Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 2

Chapter 2

Mabaraciya Book 1 Complete Hausa Novel 1,185 words 0 views Progress saved
Download Book

har suka isa dan nesa da gidan ta sauka ,dakafa tafara takowa har gaban gidan sedai yau babu kowa a kofar gidan ,jikinta ne yayi sanyi domin ga alamu masu gidan basunan tana tsaye bakin gidan Sega get man din yabude get ,kamar a mafalki taga wata motor kirar Elentra 2019 ta fito da sauri ta nufi motor din ,winning nacikin motorn yayi domin ganin wata bakuwar fuska tana tunkaro shi karaf idon su ya sarke cikin najuna ,faduwar gaba Meerah taji take taji tarasa duk wani kwarin gwiwa nata ,ganin da yayi ta dakata ne yabashi tabbacin ba wurinshi tazo ba saboda haka yacigaba da tafiyarsa ,koda ta ankara sedai taga kurar motor alamar har ya wuce ,wasu yawu masu daci ta hadiye nan take xuciyar ta tafara kai da komo Shin wanene wannan mutumin ,a iya binciken da tayi akan Saudahh batada 'da babba hasalima yarinyar ta tafarko macece ,to ko shine mijinta wannan din ,haka kawai tasamu kanta fa faduwar gaba tare da baiwa kanta tabbacin ba mijinta bane 'Karasawa tayi bakin get din tayi knocking, lekowa get man din yayi ,seda yagama kare mata kallo tukuna yace "Ke yau baza'ayi sadaka ba ,wai meyasa Ku Mabaratan nan bakuda godiyar Allah ne komai aka baku baya isarku ,ji kukeyi kamar kuyi sata, ina jiya ba da dadewa ba ma matar gidan nan seda tayi sada'ka to yanzu menene na dawowa? " Baba kana nufin jiya matar tafito kenan "Ehhhh mana kuma taraba kudi saboda haka yanzu bata gari ma tayi tafiya ,idan kuma zama zakiyi to ga wurinan yafada yana rufe get din " ohhhh god ,Ameerah tafada tana dafe kai "meyasa nayi gajen hakuri na tabbata jiya da ban tafi ba ,da nahadu da Saudah ,ok dama lokacin da na jiyo naga babu kowa Ashe sun shiga cikine ,Murmushi tayi kuma da ta tuna mutumin nan na dazu da yafito daga gidan ,to waya sani ma ko kwarton tane ,sekuma ta girgiza kai " aa shi baiyi kama da mutumin banza ba daga ganin shi yana da kamala ,to waye shidin ,haka tacigaba da tafiya tana sanbatu ,hartayi nisa bata sani ba ,horn taji anayi mata abayanta ,dan waigawa tayi ,sedai tayi nasarar bin motorn da ido domin bazata iya ganin Wanda yake cikiba kasancewar bakin glass ne a motor ,cike da jin haushin rainin wayon mutumin juyawa tayi taci gaba da tafiyarta ,ganin mutum tayi a gabanta "Assalamu alaiki , ya furta cikin silent voice dinsa ,kamar bazata amsa ba sekuma taga ai sallama ne kuma shi da yayi sunnah ya 'dabbaka ,amma ita wajibine ta amsa masa domin yin sallama ga musulmi sunnah ne amma maidata wajibije Amsawa tayi batare da ta dakata da tafiyar ba " baiwar Allah idan bazaki damu ba ki shigo narage miki hanya domin baikamata mace kamarki ace ta bari rana yana dukanta ba ,karkisa hukumar kare hakkin mata ta hukun tamu yafada cikin sigar tsokana Kara tamke fuska tayi ,cikin rashin son zancen yayi tswo tace "na gode bana bukata " haba ke kuwa ai cancantar ki ne yasa nace ki shigo bawai se kina bukata ba ,bata sake cewa komai ba tarabashi ta tafi Yana tsaye a wurin har seda yaga tayi nisa alamar dai da gaske ba shigar zatayi ba tukuna yakoma motorn shi Follow me on wattpad@damselfeedo #Real@Bazamfaria💙 *INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION* ( *On* *word* *together* ) *MABARACIYA* *Story* *and* *writing* *By* *FIDDAUSI* *SANI* (damsel feedorh) 🅿️:4️⃣ ,,,,,,,tunda daga ranar Ameerah batasake zuwa gidan ba ,amma ko yaushe plan dinta taya zata shiga gidan sauda takeyin shi tanasone idan tayi nasarar haduwa da ita ,duk wani shiri nata yayi aiki ,shigowar aunty ne yasakata dawowa daga duniyar tunani ,murmushi tayi tare da fadin " aunty ce da kanta ,itama murmushin ta mayar mata tace " to yau najiki shiru nama zata ko kinfita ne shine nace bara nazo na dubaki tafada tana zama gefen katifa " wlh aunty ina nan bana fada miki shegiyar tayi tafiya ba ,tana can wurin fasadin nata Ameerah tafada tana cixon baki da alama abun yana yi mata ciwo ,dafata aunty tayi tace " Ameerah nifa inaganin wannan abun da kikeyi ba mafita bane taya xa'ayi ki ajiye karatunki ,kawai saboda kinaso ki dauki fansa kinsani burin Maryam be wuce taga kinyi karatu ba to mezesa saboda ita ki ajiye karatun ki nidai anawa shawarar ki koma makaranta na tabbata ko baki tona asirin Saudah ba yau da gobe Batabar komai ba asirinta se ya tonu ,amma yarinya kamarki a ce kina yawon gidaje tare da amsa sunan Mabaraciya wanann ai ba solution bane Ameerah dai batace komai ba hasalima se wani zancen ta dauko ,tunda aunty taga haka tasan cewar ba daukar shawarar ta zatayi ba ,bata taba ganin yarinyar da ke rike abu a ranta ba kamar Ameerah, abunnan anyishi tun bata wani mallaki hankalin kanta ba amma yakasa barin xuciyar ta "Akwai dalilina na dakatawa da karatu ,kinsani lamarin karatu yana bukatar kudi kingani yaya bawani karfi ne dashi ba kema ba wani Sana'a kikeyi ba ,shin me kike tunani idan nasaka araina cewa dole se nayi karatu ,bafa dole se mutum yayi karatu bane ze iya dogoro da kai ,nasani karatun ma yanada matukar anfani amma idan inada rabon yi sekiga nayi konan gabane ,nifa araina banajin komai saboda dakatar da karatu na kawai dai idan natuna burin yaya Maryam kenan senaji wani iri cikin raina " hakane Ameerah amma kinsani indai kinason karatun nan na tabbata Isma'l ze iya daukar dawainiyar komai "hakane aunty nagode sosai da kokarinku amma dawainiyar da kukeyi dani haka ma ya isa fatana rabbi yabani ikon kyautata muku Niger state Wata matace zaune ta hakimce daga ganinta kasan tana da isa da kuma izza waya takeyi cikeda takama ,Sam bakajin me take fada kasancewar sedai bakinta ya motsa yarane 'yan mata tsugune a gabanta waya takeyi amma tana kare musu kallo ,se bayan tagama wayar ne tukuna tace " zaku iya zama ,tashi sukayi suka zauna cikeda tsoro Kallon su tayi tasake wani killer smile cikeda isa tace " to ya kun shirya abunda nake bukata ko kuwa cikin kyar kyarwa dayar tace " munshirya Hajia daga mata hannu tayi tace "naji naki amsar kefa ,tafada tana nuna dayar budar bakin ta tace " tabbas duk Wanda babu Allah a cikin ranshi to ze iya aikata komai ,dama idan bakada kunya to ka aikata abunda kaso kidubemu hajiya anan ciki babu wacce baki isa haifarta ba amma kuma kice mune zamu zameki ababen jin dadi ,daga karshe kuma kitura mu karuwanci anabaki kudi wa'iyaxubillah ,amma ba lefinki bane lefin iyayen mune da Allah ya dora nauyim mu akansu amma suka kasa saukewa har wasu suka yaudaresu suka daukomu da sunan aikatau ,domin subata mana rayuwa duk maganar da yarinyar nan keyi babu wacce ta taba zuciyar hajiya itadai abunda tasani dole zata biya bukatar ta dasu takuma samu kudi ta dalilinsu ,daya daga cikin masuyimata hidma takira tace "tafi dasu kitabbata sun tsabtace jikinsu domin bana bukatar na shaki wari ko akasinsa ,kuma ki koya musu yanda zasu sarrafani domin naji dadi daga nan zuwa gobe Wacece wannan matar? Kucigaba da bina asannu zan bayyana muku komai #comment and share Follow

Table of Contents

Chapters

34 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34