Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 10

Chapter 10

Mabaraciya Book 1 Complete Hausa Novel 1,192 words 0 views Progress saved
Download Book

tafiya sukayi se gasu sun bayyana a cikin wani falo na alfarma ,fadin kyau da tsarinshi bata lokacine ,zama Fatima tayi akan daya daga cikin kujerun falon ,itama Meerah ta samu daya ta zauna " sannu da zuwa Hajia me aiki ta gaisheta ,cikin sakim fuska Fatima ta amsa ,kifadawa Rufaida ina jiranta,da "to ta amsa,bata dade da tafiya ba segata tadawo tace " tana zuwa ,andauki tsawon 10 minutes,se alamun saukowar Rufaida daga stairs sukayi " tun kafin ta karaso suka tsinkayi muryarta tanafadin ......... **Magana ta gaskiya mutanen Group ɗina zan Dena yi muku posting,se nake ganin kamar labarin be karɓu* a *wurinku ba ace bb wacce zata iya yin comment,ku gyara idan kunaso ko na* *komawats* *Wattpad dama asalin labarin nasu ne* Comments nd share #Vote and follow me@ damselfeedo #Real#Bazamfaria *INTELLIGENT* *WRITERS* *ASSOCIATION* (On ward together) *MABARACIYA* *Story* *and* *writing* By *FIDDAUSI* *SANI* (damselfeedorh) 🅿️:1️⃣1️⃣ ,,,,,,,Kuskure mafi girma shine na riski kaskantacciyar yarinya zaune a inda nake zama ,tunda Rufaida tayi wannan maganar Meerah ta fahimci da ita take ,cikin sanyi jiki ta zube kasa,cikeda da isa Rufaida ta karaso cikin falon ,seda ta samu wuri ta zauna tukuna ta kalli Fatima tana wani yamutsa fuska tace " ke kam Teemah kincika jajume jajume ina kuma yau kika samo Mahaukaciya? Tayi maganar cikeda wulakanci ,sosai kalmar ta shigi Meerah wanda hakan yasakata dago ido da sauri ta kalli Rufaida,sedai saurin mayar da kanta tayi akasa ,saboda bataso ta fahimci komai. Murmushi Fatima tayi tace " she's the one, blinking ido Meerah tayi mata alamar bataso ta nuna taganeta ,saboda kar yarinyar ta canja ra'ayi ,shiru Meerah tayi tana saurarensu Fatima kamar yanda naji kince kina neman 'yar aiki to gata na samo miki ,cikeda hargowa tace "me kike nufi badai wannan me kala da mahaukatan ce zan dauka aiki ba ,wannan ko ruwa ta taba ai bazan iya shan suba kidubeta fa " aa Rufee bazamuyi haka ba ,ko ba komai yarinyar ,iyayenta ne abun tausayi ba ita ba ,suna fama da ciwon talauci " And so? Ko nice na saka musu talaucin ,daga ganin iyayenta ,basu san me sukeyi ba tunda har zasu iya turota aiki a irin wanann yanayin,cikin tsawa Meerah tace " karki kuskura 'yarnan zan iya daukar komai amma banda cin fuska ga sanyi idaniya ta ,iyaye da kike gani sunfi karfin to zarci ,tana gama fadar hakan ta tashi da niyar fita ,sedai a cikin xuciyarta addu'ah take Allah yasa Fatima ta tsaidata ,domin batasan da wannan plan dinba ,har tafara taka kafarta ta tsinkayi muryar Fatima tana fadin " fitar da zakiyi shine sakaci na karshe da zakiyi da damarki ,idan har da gaske kike iyayenki sanyin idaniyarki ne to kuwa tafiya bata kamakiba domin kinsan yanda suka kwallafa rai a wannan aikin naki ,suna ganin kamar wata mafita ce Allah ya kawo musu na fita daga kangi yunwar da kuke fama dashi ,kinada kanne kanana ,dukansu yanzu ,burinsu akanki yake be kamata mai nema yarika xuciya ba . Shiru Rufaida tayi tana saurarensu,ita sam hankalinta be kam maganar Fatima kawai tunanin irin xuciyar yarinyar takeyi ,tayi zaton ,komai zatayi mata bazata tanka ba saboda ,zafin talauci kwafa tayi tana ayyana irin tozarcin da zatayi mata ,jiki a sabule Meerah ta dawo ta zauna ,tana sauke ajiyar zuciya domin batayi tunanin Fatima zata iya yin wanan tunanin ba , seda Rufee tayi wani irin murmushi wanda itakadai ta barwa kanta sani manufar sa tukuna tace " Temah ,idan zata iya kiyaye duka sharuddan da zan gindaya mata ,kallon Meerah Fatima tayi tace to kinji ,cikeda dakewa tace" ina saurare Na farko dai ni banda 'dakin da zan ajiyeki , bawai kuma saboda babu dakin a gidan bane sam sedai baki can canci ki zauna ba ,na biyu dole 7:00 yayi miki a cikin gidannan ,saboda 8 Nake tashi nayi sallah to kafin nashiga bayi ina bukatar ki tsaftace shi, se abu na karshe ,gada kiyarda yunwar iyayenki yasaki tunanin,daukar abincin gidan nan kitafi dashi koda kuwa an rage ne ,idan kika kiyaye wanan shikenan kuskure musu kuwa ,hmmm takarashe tana lumshe ido ,cikeda rashin damuwa Meerah tace " indai zaki kiyaye biyana hakkina ai wanan ba matsala bane ,jin amsarta yasaka Rufee dagowa ta dubeta ,sosai take mamakin jinkai irin na yarinyar ,kiran Larai wacce ke mata aiki tayi ,cikeda ladabi tace " Hajia gani ,kallon mamaki Meerah tabi Larai da shi ,idan aure kauye tayi kusan tahaifi Rufaida,amma gashi tana kankantar da kanta gareta " Rabbi ka kara rufa mana asiri tafada cikin xuciyarta " ki nuna mata dakina ta gyara komai kafin nazo ,tun kafin Larai tayi magana Meerah ta tashi binta tayi ,seda suka fara taka steeps tukuna ta juyo cikin sa'a kuwa sukayi ido biyu da Fatima ,kashe mata ido tayi tare da jinjina mata hannu alamar godiya , murmushi kawai Fatima tayi mata ,daga haka ta dawo kan Rufaida " Nikam Rufee wai yanzu wane irin horo kike tunanin zakiyiwa yarinyar nan ,saboda da alama tanada jin kai "hararar ta Rufee tayi tace, malama ina da zan dauki matakin kece kika hana " haba taya zan hana baki fahimceni ba kenan ,kinsan dalilin da yasa na sanyayar mata da jiki saboda kar ta tafi? Bata jira amsar Rufee ba tacigaba da magana "to saboda nayi miki alkawarin se kin wulakanta ta kamar dai yanda kikayi alwashi kuma kema nasan kinason haka ,matsalar da aka samu ,saurin fushi dakikayi da wannan nayi anfani na tabbata komai zakiyi mata bazata bar gidannan ba saboda tana kaunar iyayenta kuma tana tausayinsu ,idan tabar gidan nan shikenan duk wani Hop nasu ya lalace,kinga dole zatayi hakuri ko badan saboda itaba ,domin iyayenta Lumshe ido kawai Rufee tayi "amma yanayin da take magana ne idan kin kula kamar ba na sauran yayan talakawa ba,ni se nake ganin kamar tanada jin kai " karki damu da wannan ,haka wasu yayan talakawa suke idan kika ga suna daukar kai seki zata sudin wasu ne ,ajiyar zuciya Rufaida ta sauke tace " shikenan Teeamah na gode bari na koma bacci nakeji ,kallon mamaki tabita da shi kamar ba daga baccin ta taso ba ,amma a zahiri murmushi tayi tare da fadin " shikenan nima bara na wuce Mamana tana jirana ,dan ya mutsa fuska Rufaida tayi kamar bataji dadin furucin Teema ba bata dai ce komai ba ta tashi sukayi sallama. Cikin ƙanƙanin lokaci Meerah ta gayara duka rooms ɗin ,bakin wani da yake a rufe ta dawo ,tsaye tayi tana ƙare wa ɗakin kallo cikin zuciyarta take ayyana cewar shine ɗakin Hajia Saudah ,ɗan zagayawa tayi inda taga window,sedai a rufe windown take ,motsin da tajine kamar ana taka steps yasakata barin wurin da sauri ,kallon tuhuma Rufee tabita dashi ƙasa tayi da kanta tace " na kammala ,tsaki kawai tayi mata ta taɓa ta tayi shigewarta ,da kallo Meerah tabita ,tana nemamata shiriya ga Allah,dan Allah yayi ka mai kuɗi bayana nufin kafi kowa bane . Rufaida na shiga ɗakinta taji wani sanyi da ƙanshi ya bugeta babu shiri tafaɗa kan gado tana lumshe ido a zuciyarta mamaki take ya'akayi wannan villager ta iya gyaran ɗaki har haka gashi bata wani ɓata lokaci ba tayi mata aikin da ko Larai da

Table of Contents

Chapters

34 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34