Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 11

Chapter 11

Mabaraciya Book 1 Complete Hausa Novel 1,192 words 0 views Progress saved
Download Book

take babba bazata iya irinshi ba ,taɓa baki tayi tace " ko da yake dagani tasaba aikatau . Meerah kam tana saukowa ,ta samu wuri a falon ta zauna ganin shiru shiru bata fitoba yasakata sha'awar zuwa haraban gidan ,tana tafe tana ƙare wa gidan kallo ,batayi aune ba taji tayi karo da mutum,cikeda tsoro ta ɗago don gudun kar kowaye yayi mata rashin mutumci tunda ta kula kamar halayyar ƴan gidan ne "ke? taji yafaɗa yana nuna ta ,itama zare ido tayi saboda ta ganeshi mutumin nan ne da tataɓa yaɗuwa dashi kasuwa " me kikeyi a gidanmu ? Tambayar da yayi mata kenan,murguɗa masa baki tayi zata taɓa shi ta wuce ,fixgota yayi yace " bakiji me nace ba ? Cike da jin haushi tace " aikatau ,shiru yayi yana kallonta ,bece komaiba ya saketa ,raɓashi tayi ta wuce fasa zuwa balcony ɗin tayi tadawo falon ta zauna da kallo yabita ,tabbas yasaka wasi-wasi akan yarinyar ,da fari tazo gidan amatsayin Mabaraciya ahaka yaganta ,se kuma ya ganta a hanya a matsayin cikakkiyar me gata ,a yau kuma ta dawo gidansu amatsayin ƴar aiki,anya kuwa yarinyar nan Mabaraciya ce kodai anturo ta ne leƙen asiri" i will find it out ,yafaɗa yana shiga falon shima a falon ya ganta raɓe gefen kujera ,bece da ita komai ba ,Larai da yaga tafito ya kalla yace " ke kiramin Rufaida , kusan a tare suka sauko itada Rufaida ,tunda ta hangoshi ta washe baki,cikeda jin daɗin ganinsa tace " Welcome MM ,shima Murmushi ya mayar mata yace " tnz ,haka kike zaune a ɗaki ke kaɗai instead of ko ƴan aikinnan kizauna kuyi hira ai sa ragemiki kaɗaici ko? Wane irin kallo tabi Meerah da sam tanuna hankalin ta baya kansu " yanzu Yaya saboda banda hankali se na zauna cikin ƴan aikin da sukecin abinci a ƙarƙashina na sakasu aikin da duk na gadama ,kuma zan iya marinsu idan suka kuskurewa umurni na ,amma duk da haka kake cewa wai nayi hira dasu? God forbid,never dead my body ,girgiza kai kawai Mu'aiseen yayi cikin zuciyarshi yake faɗar " yuh won't ever change ,a zahiri kuma tashi yayi tsaye yace " to ni zantafi dama fita zanyi nace bara na leƙoƙi tunda ke kinfi ƙarfin zuwa inda mutane suke "afuwan yaya ,harzaka tafi ko lemu bakasha ba ,laluba cikinsa yayi yace " don't worry am ok " ok to mutafi na rakaka,haka suka jero suna tafe suna hira ,itadai Meerah mamaki yakasheta ashe dama tana dariya lallai tafaɗa tana ci gaba da kallon tv,tana nan har Rufee tazo ta wuce ta,kallon agogon falon tayi taga har lokacin sallah yayi,inda taga Larai ta shiga tun ɗazu nan tabi Sega ta cikin kithen,sannu da aiki tayiwa Larai kafin ta tambayeta inda zata samu ruwan alolah,da sakin fuska Larai ta nuna mata wani coridor tace " akwai bayima acan idan zaki zagaya,Murmushi itama tayi tace " Nagode tare da bin hanyar seda tashiga toilet tayi fitsari tukuna tayi alwala ,a ɗan gefen wurin ta shinfiɗa kallabinta ta tayarda Sallah,tana idarwa ta dawo ciki zaman jiran tsammani ,ganin har kusan ƙarfe 4 Rufaida bata sauko ba ga kuma yunwa da takeji se kawai ta yanke shawar tafiya gida tunda dai ta kammala ayyukan ta to bataga dalilin zamanta ba kuma,wurin Larai taje tayi mata sallama ,kafin ta fito ta kama hanya ,koda ta shiga gida ana kiraye-kirayen sallar la'asar,a matuƙar gajiye tashiga gidan Aunty da ke zaune tana jiran dawo warta ta tareta da sauri tanayi mata sannu Ruwa tafara kawo mata girgiza kai tayi tace " Aunty ai se cikina ya ƙulle me kika dafa mana yau? Narasa me zan dafa shine kawai na yimana ɗan wake ,washe baki Meerah tayi tace," kin kyau ta min kamar kinsan nayi marmarin sa bani naci cikina har kukan yunwa yakeyi ,tashi aunty tayi ta kawo mata ɗan waken aikuwa ta hau ci kamar Mayun waciya ,seda tazo ƙarshe Aunty tace " gaskiya Ameerah ki canja wata shawarar dan bazaki sake komawa aikin nan ba ,a firgice ta saki sauran ɗan waken da yake hannunta tace " haba Aunty kenan duk wahalata tatafi a banza kenan seda nafarajin ƙanshin nasara shine zakice na dena ,koda a ce Rufaida zata riƙa yanka nama na ne zan jure matuƙar zan haɗu da muguwar matar nan Hajia Saudah....... #Real@Bazamfaria *INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION* ( *On* *word* *together* ) *MABARACIYA* *Story* *and* *writing* *By* *FIDDAUSI* *SANI* (damsel feedorh) 🅿️:1️⃣2️⃣ dafa kafaɗarta Aunty tayi cikin sanyin murya tace "Meerah bawai ina so na hanaki ɗaukar fansan abinda akayi Miki bane ,saboda addini ma yabamu wannan damar idan har aka cuceka kuma kaga bazaka iya yafewa ba to ka rama daidai da yadda akayi maka ,sedai kituna irin tanadin da Allah yayiwa masu yafiya musamman a inda sukeda halin ramawa, Meerah inajin tsoron faruwar wani abu gareki Hajia saudah da kike gani ba ƙaramar mace ba kuma mijinta ma babban mutum ne na tabbata koda za'a kamata da lefin fasa kauri da yara mata tofa babu wani hukunci da zata fuskanta ,domin su sukeda doka , Allah ne kawai xe iya hukunta su bawai dan'adam ba musamman ke mace karama me rauni ,karkiyi wasa da rayuwar ki bamuda kowa se Allah. Shiru Meerah tayi tana sauraren Aunty har seda tayi shiru ,alamun ta gama maganarta,murmushi tayi harseda fararen haƙoranta suka bayyana ,cikin salon maganarta tace " Aunty naji daɗi da kika ce Allah ne ce iya hukunta ,ki fahimceni bawai inason yaƙar ta bane ko kuma burin fansa ne kawai a gabana ba , a'a inaso ne na nuɓutar da sauran yaran da take ƙoƙarin halakarwa na kuma bayyanar da ɓoyayyiyar fuskanta wacce take cin amanar addini ,mutane da yawa suna yabonta akan kirkin ta har takan ɗauke wasu daga cikin yaran marasa ƙarfi da sunan zata tallafi rayuwar su wanda babu wanda yasan me take sakasu sunayi ,kasuwanci takeyi dasu Saboda haka temako ɗaya nikeso kiyimin Aunty shine kitayani da addu'a Allah yabani ikon cin nasara akanta" tana gama faɗar haka bata jira cewar Aunty ba ,tayi shigewar ta ɗaki, girgiza kai kawai tayi saboda tasan halin Meerah da naci akan bu tunda har tayi niyya to babu wanda ya isa ya dakar da ita. Washe gari tunda tayi Sallahr asuba bata koma bacci ba dan haka tafita tayi share² sannan tayi wanke² seda ta gama tukuna ta shiga wanka ,bata ɓata lokaci ba saboda saurin da takeyi kar ta haɗu da rashin mutuncin Rufaidah ,yau kam doguwar rigar atamfa ta saka babu lefi da ɗan haske ta duk da ta koɗe amma tafi kayan jiya haske ,ko mai bata shafawa jikinta ba ta ɗauki hijabinta tsoho shima ta saka ,a bakin ƙofa ta haɗu da aunty tana shirin shigowa ɗakin ,ɗan matsawa tayi daga gefe tana murmushi ta gaisheta " bade har zaki tafi ba gashi na makara daga na gishingiɗa bacci ya ɗaukeni" murmushi ta sake yi tace " karki damu Aunty ,ai dama za'a riƙa bani abinci a can yanzu idan nace na tsaya zanbata lokaci ,ga yarinyar batada kirki"to shikenan kide kula dan Allah ,kikama mutuncin ki kuma Allah ya kiyaye se kin dawo "Insha'Allah Aunty Nagode" daga haka ta fita gidan , cikin natsuwa take tafiyar ta

Table of Contents

Chapters

34 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34