Chapter 1
Chapter 1
*INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION* ( *On* *word* *together* ) *MABARACIYA* *Story* *and* *writing* *By* *FIDDAUSI* *SANI* (damsel feedorh) 🅿️:1️⃣ Dan dazon mabarata ne cike da 'kofar wani makeken gida ,dukkanin su a zaune suke ,kamar dahadin baki kuma duk suke tashi taye ga alama mai gidan ne xe fito ,se turereniya sukeyi ,kamar daga sama saiga wata matashiyar yarinya ,kutse kawai takeyi a cikin jama'a ita birinta baiwuce taganta a gaban layiba saboda tasan ta hakane kawai zata kusanci ganin mai gidan ko matar gidan domin bata damu se mai gidan ne zata gani ba ko matar tagani tasan ta wadata. tana isowa a gaban sahun se taja ta tsaya ,sedai abun mamaki duka tsofaffine a wurin babu yaro ko daya ,kuma ga Alama ba yaune tasaba zuwa ba domin matan nan babu wacce tayi complain akan abunda yarinyar tayi sai wani zare ido take kamar wacce tayi karya ,sunfi 30 minutes a wurin sedai babu alamun cewa masu gidan zasu fito ,hakan ne yasaka jikinta yayi sanyi ,sega hawaye masu zafi suna bin kuncinta ,wata tsohuwa da take taye kusa da ita ta dafata "kiyi hakuri Ameerah,ga alama yau ma masu gidan basanan ,amma kekam ina iyayenki da sukabar yarinya kamarke kina yawon bara, ai da sun sani zaunar dake sukayi a gida sukuma sufito ,saboda yanzu duniyar nan babu gaskiya wani ze iya anfani da dukiyarsa ya lalata miki rayuwa ,duk maganar nan da take hankali Ameerah baya gunta domin ta tafi duniyar tunanin hanyar da zata sadata da mai gidan Saida tsohuwar ta girgizata ,tukuna tadawo hayyacinta ,murmushin yake tayi tace " karki damu Innah gobe ma zan dawo ai mainema baya gajiya ,daga daga haka tajuya da nifin komawa gida ,itadai matar nan da ido kawai ta bita saboda tarasa gane me yarinyar ke nufi itadai idan kaganta bazaka kirata *MABARACIYA* ba domin bata tattre da wahala irin na mabarata ,gashi ita mai tsabtace "ya Allah ka wadatamu abunda ta fada kenan. Saida Ameerah tayi nisa sosai tukuna ta juyo sedai bata hango kowa ba a bakin gidan ,murmushi kawai tayi batasan me yasa ba ko yaushe tazo wurin zata sami mutane da yawa a bakin gidan ,amma kuma da ta tayi nufin barin wurin se kowa ya watse ko meyasa haka,tambayar da takeyiwa kanta kenan sedai bata da mai bata amsa,wuri tasamu ta sauna tana tunanin wace hanya zatabi shin domin samun cikar burinta ,tabbas bazata dakata ba harse ta cimma manufarta , tacikawa yayarta alkawarin da tayi mata ,kuma dole se ta dauki fans a akan Saudahhhh.... #shin wacece Ameerah kuma wacece saudah wane burine takeson cikawa Comment dinku shi ze bani tabbacin labarin yakarbu #followme on wattpad@damselfeedo Real@bazamfaria💙 It's ur Feedorh *INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION* ( *On* *word* *together* ) *MABARACIYA* *Story* *and* *writing* *By* *FIDDAUSI* *SANI* (damsel feedorh) 🅿️:2️⃣ ,,,,,,napep ta tsayar ta shiga fada masa unguwar da xekaita tayi ,sunyi tafiya me dan nisa ,ta sauka Wani madai-daicin gida ta shiga da sallamarta ,kai tsaye daki tanufa tare da furta " aunty na dawo ,da sauri wacce takira da aunty ta fito tace "Meerah andace? Ajiyar zuciya ta sauke tace " ankusa dai aunty "kinga Meerah nifa da zakiji nawa da kin hakura kinbarwa Allah komai domin kuwa shi ba azzalumin sarki bane na tabbata yaji kuma yagani da sannu sakayyar Maryam ze biyo baya Seda ta sauke ajiyar zuciya ,cike da rauni tafara magana " tabbas aunty nasani Allah yanaji baya bacci kuma a addinance ma anbamu damar idan aka zalunceka bazaka iya yafewa ba ,to karama kwatan kwancin abunda akayi maka ,katseta Aunty tayi da fadin " natabbata idan Maryam na raye zata yafe takuma shafe abun a ranta dan Allah Meerah gada kijamana abunda yafi karfinmu ,matar nan tanada iko fiye da tunani zata iya komai saboda mutuncinta ,shin meyasa ke bazaki hakura ba,takarashe maganar tana kafeta da ido ,cike da kwarin gwiwa tace "aunty ,duk wani gata idan ba na Allah bane to ba dawwamamme bane ,bamuda kowa amma muna da Allah saboda haka shine zai taimakeni ,wlh matukar bandauki fansar 'yar uwata ba ,to bazan sake kiran kaina a cikin a halinku ba ,kedai kixuba ido ,ni yunwa nakeji ina abinci na ,girgiza kai kawai aunty tayi tare da fadin " yana da kin ki nakai miki ,Ameerah bata sake magana ba ta nufi dakinta. Seda tafara watsa ruwa tukuna ta dauro alola bayan tagabatar da sallah ,se ta dauko wani littafi ,ta dade tana kallon murfin littafin ,kamar zata bude sekoma ta maida ta ajiye ,shiru tayi tana tunani can kuma se ta fashe da kuka, cikin kukan ne take suratai " tabbas baikamata ace har kinkai yanzu ban cika alkawarina ba yaya Maryam ,ke Kadai ce gatana kece wacce ta sadaukar da mutun cinta saboda nawa ,kin kula dani kinhani nayi kukan maraici ,tabbas bazan samu sukuni ba se Sauda ta tozarta ,tabbas zan wulakanta ta a idon duniya ,zansa ta fahimci ba komai ne kudi da mulki ke bayar wa Allah yagafarta miki tafada tana kara sautin kukanta ,seda tayi kuka sosai tukuna ta rarrashi kanta saboda bata son Aunty ta fahimci halin da take ciki hakan ze zama kamar tayi butulci ne da irin kokarin da take mata Ahaka bacci mai nauyi ya dauketa Ba ita ta falka ba seda akafara kiran sallahr asr da ciwon kai tafalka saboda kukan da tayi lallabawa tayi tayi sallah ,tukuna tafito don dora girki ,a kitchen ta samu aunty marairaicewa tayi kamar zatayi kuka tace "aunty shine baki tashe ne ba ,murmushi kawai tayi mata " to kawo nakarasa aikin ,se a lokacin aunty tayi magana "aa Meerah nasan kingaji kitafi ki huta kawai " aa haba aunty dan Allah kema ya kamata kihuta hakan tafada tana amsar jajjagen da takeyi dole ta sakar mata ,tana tausayin rayuwar Ameerah gata yarinya mai gata da natsuwa amma saboda rashin adalci da son zuciya irin na wasu yana Neman sauyata ya Allah ka kawo d'oki a ratuwar Ameerah "Amen taji muryar Ameerah ta amsa ashe a fili tayi addu'ar ba'a zuciya ba ,murmushi sukayi dukansu Ameerah tace " Aunty kinason Ameerah fiye da tunani nikaina a duk lokacin da na tuna dangina nakan samu kaina cikin zubar hawaye naji na tsane duniya baki daya sedai da na tuna Inada ke se naji damuwata ta gushe ya Allah yakara zaman lafiya a tsakaninki da yaya yakawo zuri'ah tagari yabani ikon kyauta ta miki nagode sosai aunty tafada kwallar da ta cika idonta yana subowa ,lakace mata hanci aunty tayi tace "to Mr tears nasan yanzu zaki fara zubar hawayen ai kedai bansan tsakanin ki da kuka ba babu damar ayi maganar arxiki dake sekinyiwa mutane kuka ,maza ki share hawayen indai baso kike aunty tayi fada da MABARACIYAR kanwata ba ,dariya sukayi dukansu Follo me on wattapad@damselfeedo #Real@Bazamfaria💙 *INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION* ( *On* *word* *together* ) *MABARACIYA* *Story* *and* *writing* *By* *FIDDAUSI* *SANI* (damsel feedorh) 🅿️:3️⃣ ,,,,,,,,,,Washe gari tunda safe Ameerah ta shirya ,koda ta leka dakin aunty bataji motsinsu ba da alama basu tashi bacci ba saboda haka kawai tafita domin yau tasawa ranta ganin sauda ko ta halin yaya ,tana fitowa tasamu Napep ta shiga shiru tayi tana tunanin wane karya zatayiwa get man yabarta ta shiga ,hakadai
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34