan dawo Insha'Allah " yawwa to kishirya se ki sameni a 'dakina aunty tafada tana fita dakin ,tashi Ameerah tayi kayan jikinta kawai ta sauya daga riga da wando zuwa bakar jalabiya sosai tayi kyau ,kamar ba Meerahn da na Sani ba saboda sak ta fito yar gayunya harta yane kanta da dan karamin vail na rigar sekuma ta sauya zuwa hijab red colour Masha'Allah Allah ,tayi kyau sosai abunda ,cikeda na tsuwa ta shiga dakin aunty ,sakin baki aunty tayi tana kallonta har seda tayi kasa da kanta don taji kunyar kallon da aunty ke binta da shi Cikeda xolaya Aunty tace " Masha'Allah Meerah kinganki kuwa ,idan a hanya na ganki ai bazanxe wannan Meerah ta bace tafada tana dariya ,Dan turo baki Meerah tayi tace" idan da bansan halin aunty na ba da se tafasan kai ,bani sakon nidai natafi ,dariya kawai Aunty tayi ta dauko kudin sakon tabata tare da fada mata abunda zata siyo ,sallama tayimata sannan ta tafi Adaidaita sahu ta shiga kasancewar

Table of Contents

Chapters

34 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34