Chapter 31
Chapter 31
Bilki da Zainabu mutanen da basu taɓa sona a zuciyarsu ba wanda saboda hassadar da sukeyi min ne yasaka Bilki yin kyautar ɗanta ga Zainabu ,shi kansa yaron ba mutuncina yake gani ba saboda haka nikeso ke da kanki kitafin ki faɗa wa Alh cewar bakison wannan auren akwai wanda kikeso! Da sauri Rufee ta kalleta ,tana girgiza mata kai " A'a Mama karkiyi haka ,ni kaina ba kaunar Ammi nike ba amma hakan baze hana naso Mu'aisam ba ,kiyimin wannan Alfarmar koda ze zama na ƙarshe a tsakanin mu dan Allah kibarni na aureshi wlh bazan iya auren wani namiji bayan shi ba. Rufaidah na fahimci bakisan inda ke miki ciwo ba to saboda haka magana ta karshe zaki zaɓa tsakanin nida Mu'aisam dan kuwa matukar kika yarda da auren nan to kisani babu ni babu ke kimanta cewar nice na haifeki kitafi can na barwa Zainabu ku dama kunfi kaunarta dani ,na samu na rabu da Khadijah gaki ke zaki zaman min karfen kafa , shikennan babu komai ,tunda kin zaɓesa akaina " ta karasa tana fashewa da kukan muna funci , wanda yasaka Rufee rarrafawa ta isa gare ta ,itama kukan takeyi amma takasa magana se sharewa Mama hawaye takeyi ,duk da tanajin bazata iya haƙura da auren Mu'aisam ba ,sedai xatayi kokari ta shawo kan Mama ,tunda tana son ta tasan zata barta ta auri wanda take so Ameerah# lokacin da ta koma gida ta riske wani batu da ya jirkita tunanin ta ,wai Muhsin yazo tambayar auren ta wurin Yaya Labaran ,kuma ya amince masa ,lokacin da Aunty ta gama labarta mata se kawai taji hawaye yana bin kunci ta ,wanda ta rasa ko na miye, sedai ta alaƙanta hakan da rusa mata plan da wannan auren zeyi "haba Ameerah me kikeyi haka ,se kace za'ayi miki dole shifa yayanki ba yace yabasa bane ,kawai dai ze shiga cikin manema ne ,idan kika ce ga wanda kike so dole shi zamu aura miki" Aunty ta faɗa tana goge mata hawaye " Aunty baxaki gane bane ,nifa wannan Managern yasa nafara jin haushi sa meyasa baze tambayeni ba ,se kawai zeyimin kutse a rayuwa ta ,kinsan dai halin Yaya ai ,ganin sa ze iya cewa aure zanyi nikuma ban shiryawa hakan ba impact ma bana son Muhsin" to wa kekeso? Aunty ta tare nunfashin ta " abinda nake gudu kenan na tabbata shima Yaya idan nace banason Muhsin tambayar da zeyimin kenan ,wanda ke kinsan ba wannan bane a gabana ,hasali ma bazan iya aure da ƙarancin shekarun nan ba gaskiya ,nasan ke zaki fahimceni amma Yaya fa? bazan so na furta wa wani mutum kalmar rashin so ba amma a wannan lokacin dole zan gayawa Manager cewar bana son sa ko hakan zesa ya haƙura dani" "A'a Meerah baza'ayi haka ba ai ,babu kyau furta kalmar ƙi musamman ga wanda ke son ka ,bakisan me Allah zeyi a gaba ba ,shin idan da rabon aure a tsakanin ku ,kin isa ki tsallake ne? Ni sam banga lefin wannan mutumin ba ,da badan son gaskiya yake yi miki ba na tabbata baze gabatar da kansa garemu ba ,nide shawara ta itace ,kici gaba da kulasa har zuwa lokacin da Allah ze yi miki zaɓi ,idan kuma shine Alkhairi ,se kiga munsha biki....... Manage pls Real Bazamfaria ce ❤️ *INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION* ( *On* *word* *together* ) *MABARACIYA* *Story* *and* *writing* *By* *FIDDAUSI* *SANI* (damsel feedorh) 🅿️:2️⃣4️⃣ *This page is* *for My Caring fans @Farida L Nuhu @ Amina Abdullahi@ A* *U* *almarkazy @ Nourrieyyer* *Nagode sosai da kulawar* *ku Allah yabar* *ƙauna❤️* Hankali tashe Hajia Sauda ta kira Laura ,sedai kusan ita ma hankalin ta yafi na Sauda tashi ,dan kuwa ta tabbatar da matuƙar Rufee tayi aure to ko ta rasata kenan ,dan haka tace " Hajiya Sauda wannan fa ba ƙaramin al'amari bane ,shiyasa tun farko muke faɗa miki cewar kinyi sake da har kika bari Namiji yake juya ki ,menene a wurinsa me yake baki wanda baki samun finshi ,idan ma kuɗi ne na tabbatar da yanzu ko da baki fishi kuɗi ba to zakuzo daidai ,saboda haka tun wuri kinuna masa cewar kema kinada ƙarfin iko ,ko da hakan ze zamo sanadin rabuwar ku ne" " Da kata Laura bana kiraki saboda matsalar da ke tsakanina da mijina bane ,kawai mafitar fasa auren nan babu ruwanki da rayuwar aure na idan kuma bakida abun faɗa se na kira wata ko zan samu mafita" ganin kamar ta ɗauki zafi se Hajia Laura tace " to shikennan yanzu dai Hajia zama be kamamu ba gaskiya dole zan shigo Kaduna ,saboda wannan maganar ba na waya bane ,inaso kisaki ranki karki sake nuna cewar bakison wannan auren idan nazo nikuma nayi miki alƙawarin rushe maganar auren nan Alh da kansa zece ya janye " da gaske kikeyi Laura? Haba kina mamaki ne kinsan dai bana faɗar abinda bazan aikata ba ko dan haka kizuba ido kawai kijira zuwa na "to dan Allah Hajia karki ɓata lokaci kixo dín kamar yadda kikace dan wlh nikaɗai nasan me nakeji kamar zuciyata zata fashe" to ki kwantar da hankalin ki ni ma dan akwai abinda nikeyi ne yanzu kinsan akwai wasu yara da nace miki za'a kawo ,to sun iso ina jiran senator Abba yazo yafara zaɓan wacce yakeso kafin na tallata sauran to shikuma baya kasan amma yace ze dawo jibi ,to yana dawowa zaki ganni " yawwa to Nagode sosai Hajia Laura se kinzo ɗin ina dibon hanyarki". Muhsin be sake zuwa gidan su Meerah ba kuma be kirata ba ,se bayan kwana biyu ,wannan karon tare da karamar ƴarsa yazo wacce zstakai 4yers ,yarinyar kuwa anyimata gayu tayi kyau sosai cikin riga da wando ta ,zuwan yamma yayi dan haka yasamu unguwar da ɗan mutane babu lefi ,seda ya yi parking tukuna yakira wayarta ,ta na ɗaga wa ,ta gaishe shi " gani a ƙofar gidanku" gidan mu kuma Manager? Be bata amsa ba kawai ya kashe wayar sa, dan ya san halinta ,da musun tsiya ,ya daɗe a wurin zaune yana jiran fitowar ta amma shiru ,itakam Ameerah lokacin da ya kirata dama tana gyaran gida ne dan haka yana kashewa taci gaba da aikin ta ,sam ta ma manta da zuwan shi Aunty da tafito ne zata shiga duba mara lafiya anan maƙota ta ga motar sa ,koma wa tayi cikin gidan tace " Meerah naga wata mota a bakin gida anya kodai Manager ne yazo ? Hala be samu wanda ze kira masa ke bane" turo baki tayi tace" Aunty sharesa idan ya gaji da zaman ai ze koma inda ya fito ,ni sam bana son takura wlh ina zaman zamana zezo ya dameni" au kinma san da zuwan sa kenan? Shiru tayi batace da Aunty komai ba " Ameerah kidena abinda kike sam babu kyau wulaƙanci bakisan waye mutun ba bakisan darajar da Allah yayi masa ba ,dan haka maza ki ɗauko nayafinki kitafi ,bara ni nabar fitar se zuwa dare " tana ƙunaƙuni ta shiga ɗaki ta ɗauki haijabin ta ,tazo zata tafi " haba Ameerah yanzu saboda Allah se kije masa a haka ko ɗan powder baxaki shafa ba ,kuma ki sake hijabi dan wannan yayi tsufa da yawa"
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34