Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 18

Chapter 18

Mabaraciya Book 1 Complete Hausa Novel 1,169 words 0 views Progress saved
Download Book

da jan tsaki " muna funcin banza nide duk yadda za'a so shiga tsakanina da Abba ,Allah yafi mutum" girgiza kai kawai Abba yayi tare da furta "Allah ya shirya "da Ameen Rumaisa ta amsa tana ci gaba da bashi labarin da sukeyi tun ɗazu ,itadai Rufee shiru kawai tayi tana sauraren su , lallai ta yarda Mama ce gatan ta duk ranar da aka ce babuta a gidan kila ko ganin Abba se yayi mata wuya Ameerah# Tunda ta kammala gyaran ɗakin ta rufo ƙofa ,se ta dawo warta harabar gidan jikin flowers ɗin da take zama batasan meyasa zaman wurin keyi mata daɗi ba ,tana zaune tana kallon ma'aikatan gidan da suke ta kai da kawo kowa sha'anin gaban sa yake yi wasu yan kyawawan yara da bazasu wuce 7 years bane suka fito daga sashen su Mu'aiseen mace da na miji ,macen ta biyo namijin tanaso ta amshi abinda ke hannun sa ,shikuma ya hanata daganan suka fara kokuwa, cikin rashin Sa'a namijin ya tura macen da hannu biyu se tayi baya ta faɗi ,da sauri Meerah ta isa wurin dagata tayi tana lallahin ta saboda kukan da takeyi ,daƙyar yarinyar tayi shiru tana cewa " Aunty kice yabani abuna nawane Aunty Mimi ta bani" maida hankalin ta tayi wurin Nurain tace " zo kabata kayanta ,ganin zata kamoshi se kawai ya ruga da gudu cikin gida ,dariya Meerah tayi dan sosai yaran suka burgeta ,kama hannun Nawwara tayi tace " kinga ki kyalesa gobe zan kawo miki wanda yafi wannan kyau "cike da jin daɗi tace " da gaske? Ɗaga mata kai tayi tace to shiga daga ciki kema ,goben zan kawo miki ,amma baki faɗa min sunan ki ba " Abban mu yana cemana twince ,Ammin mu kuma tace auta Yaya Rumaisa ke cemin cutie , Aunty Mimi ita ke mun Nauwara ,amma kinsan yayanmu me yake cemin? Girgiza nata kai Meerah tayi, tace" last born"Kai kice sunan naki da yawa duk ke ɗaya lallai ke yar gata ce shikennan shiga ciki kinji kar Ammi ta nemeki " Aunty ni bantaɓa ganin ki ba a gidan su Ya Rufaidah kike? Ɗaga mata kai Meerah tayi dan ta fahimci Nawwara irin yara nan ne masu shegen surutu ,duk da gaskiya yarinyar ta burgeta kasancewar ta wacce ta saba da sabgogin yara duk da bawai tana da ƙanne bane a gidan su . "Nawwara Nawwara tun daga cikin gidan ake kwala mata kira ,sakin hannun ta Meerah tayi tace " kinji ana nemanki ,kafin ta tafi sega Rumaisa ta fito cikin sauri ,da alama ta dade tana nemanta ,ganin ta tare da wacce bata sani ba yasaka ta karasowa da sauri ,takama hannun ta ,tace " me kike yi anan ? nuna mata Meerah tayi tace wannan Auntyn ce tace zata kawo min abuna da Nurain ya kwace ,kallon Meerah tayi ,suka sakarwa juna murmushi a tare tace " kinsha surutu ko " a'a babu wani surutu sun fito ne suna faɗa shine na fabasu " Allah sarki ,ke baƙuwar Rufaidah ce kenan ? Murmushi Meerah tayi tace " a'a me aikinsu ce dai ,tana faɗa ta kalli Nawwara tace " to ƙanwata natafi se goben idan Nazo ko zan kawo miki alkawarin ki " daga haka ta tafi ,da kallon mamaki,Rumaisa ta bita ,haka kawai se taji yarinyar tabata tausayi ,gata karama da ita ,kamata yayi ace tana school a halin yanzu ,amma rashi yasaka ta zuwa aikatau ,kuma tasan a yadda Rufaidah batada kirki ba lallai bane ta sarara mata ,gaskiya da Abba xe yarda da ta rokesa ya temaki rayuwar yarinyar a mayar da ita school ,amma zata gwada sa'ar ta tagani ko zata da ce. Tun da suka shiga ciki Nawwara ke bawa Mimi labarin sabuwar Auntyn ta ,abu kaɗan idan Nurain yayi mata zatace se ta gayawa Aunty ,Ammi da tagaji da jin sunan Auntyn ne yasaka ta cewar wai nikam Auta wace Aunty kika samu ne haka "yawwa Ammi inaso ma muyi maganar dun dazu mantawa nayi ,wlh wata sabuwar me aiki ce su Rufaidah suka dauka sema kin ganta kyakkawa da ita kuma yarinya ce bazatafi 15 yrs to 16 ba ɗazu da kikace na nemo Auta ne naganta ashe itace ta raba musu gardama da sukeyi ,wlh tabani tausayi shi ne nace zanyiwa dady magana ,ko ze temakawa iyayen ta se ta koma school" tun kafin ta ƙara sa Ammi tace " kinsan na haneki da shiga abinda be ganoki ba ko ,so kikeyi ki yawo mana wata jarabar, kinsan dai zasuce wani muna funcine ,kuma daga ganin yarinya kinsan alakar da ke tsakanin su ,to babu ruwanki ban amince kiyi magana akan masu aikin su ba ,da ace ana bangaren take aiki to zaki iya amma a can bakida wannan hurumin " cikin sanyin jiki tace to shikennan Ammi dama nima seda nayi wannan tunanin shiyasa ma ban fada masa ba nace se naji ta bakin ki. Zahra# da dare bayan tagama shirin bacci har ta kwanta se kuma taji tana so takira Fatima ,ta bata labarin Rufaidah dan har yanzu mamakin halayyar ta yaƙi barin zuciyar ta ,bugu biyu kuwa ta ɗaga " Mabaraciya" shine abinda Fatima tafaɗa yayin da ta ɗaga wayar tana sakin dariya ,itama Meerah dariyar tayi tace " is my name ya kike ya Momy? "Lafiya lau ranar se ga kiran uwar gijiyarki rai a bace wai ita dai na nemo wani solution da zata wulakanta ki wannan beyi mata ba ,dan se take ganin kamar ma daɗin aikin kikeji a gidan " hhhhh to ke me kika ce mata? " Haba kema kinsan bazan barta ta rusa Miki plan ba ,dan nagama fahimtar jinkaine kawai da wulakanci ke damunta amma sam batada tunani Brain dinta baya aiki kamar dai kifi haka take " dariya sukayi dukansu ,cikin zolaya Rufaidah tace banason wulaƙancin nan Hajiyar tawace me Brain na kifi " au am sorry fa na manta ,haka sukayi ta labarin halin Rufaidah da suka fahimta wani suyi dariya wani kuma suce Allah ya kyauta ,sun daɗe suna hira a wayar kafin takashe ,dan ganin wanda ke kiranta tun ɗaxu Ko sauke wayar daga kunne batayi ba kiran yasake shigo wa ,kallon mamaki takeyiwa numbern ,dan bakuwa ce ,har zata aje se kuma dai taga rashin dacewar hakan tunda batasan wanda ke kiran ta ba. "Assalamu alaikum" ta furta cikin cool voice nata,wani irin ajiyar zuciya taji an sauke da mamaki tace "waye ? Haba ,ranki ya daɗe saura kadan kisa xuciyata ta buga " har ga Allah ta manta da zancen sa ,murmushi tayi tace " ina wuni ya aiki? Be amsata ba sema tambayar da ya jefa mata " da wa kike waya ,for almost 30 minutes? Uhmmm kawata ce fa " shine kuma kinaganin kirana kikaƙi ɗauka dax means tafini muhimmanci kenan? mamaki maganar sa ta bata amma se tace " to kayi haƙuri bansan kai bane kasan ai banda no naka ko? To shikennan nayi miki uzuri amma dai a kiyaye gaba dan Allah,dan wlh bakiji yadda hankalina ya tashi ba xuciyata se sake²take min ko kina waya da wani namijin ne kuma kinsan bazan iya jurar wannan ba , Ameerah wlh ina sonki fiye da tunanin ki ,kibani

Table of Contents

Chapters

34 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34