Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 16

Chapter 16

Mabaraciya Book 1 Complete Hausa Novel 1,182 words 0 views Progress saved
Download Book

san hidimar da akeyi ba ,shiyasa tayi shirinta cikin atamfa riga da sket ,key din motar ta ta ɗauka ta fito ,daga falo take kwalawa Larai kira ,da sauri tazo ,abinda zata dafa mata da dare ta faɗa tana wani yamutsa face ,cikin girmamawa Larai tace " am Hajia fita zakiyi? Da ido Rufee tabita dan jin tambayar rainin wayo ,ya tana ganinta da gyale a hannu kuma take tambayar ta fita xatayi ,ganin haka yasa Larai fadin " yi hakuri dama gani nayi yau Alh ya dawo ,kuma nasan idan ya dawo dukanku babu wanda yake fita shiyasa Allah ya huci zuciyar ki " Larai kika ce Abba ya dawo fa? yaushe kuma ai ko shekaran jiya munyi waya dashi meyasa be faɗamin ba " ai dama nayi mamaki da naga yadawo baki fito nace kodai baki sani bane " lallai ba sunga Mama batanan ba shiyasa suka kwamushe sa a part nasu ,su muna fukai ,a jiye gyalen hannun ta tayi tafita cikin fushi. Motocin da tagani a fake harabar gidan ne yaƙara tabbatar mata da maganar Larai ,idan ranta yayi dubu to ya ɓaci ,saboda haka kai tsaye ta shiga party ɗinsu Mu'aiseen tana shiga duka hankalin su yadawo kanta , kasancewar lokacin duk suna hira ne a tsakaninsu da ido take bin kowanne daga cikinsu sedai bataga Abban ba ,ganin ko sallama batayi ba yasaka dukansu babu wanda ya tanka ta sema ci gaba da hirar su sukeyi ,haɗe fuska tayi ,cikeda rashin mutun ci take " se a wani tsare mutum da ido kamar ba'a san shi ba " ta karasa faɗa tana jan tsaki " ke Rufaidah iskancin ki ya tsaya can sashen ku ,wlh baxaki zo nan kinemi rainamana hankali ba " Rumaisa ta faɗa cikin fushi itama ,da ido Ammin su tayi mata alama da tayi shiru ,duƙar da kanta tayi kasa saboda a duniya idan akwai abinda ta tsana be wuce rashin kirkin da Rufee keyiwa Ammin su ba kuma idan zasuyi nagana se ta hanasu "ke Rumaisa yaushe nafara wasa dake da har zaki gayan magana ,ke kinsani ganina a part dinnann dalili ne badan Ubana da aka hanashi zuwa dubani ba saboda munafurci ,ai da babu abinda ze kawo ni anan ...bata samu karasa maganar ta ba saboda tsawar da aka daka mata ,ba ita ba hatta su Rumaisa seda sukaji tsoro ,cikin kakkausar murya Mu'aiseen da fitowar sa daga ɗakinsa kenan kunnunwan sa yajiyo masa rashin kunyar da takeyi yace " zan babballaki Rufaidah meyasa ke sam bakida kunya ne waye zeyi miki muna furci anan ,ke san bakisan ki girma ma kowa ba ko maza barnan"ya nuna mata hanya ,marairaicewa tayi saboda harga Allah batasan cewar yana gidan ba dan bata kula da motar sa ba ,dan duk iskancin da takeyi batayi a gabansa ,duk da yana da saukin kai amma matuƙar aka taba Ammi tofa baya sararawa kowa ,kuma ko bacin haka ,ita duk duniya babu wanda take so kuma take fatar ta aura kamar Mu'aiseen, dan kuwa ya haɗa duk wani abun da mace zata so a wurin namiji.tsawar da yasake daka mata ne yasaka ta saurin kankameshi tare da fashewa da kuka ,duka suka bita da kallon mamaki ,ganin yadda ta rikeshi kamar wacce zata shige ciki ,ko kunyar Ammi bataji ba Sannu da fitowar da taji yaran sunayiwa Abbane ya saka ta ɗagowa ta kalleshi ganinsa tayi cikin farar jalabiya,sajen fuskarsa ya sake kwantawa ,sakin sa tayi da gudu ta tafi wurin Abba tana kara fashewa da kuka ,jan hannunta Abba yayi ya zaunar kan kujera kafin shima ya zauna cikeda kulawa yace " me akayi wa ƴar shagwaɓa ta take kuka haka? Haba Abba yanzu shikennan saboda anga Mama batanan shine har zaka dawo gidan nan bansani ba kuma baka nemeni ba ,shi ne nashigo na gaishe ka Rumaisa tayimin Rashin kunya nayi magana shine yaya Mu'aiseen yake min tsawa " tasake fashewa da kuka Kallon Rumaisa Abba yayi yace " Rumaisa meyasa kikayiwa yayarki rashin kunya? Rasa abun cewa Rumaisa tayi se kawai tace " Abba tayi hakuri to ni ba rashin kunya nayi mata ba "dawo da idon sa yayi kan Mu'aiseen da yahaɗe fuska yace " Mu'aiseen kariƙa bincike kafin ka zarta hukun ci" haba Abba kasan me yarinyar nan tayi kuwa"Mu'aiseen"Ammi ta kira sunan sa ,batare da ya kalleta ba yace" ayi haƙuri Abba Insha'Allah zan kiyaye "yafadi hakanne dan yasan dalilin kiran da Ammi tayi masa kenan ,besake magana ba se kawai ya fita ya bar gidan dan ransa yagama baci Lallahin Rufaidah Abba ya shiga yi daƙyar ta yi shiru se kuma suka shiga fira ita da shi ,kamar babu kowa a falon ganin haka Ammi ta tashi tashiga daga ciki itama Rumaisa kama hannun su Nurain tayi suka shige ɗaki ,dan ranta yagama baci da abinda Rufee tayi . Rufaidah wai nikam ya zancen school kina zuwa kuwa? " Kai Abba na kammala fa 2 months kenan yanzu service kawai ya rage mana" kai Masha'Allah kice se aure kenan tunda angama karatu" dariya kawai tayi " so nikeyi na hadaku keda yar'uwarki na aurar duka na huta se naji da yan biyu na su Nurain" haɗe fuska tayi tace "nide gaskiya Abba baza'a haɗa bikina da kowa ba ,to yaushe ma ita ta girma duka duka fa yanzu take UG 3" dariya Abba yayi yace" lalai Rufaidah ko kunyata bakiji ba kike zancen baxaki jira Rumaisa ba , shikennan waye surikin nawa "lah Abba bawani bane fa a gidan nan yake" to ikon Allah waye nikam a gidan nan nide sani na ba bu wani namiji a gidan nan sedai masu yi mana hidma kuma nasan baacikin su bane "haba Abba dan Allah kadena ma zancen wa'yannan ai basa cikin lissafi" to shikennan dai yanzu faɗamin waye" uhmm ba yanzu ba "to shikennan babu damuwa nasan dai idan andafa a boye ai baza'aci boye ba idan tayi tsami ma ji" dariya Rufaidah tayi ,haka suka ci gaba da hira ,gwanin ban sha'awa kai bazakace ma da baban ta bane. ta ɗauki tsawon lokaci anan part din kafin ta tashi tace " Abba bara na tafi ,Allah huta gajia "au wai har angama min hirar kenan " yamutsa face tayi " kawadai dai nasan kana bukatar hutu ne amma ai zaka shigo wurinmu ko? ta tsare shi da ido "zan shigo mana ,yanzu ma da zaki tsaya muyi dinner anan tare da yan' uwanki ,Rufaidah inaso naga kun haɗa kanku dukan ku abu ɗaya ne sam banajin daɗin rashin jituwar da bakuyi musamman keda Rumaisa ,dan Allah kicire duk wani damuwa a ranki dukan ku yayana ne kuma ina sonku, Kinga lokacin yayarku Amina ai bahaka takeyi ba tana son yan uwanta sosai "haba Abba to yanxu me nayi kana gani fa daga shigowa na suka nemi su walakanta ni ,taya zan riƙa zuwa inda ake munafurta na ,and dukansu nice yayyarsu so idan ma wani zebi wani sune yakamata ,any wai dai Abba zan wuce ina jiran zuwan ka" girgiza kai kawai yayi dan ya san halin Hajia saudah ne Rufaidah ta kwashe wanda Amina ita sam bata biyewa bakin halinsu zuwa goma idan xatayi gidan to se ta je ta gaishe da Ammi ,kuma

Table of Contents

Chapters

34 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34